Save The Children Ta Shirya Taron Bita Ga Yan Jarida Da Kungiyoyi Masu Zaman Kansu A Kaduna.
Published: 31st, May 2025 GMT
A wani yunƙuri na ƙarfafa ilimi mai inganci, adalci da shigar da kowa a cikinsa ga yara da matasa a Jihar Kaduna, ƙungiyar Save the Children ta shirya taron bita na kwana biyu ga yan jarida da kungiyoyi masu zaman kansu a Kaduna.
Taron ya haɗa wakilai daga sashen ilimi, kafafen yaɗa labarai da ƙungiyoyin masu zaman kansu.
Taron wani ɓangare ne na babban shiri da ke da nufin haskaka ƙalubale da damar da ke akwai wajen dawo da yara makarantun da kuma tabbatar da samun ingantaccen ilimi.
Rahoton Hukumar Ƙididdiga ta Jihar Kaduna na shekarar 2020 ya nuna cewa fiye da yara dubu 700,000 ne basa zuwa makaranta a jihar – adadi mafi yawa a Najeriya.
Wannan matsala ta nuna bukatar daukar matakai na gaggawa da samarda domin kawar da duk wasu kalubale da ke hana yara shiga makaranta, ƙara adadin masu rajistar shiga makaranta da kuma inganta yadda ake koyarwa da koya.
Da yake jawabi a taron, Daraktan Tsare-tsare na Ma’aikatar Ilimi ta Jihar Kaduna, Malam Salisu Baba Lawal, tare da Mataimakin Shugaban Ayyuka, Hassan Abdul, sun tabbatar da cewa gwamnatin jihar na da niyyar rage adadin yaran da basa zuwa makaranta.
Sun bayyana cewa jihar na aiki tare da abokan haɗin gwiwa ciki har da Save the Children da UNICEF, domin shigar da yara akalla 200,000 cikin tsarin ilimi na yau da kullum.
Sun jaddada muhimmancin tabbatar da cewa shirin ya shafi kowane ɗalibi, musamman masu buƙatu na musamman.
Sun bayyana cewa aiwatar da wannan shiri mai da hankali kan yara yana da matuƙar muhimmanci, musamman a makarantun da ke da yawan yara masu cutar autism, domin hakan zai iya haɓaka ingancin karatu da tabbatar da cewa ba a bar ko wane yaro a baya ba.
Wadanda suka halarci taron sun jaddada rawar da kafafen yaɗa labarai ke takawa wajen wayar da kai da kuma ƙarfafa fafutukar neman ilimi mai shigar da kowa.
Daya daga cikin manyan abubuwan da aka cimma a taron shi ne tsara shirin tallata batun yara da basa zuwa makaranta ta hanyar amfani da labarun rayuwa, fasahar da muradun yara domin tasiri ga manufofi da kuma ƙarfafa haɗin kan al’umma.
Shugaban Ƙungiyar ‘Yan Jarida ta Najeriya (NUJ), reshen Jihar Kaduna, Malam AbdulGhaffar Alabewele, ya yaba wa masu shirya taron bisa yadda suka haɗa ‘yan jarida tun daga farko.
Ya ce hakan zai taimaka wajen fahimtar shirin da kyau da kuma samar da haɗin kai mai ma’ana.
Wani mahalarci daga Radio Nigeria Kaduna, Malam Adamu Yusuf, ya roƙi Gwamnatin Jihar Kaduna da ta ɗauki malamai ƙwararru a makarantun firamare, musamman a cikin yankunan karkara da ke da buƙata sosai.
Wasu daga cikin mahalarta sun bayyana taron a matsayin Wanda ya zo a lokacin da ya dace la’akari da yawan yara masu cutar autism da ke ƙaruwa da kuma buƙatar ƙarin tsarin tallafi.
Wani daga cikin mahalartan ya jaddada muhimmancin fara shirye-shiryen gwamnati da ke mai da hankali kan yara masu buƙatu na musamman, yana mai cewa fara tun da wuri yana da matuƙar tasiri wajen gina makoma mai haɗin kai da ci gaba.
A lokacin taron, an gabatar da bayanai daban-daban da suka bayyana manyan ƙalubalen da ilimi ke fuskanta a Jihar Kaduna da kuma hanyoyin aiwatar da shirin shekaru huɗu cikin nasara domin tabbatar da cewa kowane yaro ya samu ilimi mai nagarta.
Wannan shiri wani ɓangare ne na babban yunƙuri domin tabbatar da cewa dukkan yara a Jihar Kaduna—ko daga wane asali ko halin rayuwa—an ba su damar koyo, girma da cimma burinsu a rayuwa.
COV: Adamu Yusuf
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Yan Jarida Shirya Taron
এছাড়াও পড়ুন:
Tinubu Ya Tattauna da Gwamnonin APC Kafin Muhimmin Taron NEC
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp