Ana Fargabar Mutane Da Dama Sun Rasu Sakamakon Ambaliyar Ruwa A Neja
Published: 29th, May 2025 GMT
Ambaliyar dai, ta afku ne sakamakon mamakon ruwan sama da aka shafe sa’o’i da dama yana sauka a daren Laraba.
Wani mazaunin garin, Mohammed Usman ya ce tuni aka fara tsamo gawarwaki da dama a cikin ruwan, amma wasu da dama ba a iya ganin su ba musamman a wuraren da gidaje suka nutse.
Daraktan yada labarai da ayyuka na musamman a Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Neja, Dakta Ibrahim Audu Hussaini, ya tabbatar da faruwar lamarin.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Sin Ta Samar Da Karin Guraben Aikin Yi Miliyan 6.95 A Rabin Farko Na Bana
Alkaluma da aka fitar a hukumance sun nuna cewa, kasar Sin ta samar da sabbin guraben aikin yi miliyan 6.95 a rabin farko na bana, inda ta cimma kaso 58 bisa dari na burinta na shekara.
Kakakin ma’aikatar kula da ma’aikata da walwalar al’umma ta kasar Sin Cui Pengcheng ne ya bayyana haka yayin wani taron manema labarai a yau Talata, inda ya ce a watan Yuni, yawan wadanda ba su da aiki a birane ya tsaya kan kaso 5 bisa dari, watau bai sauya ba daga yadda ya kasance shekara 1 da ya wuce.
Kasar Sin na da burin adadin marasa aikin yi ya tsaya kan kaso 5.5 a bana, tare da burin samar da guraben aikin yi sama da miliyan 12. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp