2025-11-03@12:32:30 GMT
إجمالي نتائج البحث: 11069

«takardun lamuni»:

    Turkiyye na karbar bakuncin wani taron ministocin harkokin wajen kasashen musulmi kan halin da ake ciki a Gaza. Wannan taron ya zo ne bayan makonni uku da fara aiki da yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza. A cewar Turkiyya, manufar taron ita ce taimakawa wajen mutunta yarjejeniyar tsagaita wuta da kuma sake tabbatar da rawar da...
    Ofishin Yada Labarai na Gwamnatin Gaza Ismail al-Thawabteh y ace Rundunar sojin Isra’ila ta aikata laifuka 194 tun bayan cimma yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza wadda ta fara aiki a ranar 10 ga Oktoba. al-Thawabteh, darektan ofishin, ya shaida wa kamfanin dinalancin labarai na Anadolu cewa laifukan sun hada da hare-haren da Isra’ila ta kai...
    Rahotanni daga Afganistan na nuni da cewa mutane akalla 20 ne suka rasa rayukansu a wata girgizar data auka wa kasar a cikin daren jiya Lahadi. Girgizar kasar ta auku ne a arewacin kasar ta Afghanistan a yankin Kholm, da lardin Samangan, kusa da birnin Mazar-e-Sharif, inda ta yi sanadiyyar mutuwar akalla mutane 20, a...
      Kwankwaso, wanda shi ne dan takarar shugaban kasa na NNPP a zaben 2023, ya fitar da wata sanarwa mai karfi yana gargadin cewa kalaman Trump na iya kara ruruta wutar rikicin addini da kuma kara ta’azzara rashin tsaro a kasar.   A shafinsa na X, tsohon gwamnan ya yi Allah-wadai da matakin Trump na...
    Shugaba Bola Tinubu ya ce “ya riga ya yi nisa da wasan da aka tsara a Amurka,” in ji fadar shugaban Najeriya a cikin wata sanarwa a ranar Lahadi, bayan da shugaban Amurka Donald Trump ya yi zargin cewa ana cin zarafin Kiristoci a Najeriya kwanan nan. A cewar Bayo Onanuga, mai ba Tinubu shawara...
    Daga Aminu Dalhatu Uwargidan Gwamnan Jihar Zamfara, Hajiya Huriyya Dauda Lawal, ta yaba wa Shugaban Karamar Hukumar Gusau, Alhaji Abubakar Imam, bisa shirin tallafawa jama’a domin dogaro da kai da kuma inganta rayuwarsu. Ta yi wannan yabo ne yayin bikin kaddamar da kayan tallafi a Gusau, babban birnin jihar Zamfara. Hajiya Huriyya Dauda Lawal...
    Daga Usman Mohammed Zaria Shugaban Karamar Hukumar Birnin Kudu, Injiniya (Dr.) Muhammad Uba, ya yaba wa Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, bisa amincewa da sabbin ayyukan gina hanyoyi a fadin jihar, ciki har da na Birnin Kudu. Ya ce wannan mataki na cikin ajandar gwamnati 12, musamman wajen inganta ci gaban ababen more rayuwa....
    Ana ta ce-ce- ku-ce kan batun da shugaban kasar Amurka Donald Trump ya yi na kawo dakarun kasar sa Najeriya don taimakawa wajen yaki da matslar tsaro.   Yayin da wasu ke ganin hakan abun san barka ne, wasu kuwa tofin Ala tsine suka yi ga wannan batu. Shin ko me zai faru idan aka...
    Har ila yau, majalisar ta amince da Naira biliyan 3.3 don ayyukan samar da ruwa da makamashi domin inganta samar da ruwa mai tsafta da aminci a cikin al’ummomin birane da karkara.   Daga cikin ayyukan samar da ruwan, an amince da gina tashar tace ruwa ta zamani a Taliwaiwai da ke ƙaramar hukumar Rano,...
    Shugaba Donald Trump, ya jaddada cewa Amurka na iya tura sojoji ko ƙaddamar da hare-hare a kan Najeriya idan har kashe-kashen da ya ce ana yi wa Kiristoci suka ci gaba. A yayin tattaunawa da manema labarai da kuma saƙonnin da ya wallafa a shafukan sada zumunta, Mista Trump ya ce ba zai zauna yana...
    Sabon rikici ya kunno kai a Jam’iyyar PDP yayin da ɓangarori biyu da ke taƙaddamar — na Umar Iliya Damagum, muƙaddashin shugaban jam’iyyar, da na Samuel Anyanwu, sakataren jam’iyyar na ƙasa — ke shirin mamaye hedikwatar jam’iyyar da ke Abuja yau Litinin. A ranar Asabar, yayin da Damagum da wasu mambobin Kwamitin Ayyuka na Ƙasa...
    An kama wata matar aure a garin Kuta, hedikwatar Karamar Hukumar Shiroro ta Jihar Neja, bisa zargin yankar wuyan mijinta, Salisu Suleiman, da wukar girki. Majiyoyi sun ce matar ta kuma soka wa mijin wuka a idonsa na hagu, lamarin da ya lalata idon gaba ɗaya. Wata majiya da ta nemi a ɓoye sunanta ta bayyana...
    Wani magidanci, Malam Jibrin Rabi’u, ya bayyana yadda matarsa, Khadijat Ado, ta ɓace a gidansu da ke unguwar Life Camp a Abuja a ranar Alhamis da ta gabata, sannan kuma aka gano ta a Sakkwato washegari. Ya shaida wa wakilinmu da yammacin Lahadi, cewa ya dawo gida a ranar Alhamis, sai ya tarar da matarsa...
    Kakakin hukumar kula da kanana yaran ta majalisar dinkin duniya  tess ingram ta bayyana cewa yanayin da yara ke ciki a yankin gaza yayi muni sosai, inda sama da yara miliyan daya dake gaza suke bukatar taimakon gaggawa na ruwan sha da kuma abinci Ingram ta fadi a wata hira da aka yi da ita...
    Rahotanni sun bayyana cewa kungiyar gwagwarmaya ta Hamas tayi watsi da zargin da Amurka ta yi mata a baya bayan nan na cewa mayakanta sun wawushe kayayyakin agaji da wata mota take dauke da shi a yankin Gaza, ta bayyana zargin a matsayin karyace kawai mara tushe balle madafa, tace Amurka na wannan zargin ne...
    A wata hira da kafar watsa labarai ta iran press ta yi da jagoran harkar musulunci a najeriya shaikh Ibrahim zakzaki yayi tir da ci gaba da kashe mutane da ake yi a kasar sudan inda kungiyar RSF ta kasashe sama da mutane 2000 a garin el-fishar, ya zargi kasar hadaddiyar daular larabawa da ruruta...
    Kakakin gwamnatin kasar iran fateme muhajirani ta bayyana cewa ma’aikatar harkokin wajen kasar iran ta tabbar da karbar sakon da ya kunshi batun fara tattaunawar diplomasiya tsakaninsu da Amurka, sai dai za’a bayyana yadda za ta kasance da kuma abubuwa da ta kunsa a nan gaba. Wannana mataki ya nuna cewa ana iya ci gaba...
    Ministar Jin Dadin Jama’a ta Sudan, Salma Ishaq, ta bayyana cewa Mayakan (RSF) sun kashe mata kusan 300 tare da yi wa 25 fyade a El Fasher, babban birnin Jihar Darfur ta Arewa a yammacin Sudan, a matsayin wani bangare na ayyukan kisan kiyashin da suke aikatawa a yankin. A ranar 26 ga Oktoba, dakarun...
    Daga Yusuf Zubairu Kauru  Al’ummar Karamar Hukumar Kauru ta Jihar Kaduna sun shiga halin kaka-ni-ka-yi duba da yadda rayukansu ke kasancewa cikin hadari yayin da suke gonakinsu. A wata tattaunawa ta wayar tarho, wani jagoran matasa, Junaidu Ishaq, ya bayyana cewa kusan shekaru biyar ke nan da hare-haren ’yan bindiga ke ta faruwa akai-akai, wanda...
