Firaministan Pakistan na ziyara Tehran mai manufar inganta dangantaka tsakanin kasashen biyu
Published: 26th, May 2025 GMT
Firaministan Pakistan Muhammad Shehbaz Sharif ya na ziyara a birnin Tehran domin inda yake ganawa da manyan jami’an kasar kan muhimman batutuwan da suka shafi kasashen biyu, shiyya-shiyya da kuma duniya baki daya.
A yau litinin ne Sharif ya jagoranci tawaga a Tehran bisa gayyatar da shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya yi masa.
Da yake magana a wata hira da IRNA gabanin ziyarar tasa, Sharif ya yaba da diflomasiyyar zaman lafiya ta Iran a matsayin abin a yaba, yana mai jaddada goyon bayan al’ummarsa ga Jamhuriyar Musulunci.
Ya ce babban makasudin ziyarar tasa a Tehran ita ce nuna godiya ga Iran bisa goyon bayan da ta bayar, musamman yadda ta amince da diflomasiyyar Iran a yankin, a lokacin da Pakistan ke takun saka da Indiya.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Peter Obi Ya Kai Ziyarar Ta’aziyya Ga Iyalan Marigayi Aminu Dantata
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp