Yadda Rashin Ɗaukar Wani Maniyyaci Ya Hana Jirgi Tafiya Har Sai Da Ya Dawo Ya Ɗauke Shi
Published: 29th, May 2025 GMT
Bayan an bari Amer, ya shiga jirgin, suka kama hanyarsu ta tafiya har suka sauka lafiya wanda hakan ya sa ma’aikatan jirgin suka ɗauki hoton da shi don tarihi, inda a ɗayan ɓangaren mutane da dama ke suffanta lamarin a matsayin hujjar ƙarfin niyya da ikon Allah.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku.
এছাড়াও পড়ুন:
Yadda aka mayar da yaran da aka sace a Kano masu wanke-wanke a Kudu
Aisha Muhammad Abdullahi ’yar shekaru 7 ba ta da masaniyar irin hadarin da ke gaba yayin da mahaifiyarta ta aike ta ta sayo sinadarin hada lemon zoborodo amma ta manta ba ta sayo kankara ba wanda hakan ya sa ta juya.
A daidai wannan lokacin ne wata mace wacce ke bin ta a baya ta kirayi Aisha ta kuma ba ta alewa sannan ta bukaci ta bi ta.
Abin da Aisha za ta iya tunawa kawai shi ne ta farka daga barci ta ganta a garin Onitsha na Jihar Anambra a hannun wata mace mai suna Ebere.
Tinubu ya fi mayar da hankali wajen gina Kudancin Nijeriya — Kwankwaso An rantsar da Nentawe sabon shugaban APC na ƙasaAisha na cikin yara 9 ’yan Jihar Kano da aka sace zuwa Kudu da wani mai suna Paul Onwe ke yi don sayar da su ga masu neman yaran domin aikatau ko kuma sauya musu addini a Kudu.
Da take ba da labarin yadda aka canja mata suna zuwa Ijeoma tare da yi mata aski a garin Onitsha, Aisha ta ce a kan titi aka sace ta ba tare da sani iyayenta ba.
“Lokacin da aka sace ni an aike ni ne inda aka mika ni hannun wata mace mai suna Ebere da take sana’ar sayar da abinci kamar shinkafa, agbu da tuwon semovita.
“Ta sanya mu a makarantar Boko wanda idan mun taso muke zuwa shagon abinci domin wanke-wanken kwanukan da aka yi amfani da su sannan ta ba mu abinci kafin mu koma gida idan goman dare ta yi.
“Na hadu da Faruk wanda aka canjawa suna zuwa Onyeduka. Mu biyu muke zuwa makarantar Divine International da kuma Coci wanda ba zan iya tuna sunan ba a yanzu, amma dai ranar Lahadi da Labara muke zuwa duk mako.
“Daga baya ba a yarda mun je wani babban taron cocin na shekara-shekara a Abuja ba, kuma ba a dade da yin hakan ba aka kubutar da mu muka dawo gida hannun iyayenmu,” in ji Aisha wadda yanzu haka ta kai shekaru 15.
‘Ko tunanin iyayena ba ni da lokacin yi a can’
Ta ce lokacin da take Kudu ba ta tunanin iyayenta a Kano saboda daga zuwa makaranta sai aikin wanke-wanken kwanukan abinci take yi.
Kuma har yanzu shekaru 6 bayan kubutar da su tana iya tuna wasu yaran da suka yi makaranta a Onitsha kamar wata Chinaza.
Ta ce ita da Faruk ba sa magana da Hausa domin ba su da abokai Hausawa kuma sauran abokansu da Ibo ko Turanci suke magana.
Yanzu haka Aisha na aji biyu a babbar sakandaren Kawaji ta Mata kuma ta ce tun bayan kubutar su sau daya ta sake ganin Faruk a nan Kano.
Muhammad Babangida, wani malami ya ce tun da Aisha ta dawo makarantar tana nuna hazaka kuma tana karatun kimiyya ne duk da cewa ba ta fiye magana da wadanda ba ta sani ba.
