Gwamnatin Yobe Ta Ɗauki Jami’an Kiwon Lafiya 42 Aiki
Published: 16th, February 2025 GMT
Hukumar kula da lafiya a matakin farko ta Jihar Yobe ta dauki ma’aikatan jinya 42 aiki domin inganta ayyukan kiwon lafiya a jihar.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da kakakin hukumar Adamu Abba ya fitar a Damaturu.
Kifi jinsin Shark ya fusata ya fasa rufin gida Mazabar Tsanyawa/Kunchi ta shafe shekara guda ba tare da wakilci baYa ce tuni babban sakataren hukumar Babagana Machina ya gabatar da wasikun nadin aiki ga ma’aikatan jinya da aka zabo wadanda suka kammala karatun horon su daga kwalejin jinya da ungozoma ta Shehu Sule da ke Damaturu.
Abba ya kara da cewa ma’aikatan jinya za su cike gibin ma’aikata a cibiyoyin kula da lafiya a matakin farko na kananan hukumomi 17 na jihar.
“Gwamnatin Mai Mala Buni ya zuwa yanzu, ta gyara tare da gina sabbin cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko guda 142 a fadin jihar tun daga shekarar 2019.
“Tun lokacin yakin neman zaben da karo na biyu gwamnan ya yi alkawarin samar da ingantaccen cibiyar kula da lafiya a matakin farko a mazabun 178 da ke Jihar Yobe.
“Saboda haka, wannan daukar ma’aikata da aka yi za su ƙara ƙarfin ma’aikata a cibiyoyin don inganta aikin na kiwon lafiya” in Jin Abba.
Sakataren hukumar, Babagana Machina ya taya ma’aikatan jinya murna yana mai umartar da su mayar da hankali wajen sadaukar da kansu ga ayyukansu.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Jihar Yobe jinya Kiwon Lafiya ma aikatan jinya a matakin farko
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamna Namadi Ya Bada Motocin Aiki Goma Ga Rundunar ‘Yan Sanda
Daga Usman Muhammad Zaria
Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya ta yi kira ga mazauna jihar Jigawa da su kasance masu bin doka da oda, tare da yin aiki kafada da kafada da rundunar ‘yan sanda domin tabbatar da tsaro da kwanciyar hankali a fadin jihar.
Kwamishinan ‘Yan Sanda na jihar Jigawa, CP Dahiru Muhammad, ne ya bayyana haka lokacin da ya karɓi sabbin motoci 10 kirar Toyota Hilux da Gwamna Umar Namadi ya bai wa rundunar a Dutse, babban birnin jihar.
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar, SP Lawan Shiisu Adam, ya fitar, CP Dahiru Muhammad ya yaba da jajircewar Gwamna Umar Namadi wajen tallafa wa hukumomin tsaro domin sauke nauyin da ke kansu a jihar.
Ya bayyana cewa, wannan gudummawa ta nuna cikakken kudirin gwamnatin Gwamna Namadi na ƙara inganta harkokin tsaro da kuma tallafawa Rundunar ‘Yan Sanda ta Najeriya wajen aiwatar da aikinta na kare rayuka da dukiyoyin jama’a a fadin jihar.
Kwamishinan ya nuna cewa, waɗannan sabbin motoci 10 za su taimaka matuƙa wajen rage lokacin da ake ɗauka kafin amsa kiran gaggawa, tare da ƙara inganta aikin rundunar a fadin jihar.
Ya ƙara da cewa, za a yi amfani da motocin yadda ya kamata, tare da kula da su don tabbatar da ingantaccen tsaro.
CP Dahiru Muhammad ya kuma sake jaddada aniyar rundunar wajen ci gaba da tabbatar da zaman lafiya, doka da oda, tare da ƙarfafa haɗin gwiwa da sauran hukumomin tsaro da masu ruwa da tsaki.