Shugaban rundunar mayakan sama ta kasa,Air Marshal, Hassan Abubakar, ya bukaci tsoffin daliban makarantar ‘ya’yan sojoji dake Zaria watau NMS da su kasance masu kwazo da da’a a duk inda suke kamar yadda suka koya a makarantar.

Ya bayyana haka ne lokacin da ya ke jawabi a matsayin Babban bako na musamman a wurin bukin cika shekara 71 da aka gudanar a filin faretin RSM Zakari Kumasi dake harabar makarantar a zaria.

Shugaban rundunar mayakan saman ya bayyana cewa makarantar ta NMS ta yi fice wajen baiwa yara horo a fannonin karatu da kuma ilimin aikin soja wanda hakan ya sa ta samar da manyan sojoji da dama har ma da shi a ciki.

Air Marshal Abubakar ya ce bukin na da matukar muhimmanci gare shi,kasancewar sa tsohon dalibin makarantar.

A don haka sai ya yaba wa makarantar ta NMS bisa kasancewar ta akan turbar da aka santa da shi na samar da jajirtattun sojoji ga rundunar mayakan sama ta kasa tsawon shekaru 71 da kafa ta.

Shi ma a nashi jawabin, shugaban kungiyar tsoffin daliban makarantar, Laftana Kwamanda Sunday Ngegu mai ritaya, ya ce kasancewar shugaban rundunar mayakan sama tsohon dalibi a makarantar ya rinka taimaka wa kungiyar, inda ya bukaci sauran tsoffin daliban da suyi koyi da hakan.

Sunday Ngegu ya kuma yaba wa shugaban rundunar mayakan saman bisa gudunmuwar da ya baiwa kungiyar har ta samu nasarorin da ta samu.

Daliban makarantar sun gudanar da faretin ban girma ga manyan baki,yayin da kuma shugaban rundunar mayakan saman ya kaddamar da dakin shan magani na dalibin da babban dakin cin abinci tare da Kwamandan rundunar soji ta daya da sauran Kwamandodin rundunonin soja gami da mai masaukin baki na NMS.

উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa

কীওয়ার্ড: Zaria shugaban rundunar mayakan a makarantar

এছাড়াও পড়ুন:

Tinubu Ya Gana Da Gwamnonin APC Gabanin Taron Jam’iyyar

Shugaban Kungiyar Gwamnonin Jam’iyyar APC kuma Gwamnan Jihar Imo, Sanata Hope Uzodimma, ya bayyana cewa Gwamnonin APC sun gudanar da wata muhimmiyar ganawa da Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu a Fadar gwamnati da ke Abuja.

Da yake zantawa da manema labarai na Fadar Shugaban Ƙasa bayan kammala taron, Gwamna Uzodimma ya bayyana ganawar da cewa “tattaunawa ce mai muhimmanci da Shugaban Ƙasa domin ƙarfafa jam’iyyar da kuma inganta ikon ta na samar da nagartaccen shugabanci ga ‘yan Najeriya”.

Ya ƙara da cewa, a matsayin su na gwamnoni, sun haɗu da Shugaban Ƙasa domin daidaita matsayin al’amuran jam’iyya da kuma muhimman abubuwan da suka shafi shugabanci.

Da aka tambaye shi ko ana sa ran yanke wasu manyan shawarwari ko takaddama a yayin Taron Kwamitin Zartarwa na Ƙasa (NEC) na jam’iyyar APC da za a gudanar a  gobe Alhamis, gwamnan ya ce, “Ba za mu iya cewa komai yanzu ba har sai mun isa wurin taron gobe.”

Ana sa ran taron na gobe Alhamis 24 ga watan Yulin 2025 zai tattauna kan muhimman batutuwa da suka shafi jam’iyyar da kuma tsara hanyoyin ci gaba da haɗin kai da inganci a harkokin ta.

 

Bello Wakili

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Al’ummar Fegin Mahe Sun Yi Zanga-zanga Kan Kisan Jama’a Da ‘Yan Bindiga Ke Yi
  • Sojoji Sun Kashe Kwamandan Boko Haram Ibn Khalid A Borno
  • Tinubu Ya Gana Da Gwamnonin APC Gabanin Taron Jam’iyyar
  • Babban Hafsan Sojin Iran Ya Ce: Iran Zata Sanya Duk Wanda Ya Dauki Matakin Wuce Gona Kanta Nadama
  •  Kungiyar Malaman Musulmi Ta Yi Fatawar Wajabcin Kawo Karshen Killace Gaza
  • Kasar Sin Na Fatan EU Za Ta Yi Aiki Da Ita Bisa Alkibla Guda Da Tsara Hadin Gwiwa Na Shekaru 50 Masu Zuwa
  • Tsoffin Jami’an ‘Yan Sanda Sun Bukaci A fitar Da Su Daga Cikin Shirin Fansho
  • Wata Kungiyar Ta Bukaci Shugaban Kasa Ya Cika Alkwarin Marigayi Shugaba Buhari Game Da Shehu Usman Aliyu Shagari
  • Birgediya Janar Sabahi Fard Ya Jaddada Cewa: Duk Wani Sabon Hari Kan Iran Zai Fuskanci Martani Mai Gauni
  • Kungiyar Hamas Ta Yi Suka Kan Kame ‘Yan Gwagwarmaya Da Hukumar Falasdinawa Ke Yi