Ya ce ana boye wa malamai da sauran dalibai labarin sace ta da kubutar da ita kamar yadda iyayenta suka nema domin gudun nuna mata wariya.
Wasu ’yan ajin su Aisha, Khadija M Usman da Amina Isyaku Isah, sun ce Aisha yarinya ce mai faran-faran da jama’a lokacin da suka kai mata wata ziyara a gidansu.
Shi ma Umar Faruk Ibrahim, wanda aka sace zuwa Kudu kamar Aisha, bai fi shekara 6 ba lokacin da aka kai shi Onitsha, inda aka mayar da shi dan wanke-wanken kwanukan abinci bayan mayar da shi addinin Kiristanci.
To sai dai wanda ya ke kitsa sayar da yaran, Paul Onwe ya shiga komar jami’an tsaro a shekarar 2019 yayin da ya ke yunkurin satar wani yaron a Kano, kuma Mai Shari’a Zuwaira Yusuf ta Babbar Kotun Kano ta daure shi shekaru 107 a gidan gyaran hali a ranar 10 ga watan Yuli na shekarar 2021.
Sauran mambobin kungiyar barayin yaran da suka hada da Ebere Ogbono, Emmanuel Igwe, Loius Duru, Monica Orcha da Chinelo Ifedangu sun sami hukunci daurin shekaru 120 a gidan gyaran hali bayan daukar shekaru 6 ana shari’a.
Yadda Faruk ya koma Onyeduka
Da yake tuna irin halin da ya samu kansa lokacin aka sace shi zuwa Onitsha, Umar Faruk wanda yanzu shekarunsa sun kai 16, ya ce yara da yawa a yankin unguwar Dakata sun san Paul Onwe da matarsa Mercy, domin haka ba wanda ya ke tsammanin za su yi irin wannan danyen aikin na sayar da yara har zuwa Onitsha.
“Ina da shekaru 6 lokacin da aka sace ni zuwa Onitsha, inda na shafe shekaru 5 ina aikatau. An canja mun suna zuwa Onyeduka tare da mayar da ni addinin Kiristanci.
“Ina aikin a hannun wata mace mai sayar da abinci da take samar wa mutane yara. Aikina shi ne wanke-wanken kwanukan abinci. Tana ba mu abinci ta kuma sanya mu a makarantar Boko tare da zuwa coci ko da wane lokaci,” in ji Faruk.
Ya kara da cewa ’yan sanda sun kai sumame gidan matar, inda suka kubutar da shi da wasu yaran lokacin yana da shekaru 11.
Faruk dan shekaru 16 a yanzu ya ce ba zai iya tuna yaran da suka yi makaranta a Onitsha ba, amma zai iya tuna Ijeoma (watau Aisha) da suka zauna a gida daya.
Yanzu haka Faruk yana zuwa Babbar Sakandaren Brilliant International, wata makaranta mai zaman kanta a Kano. Ya kuma ce har yanzu yana da abokai ’yan kabilar Ibo a makarantar kamar Chukwuemeka da Ifeanyi, duk kuwa da cewa yanzu bai iya magana da yaren na Ibo ba.
An dauki lokaci mai tsawo kafin Aisha da Faruk su koyi magana da harshen Hausa bayan kubutar da su.
’Yarmu ta kasa gane mu lokacin da aka kubutar da ita – Mahaifiyar A’isha
Khadija Awwalu Muhammad ita ce mahaifiyar Aisha, ta ce lokacin da aka kubutar da ’yarsu ba ta gane iyayenta ba bayan an kawo su Kano, amma mahaifinta, Muhammad Abdullahi shi ya gane ta duk kuwa da aske mata gashi da aka yi.
“Ba za mu iya lissafa dararen da ban yi barci ba tun lokacin da aka sace min diya, to amma a matsayinmu na musulmi ba mu gushe ba muna addu’ar Allah Ya kubutar da su.