    Kwankwaso ya kuma buƙaci gwamnatin Tarayya da ta ƙarfafa hulɗar diflomasiyya da Amurka ta hanyar naɗa jakadu na musamman da kuma jakadun dindindin domin kare muradun Nijeriya a matakin ƙasa da ƙasa. “Ya kamata gwamnatin Nijeriya ta naɗa jakadu na musamman da kuma jakadun dindindin domin wakiltar muradunmu yadda ya kamata a kasashen waje,” in...
    Daga Usman Mohammed Zaria   Majalisar Ƙaramar Hukumar Babura ta Jihar Jigawa ta bayar da tallafin abinci ga fursunonin cibiyar gyaran hali ta Babura a matsayin wani ɓangare na ayyukan jin ƙai na majalisar. Yayin ziyarar, Alhaji Hamisu Muhammad Garu ya bayyana cewa, wannan taimako ya biyo bayan lura da bukatun fursunonin yayin da ya...
    ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Ƙasashen Da Ba Su Yanke Hukuncin Kisa A Duniya Ba November 2, 2025 Manyan Labarai 2027: Yadda Gwamnoni Suka Yi Fatali Da Mataimakansu Wajen Zaɓo Waɗanda Za Su Gaje Su November 2, 2025 Manyan Labarai Wadi Al-Salam: Maƙabartar Musulmai Mafi Girma A Duniya November 2, 2025
    Wani fursuna mai suna Abba Hassan, wanda aka yanke wa hukuncin kisa, ya tsere daga gidan gyaran hali na Potiskum da ke Jihar Yobe. Rundunar ’yan sanda ta Jihar, ta tabbatar da wannan lamari a cikin wata sanarwa da kakakinta, DSP Dungus Abdulkarim, ya fitar a ranar Asabar. Tinubu ya yanke hulɗa da Amurka kawai...
      Shugaba Xi ya kara da cewa, a halin da ake ciki yanzu, duniya na fuskantar sauye-sauye irin wadanda ba a taba gani ba kuma cikin sauri. Don haka, kamata ya yi kasashen biyu masu dadaddun wayewar kai su zurfafa koyi da juna, da shigar da sabon kuzari cikin gina cikakken salon hadin kai, bisa...
    Fitaccen Malamin Addinin Musulunci, Sheikh Ahmad Gumi, ya shawarci Shugaba Bola Tinubu da ya ɗauki mataki mai tsauri a kan Shugaban Amurka, Donald Trump, game da barazanar da ya yi na amfani da ƙarfin soja a kan Najeriya. Cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook a ranar Lahadi, malamin ya bayyana cewa...
    A 2022, kasashe shida ne suka daina yanke hukuncin kisa, ko dai gaba daya ko kuma wani bangare. Hudu daga cikinsu; Kazakhstan, Papua New Guinea, Saliyo, Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, sun jingine shi kwatakwata. Ekuatorial Guinea da Zambia sun ce za a rika amfani da shi ne kawai kan laifuka mafiya kololuwar muni. A watan...
    Ga yadda ake hada Fab biskit (wani irin biskit mai dandanon madara da sukari, mai taushi da dan kamshi kamar na “shortbread”). Da farko za ki samu roba haka sai ki zuba sukari da Bota, ki cakuda su da cokali ko maburkaki har sai sun hade jikinsu kuma sun yi laushi. Sannan ki fasa kwai...
    ShareTweetSendShare MASU ALAKA Wasanni Wolves Ta Kori Da Kocinta Vitor Pereira Sakamakon Rashin Nasara November 2, 2025 Wasanni Shin Mene Ne Matsalar Liverpool A Wannan Kakar? November 2, 2025 Wasanni Waye Zai Lashe Ƙyautar Gwarzon Ɗan Wasan Afrika Na 2025? November 1, 2025
    Da yake kaddamar da shirin, Darakta Janar na IRM, Alhaji Anas Muhammad, ya ce an kirkiro da shirin ne domin karfafa zaman lafiya da hadin kai ta hanyar tallafa wa Musulmai da Kiristoci ta bangaren samar da kiwon lafiya da bayar da tallafin kayan abinci da jari.   Ya ce: “Kalubalen lafiya ba sa bambance...
