Mene Ne Dalilin Amurka Na Cewa Zata Harba Makamamin Nukiliya Kan Yankin Zirin Gaza?
Published: 25th, May 2025 GMT
Mene ne dalilin da ya sa Amurka da Isra’ila suke barazanar jefa bama-baman nukiliya a Gaza?
Masanin siyasa kuma mai sharhi Abdel Bari Atwan ya rubuta labarin game da barazanar da Amurka ta yi na kai wa Gaza hari da makamin nukiliya, yana mai cewa; “Domin dan majalisar wakilai na jam’iyyar Republican Randy Fein ya yi kira da a kai hari kan Zirin Gaza da bama-baman nukiliya, kwatankwacin abin da kasarsa ta yi a Hiroshima da Nagasaki na Japan, a karshen yakin duniya na biyu, da kuma samun wanda ya yaba masa a gwamnatin Shugaba Donald Trump, wannan shi ne kololuwar ta’addanci, rashin mutuntaka, da kishir ruwan zubar da jini a duniya daga jagororin da ke da’awar kare hakkin bil’adama a duniya kuma daga kasar da ta fi kowace kasa da’awar kare hakkin bil’adama da neman wanzar da adalci a fadin duniya.
Wani abin mamaki shi ne, wannan kira ya fito ne daga wani dan majalisar wakilai na jam’iyyar Republican wanda shugaba Trump ke goyon bayan yakin neman zabensa, da kuma abin takaici, har ma da wasu Larabawa masu kada kuri’a. Wannan kiran na kai harin makamashin Nukiliya ya zo ne a daidai lokacin da Trump ya dawo daga rangadin da ya kai wasu kasashen Larabawa uku, inda ya yi nasarar karbar dala tiriliyan 5, ciki har da wani jirgin sama na shugaban kasa a matsayin kyauta, wanda ya kai kusan rabin dala biliyan daya bayan da aka cika masa kayan aiki.
Wannan dan majalisar mai dauke da akidar ‘yan sahayoniyya ta nuna wariyar al’umma, da bai san adadin mutanen da Benjamin Netanyahu ya zubar da jininsu a yakin kisan kiyashin da ya jagoranta kan Gaza ba, wanda abin koyi ne a cikin kungiyar ‘yan Nazin zamani kuma wadanda ya kashe ya ninka adadin wadanda harin bam din nukiliya guda biyu da aka jefa kan biranen kasar Japan biyu. Kwatanta wannan da yawan al’ummar Zirin Gaza, wadanda ba su wuce miliyan biyu ba, da kuma al’ummar Japan, wadanda aka kiyasta kusan miliyan 124.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
HKI: Sojoji 62 Ne Su Ka Halaka A Gaza A Cikin Wannan Shekara Ta 2025
Jaridar HKI ta “Haaretz'” ta buga labarin da yake cewa: A cikin wannan shekarar ta 2025, sojojinsu da su ka halaka sun kai 62.
A cikin watannin bayan nan an sami karuwar sojojin mamayar da ‘yan gwgawarmaya suke kashewa a Gaza.
Yankin Khan Yunus dake Arewacin Gaza da HKI take riya cewa ta nike shi, sannan kuma ta kori Falasdinawa daga cikinsa, yana daga cikin wuraren da aka yi wa sojojin mamayar kwanton bauna.
Bugu da kari, har yanzu ‘yan gwgawarmayar suna ci gaba da harba makamai masu linzami daga Gaza zuwa matsugunan ‘yan share wuri zauna da suke kusa da Gaza.
A jiya ma dakarun “Sarayal-Quds” na kungiyar Jihadul-Islami ta sanar da harba makamai masu linzami zuwa matsugunan da suke da Gaza.
Jaridar ta “Haaratz’ ta kuma ce, Fira ministan na HKI bai yi wa iyalan ko daya daga cikin iyalan sojojin da aka kashe a Gaza ta’aziyya ba, balle ya gana da su.
Jaridar ta kuma ce, hotunan da ake nunawa na Netanyahu yana ganawa da iyalan sojoji tsoho ne ba sabo ba ne.