“Abin da ya fi tayar min da hankali shi ne yadda aka sauya mata suna zuwa Ijeoma a lokacin da take a Anambra. Sannan abin da muka koya daga wannan shi ne rashin yanke tsammani a irin wannan mummunan hali, muka ci gaba da addu’ar har Allah Ya kawo mana agajinsa,” in ji uwar Aisha.
Babban kalubalen da iyayen Aisha da Faruk suka fuskanta shi ne yadda za su yi magana da harshen Hausa domin yaren ya bace musu da kuma abin da ya shafi abinci domin ba sa iya cin abincin Hausawa sai dai Aɓu da sauran abinci ƙabilar Ibo.
“Amma a hankali ana ba ta kwai da doya da kuma shayi har ta fara cin abincinmu na gida,” a cewar Muhammad Abdullahi, mahaifin Aisha.
Ta hanyar cudanya da sauran yara, Aisha da Faruk suka fara koyon magana da harshen Hausa kuma suka fara mantawa da harshen Ibo duk da cewa suna iya fahimtar abin da ake cewa a cikin harshen.
Wani yaro mai suna Haruna Sagir dan kimanin shekrau hudu da Paul Onwe da ’yan kungiyarsa suka yi kokarin sacewa, amma Allah bai ba su sa’a ba, domin kuwa bayan kai gidansu a Dakata, inda ya shafe kwanaki uku da yi masa aski kafin daukansa zuwa Onitsha, sai aka kama Paul Onwe yayin da ya yi yunkurin kai yaron Sabon Gari a cikin Adaidaita Sahu domin hawa motar tafiya Kudu.
“Abin da ya faru kuwa shi ne lokacin da mai Adaidaita Sahun ya tsaya domin daukar fasinja, sai gardama ta kaure tsakaninsa da Paul kan ya zai bata masa lokaci, to ana cikin haka sai ga uwar yaron, inda ta gane danta, kuma nan take ta cire masa hular da ke kansa ta kuma kwarma ihu a kawo mata taimako.
“Nan da nan ’yan sanda suka cafke Paul wanda mutane ke kokarin yi masa hukunci nan take.
“Daga nan aka gano yara 9 da Paul Onwe da abokansa suka sace zuwa Kudu wanda hakan ya sa Gwamnatin Kano ta kafa kwamiti karkashin jagorancin Mai Shari’a Wada Rano, kuma a cikin rahoton da kwamitin ya bayyana cewa yara 108 ne suka bace daga Kano.
Wani yaro, Abubakar Ismail Ibrahim da aka sace yana dan shekaru 4 a 2017, har yanzu ba gano shi ba.
Mahaifin Ismail Ibrahim, wanda shi ne shugaban iyayen yara da aka sace daga Kano, ya shaida wa Aminiya cewa har yanzu yana sa ran zai ga dan nasa musamman ganin yadda aka kara gano masu sayar da yara suna kai su Kudu.
Wata Mai fafutukar kare ’yanci yara kanana, Aisha Haruna Kabuga, ta ce ya kamata a samu horo mai tsanani ga duk wanda aka samu da aikata wannan laifin domin hana faruwar hakan nan gaba.
Ta ce tilas iyaye su kula da yaransu domin barayin yara na yawo kwararo-kwararo domin samun dama kan yaran da ba a kula da su ba. Ta yi kira ga gwamnati kan kada ta gajiya wajen ganin an kubutar da sauran yaran da aka sace aka kai su Kudu.
Jami’an Hukumar Yaki da Fataucin Mutane ta NAPTIP, ba su komai kan yadda za a shawo kan Matsalar sace-sacen kananan yara da kuma abin da hukumar ke yi wajen dakile afkuwar hakan.
Wani jami’i da ba ya son a ambaci sunansa, ya ce abin da hukumar take yi shi ne fadakarwa da kuma sa ido kan aikace-aikacen masu satar yara da nufin hana afkuwar hakan.