      Bayan an mika damar karbar bakuncin taron kungiyar APEC, kasashen duniya sun soma zura ido kan kasar Sin. Ana sa ran cewa, taron APEC da za a gudanar a Shenzhen, zai kara habaka hadin gwiwa, da samun ci gaba, da wadata tare a shiyyar, kana zai shaida yadda kasar Sin ke kara samar da...
    Tsohon Gwamnan Jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, ya bayyana damuwarsa kan kalaman da Shugaban Amurka, Donald Trump, ya yi game da Najeriya. Kwankwaso, ya yi wannan magana ne bayan Trump ya yi barazanar ɗaukar matakin yaƙi game da zargin kisan kiyashi da ake yi wa Kiristoci. Kisan Kiristoci: Ba zan yaƙi ƙasar iyayena kan labaran...
    Tsohon Gwamnan Jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, ya bayyana damuwarsa kan kalaman da Shugaban Amurka, Donald Trump, ya yi game da Najeriya. Kwankwaso, ya yi wannan magana ne bayan Trump ya yi barazanar ɗaukar matakin yaƙi game da zargin kisan kiyashi da ake yi wa Kiristoci. Kisan Kiristoci: Ba zan yaƙi ƙasar iyayena kan labaran...
    Imam Ali shi ne halifan Annabi Muhammad na hudu a mahangar Ahlussunnan, amma mabiya mazhabar Shi’a na daukar sa a matsayin na farko daga cikin imamansu 12. Wannan ya sanya akasarin mabiya Shi’a na Iraki kan bukaci a binne su a makabartar, kuma sanadiyyar saukin sufuri a zamunnan baya-bayan nan, wasu mabiya Shi’a daga kasashen...
      ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Sin: Katsalandan Cikin Harkokin Kamfani Da Netherlands Ta Yi Ya Kawo Tsaiko Ga Tsarin Masana’antu Da Samar Da Kayayyaki Na Duniya November 1, 2025 Daga Birnin Sin An Gudanar Da Taron Tattaunawa Na Duniya Kan Kirkire-Kirkire Da Bude Kofa Da Ci Gaba Na Bai Daya A...
    Shugaban kasar Iran ya bayyana cewa: Faɗaɗa masana’antar makamashin nukiliyar Iran don inganta rayuwar mutanen kasar ne, ba don makamai ba Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya gana da manyan jami’ai a masana’antar makamashin nukiliya ta ƙasar a lokacin ziyarar da ya kai Hukumar Makamashin Nukiliya ta Iran (AEOI). Shugaban Jamhuriyar Musulunci ta Iran, Masoud...
    Ministan harkokin wajen Iran ya jaddada cewa: Isra’ila ba za ta kai hari kan Iran ba sai da goyon bayan Amurka Ministan harkokin wajen Iran Seyyed Abbas Araqchi ya bayyana cewa: Gwamnatin ‘yan sahayoniyya ba za ta kaddamar da yaki kan Jamhuriyar Musulunci ba tare da samun wata kariya daga Amurka ba. Ya kara da...
    Sakataren Majalisar Tsaron kasar Iran ya jaddada cewa: Ba suna cewa ba za su gudanar da tattaunawa ba ne, amma tattaunawar dole ta kasance ta gaskiya Sakataren Majalisar Tsaron Kasa ta Iran, Ali Larijani, ya tabbatar da cewa: Ba za a iya kwantar da hankalin makiya ta hanyar yin sassauci da rashin gindaya sharaɗi ba....
    Gwamnatin mamayar Isra’ila ta yanke hukuncin kisa kan masu fama da cutar kansa da kuma waɗanda suke fama da matsalar koda na mutuwa a Gaza domin hana fitar da su wata kasa don neman magani Cibiyar Kare Hakkin Dan Adam ta Gaza ta bayyana matukar damuwarta game da tabarbarewar lafiyar marasa lafiya da ke fama...
    Qatar ta bayar da tallafin gaggawa ga mutanen da suka rasa matsugunansu a Sudan Gwamnatin Qatar ta aika da agajin gaggawa da tallafin jin kai zuwa birnin Ad-Dabba da ke Jihar Arewacin Sudan domin rage wa dubban mutanen da suka rasa matsuguninsu da ke tserewa daga El Fasher, babban birnin Jihar Arewacin Darfur. Ma’aikatar Harkokin...
    Wani sojan Ƙasar Amurka ɗan asalin Jihar Kano, Suleiman Isah, wanda yake aiki a rundunar sojin Amurka, ya ce ba zai yaƙi da ƙasarsa ta haihuwa ba saboda yaɗa labaran ƙarya game da yi wa Kiristoci kisan gilla a Najeriya. Isah, wanda ya shiga rundunar sojin Amurka shekaru biyu da suka gabata, yana aiki ne...
    Shi ma wasan da ta yi nasara a kan kungiyar Sifaniya a daf da za a tashi ta ci kwallon a gasar Zakarun Turai da na Newcastle United a Premier League. Tun daga nan alamomi suka fara bayyana cewar akwai tarin matsaloli a Liberpool, wadda kowanne wasa kwallo ke shiga ragarta in ban da wanda...
      Duk da cewa suna da karfi a fannin aikin soja, amma harinsu zai zama tamkar amfani da igwa ne wajen kashe sauro. Duk wani fifikon da suke da shi ba zai dore ba. Saboda haka, a zahiri wannan tambayar da wani mai amfani da yanar gizo ya yi, ta nuna rashin hankali cikin kalaman...
    Yawan shafa man kade a wurin ma yana rage ta sosai. Daga karshe Ina kira ga mata da su daure da zarar sun haihu su fara neman hanyan magance wannan matsalar kuma ku sani cewa wannan hadin gargajiya ne babu Kemikal a cikinsa don haka yana daukar lokaci kafin a ga canji kamar, sati biyu...
    Manajar  ofishin na NIWA,  da ke a jihar ta Legas Injiniya Sarat Braimah ta bayyana cewa, tura ma’ikatan hukumar domin yin aikin, zai taimaka wajen gudanar da aikin a cikin inganci. Kazalika, ya sanar da cewa, hakan zai kuma bayar da damar yin safarar kaya a cikin sauki da kuma safarar matafiya da ke bin...
    A yayin da ake ci gaba da cece-kuce kan kalaman Shugaban Amurka Donald Trump da ke zargin gwamnatin Nijeriya da watsi da batun kisan Kiristoci a ƙasar, Ma’aikatar Yaƙin Amurka ta bayyana cewa ta fara shirin kai farmaki a Nijeriya. Sakataren Ma’aikatar, Pete Hegseth, ne ya tabbatar da hakan cikin wani saƙo da ya wallafa...
      Da yake mayar da martani ga wannan zargin na Amurka, Bwala ya ce gwamnatin Tinubu tana jajircewa wajen kare dukkan ‘yan Nijeriya ba tare da la’akari da addini ba, yana mai cewa Amurka da Nijeriya sun dade suna hadin gwiwa a yaki da ta’addanci.   “Shugaba Bola Tinubu da Shugaba Donald Trump suna da...
     Babban dakaktan hukumar kula da makamashin nukiliya ta Duniya ya tabbatar da cewa Iran ba ta kera makaman nukiliya ba, yana mai jaddada cewa tana ci gaba da kasancewa cikin yarjejeniyar hana yaduwar makaman nukiliya (NPT). Rafael Grossi, ya shaida wa manema labarai a hedikwatar Majalisar Dinkin Duniya da ke New York cewa “Zan iya...
    Sakataren Ma’aikatar Yaki na Amurka, Pete Hegseth, ya ce ma’aikatarsa na shirin daukar matakin soja idan gwamnatin Najeriya ta gaza kawo karshen “kashe-kashen Kiristoci marasa laifi” a kasar. Hegseth, yana mayar da martani ga wani sako da Shugaban Amurka Donald Trump ya wallafa a Truth Social, inda ya zargi gwamnatin Najeriya da yin shiru kan...
    Ofishin yada labarai na gwamnati a Gaza ya musanta zargin da y ace karce ce ” da rundunar sojin Amurka (CENTCOM) ta yi cewa Hamas ta sace wata babbar mota dauke da kayan agaji. “Mun tabbatar da cewa wannan zargin karya ne, kuma wani bangare ne na manufar kafofin watsa labarai da nufin bata sunan...