2025-05-31@23:27:21 GMT
إجمالي نتائج البحث: 5208

«harkokin ilimi da noma»:

    Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, ya gana da ministan harkokin wajen kasar Kamaru Lejeune Mbella Mbella a jiya Jumma’a, wanda ya je Hong Kong don halartar bikin rattaba hannu kan yarjejeniyar kafa hukumar shiga tsakani ta kasa da kasa mai lakabin “IOMed” a Turance. A yayin ganawar, Wang ya nuna jin dadinsa kan...
    Ƙungiyar Gwamnonin Jihohin Arewa ta bayyana ambaliyar ruwa mai tsanani da ta faru a Mokwa, Jihar Neja, a matsayin babbar ibtila’i, yana mai kira da a ɗauki matakan gaggawa don tallafi da hana sake faruwar hakan. Shugaban Kungiyar kuma Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya bayyana haka a yayin mika ta’aziyyarsa ga gwamnati da...
    Gwaman ya umarci mai rikon mukamin Shugaban ma’aikata, Hukumar bada tallafin karatu ta Jihar, ma’aikatar ilimi,da kuma kungiyar APWEN reshen Maiduguri cewar wadanda suka cika sharuddan da ake bukata ya dace a basu tallafin na karatu. Lokacin taron ya taya Shugabnnin kungiyar amsu barin gado da kuma wadanda za su gaje su kan jajircewar da...
    Bayan mintuna 90 na wasan ba tareda wani ya doke wani ba sai alkalin wasa ya bayar da damar bugun daga kai sai mai tsaron raga, Jamaica ta ci kwallaye 4 inda Nijeriya ta ci dukkan kwallaye 5 da yan wasan suka buga, hakan ya sa yaran na Eric Chelle suka lashe gasar Unity Cup...
    An gudanar da bikin cika shekaru 30 da kafuwar asusun hadin gwiwar kasashe masu tasowa na MDD a birnin New York, babban birnin Amurka. Yayin bikin, zaunannen wakilin Sin dake MDD, Fu Cong, ya fitar da jawabi cewa, bangaren Sin ya yaba da sakamakon hadin gwiwa mai inganci da asusun ke goyon baya. Kuma Sin...
    Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bayyana cewa JMI ta gina shirinta na makamashin nukliya ne kan fahinta da kuma kundin tsarin mulkin kasar wanda yayi tir da mamaya da kuma babakere. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto ministan yana fadar haka a safiyar yau Asabar a hubbaren Imam Ruhullah...
    Kamfanin Barakat, mai samar da magunguna a nan JMI ya kaddamarda sabbin magunguna har 23 wanda kamfanin ya samar a cikin gida daga ciki har da riga kafi mai suna HPV. Kamfanin dilancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa wannan ci gaban da kamfanin Barakat ya samu mataki ne mai girma a fagen...
    “Gane amfanin lamarin da ya shafi ilimi shi yasa, Gwamna Lawal ya kaddamar da dokar ta baci a bangaren ilimi a watan Nuwamba 2023,matakin da aka dauka an yi sa’a ya haifar da da mai ido a bangaren ilimi a Jihar Zamfara. “Fiye da makarantu 500 aka y masu kwaskwarima da samar masu abubuwan da...
    Kungiyar Gwamnonin Najeriya (NGF) ta bayyana alhininta bisa rasuwar wasu ‘yan wasa daga jihar Kano a wani hadarin mota. A cikin wata sanarwa da shugaban kungiyar kuma gwamnan jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq ya fitar, ya ce hadarin ya faru ne yayin da tawagar jihar ke dawowa daga gasar wasanni ta kasa da aka kammala a...
    A karon farko, rundunar tsaron Indiya ta tabbatar da cewa ta rasa wasu jiragen yaƙi a yayin arangama mai tsanani da suka fafata da Pakistan a farkon watan Mayu. Wannan sanarwa ta fito ne daga bakin Babban Hafsan Tsaro na Indiya, Anil Chauhan, a taron Shangri-La Dialogue, babban taron tsaro na Asiya, a Singapore. Tun...
    Kungiyar Hamas wacce take iko da zirin gaza ta bukaci masu shiga tsakanin Amurkawa su ngamtar da ita kan cewa HKI zata dakatar da yaki ta kuma fice daga zirin gaza. Amma shawarar da Steve Witkoff ya gabatar bata kunshi wani abu wanda zaia gamsar da kungiyar ta amince da wani sulhu ba. Jihad Taha...
    Masu zanga zanga kimani makunni uku da suka gabata a kasar Libya sun bukaci firai ministan kasar Abdulhamid Dubba ya sauka saboda shi ne ya haddasa rikicin da ya faru a cikin yan makonnin da suka gabata a kasar. Shafin yanar gizo na labarai Africa News ya bayyana cewa masu zanga zanga kimani 200 sun...
    Shugaban hukumar bada agajin gaggawa a jihar Naija na tarayyar Najeriya NSEMA ya basa sanarwan cewa yawan mutanen da suka rasa rayukansu sanadiyyar ambaliyar ruwa a ranar Alhamis data gabata a karamar hukumar Mokwa ya kai 151 bayan an sake gano karin gawakin mutane 36. Jaridar Daily Trust ta Najeriya ta nakalto Abdullahi Arah yana...
    Hukumomin ƙasar Saudiyya sun sanar cewa a bana za a gabatar wa mahajjata huɗubar Ranar a cikin harsuna uku na Najeriya. Harsunan Najeriya guda uku da za a gabatar da Huɗubar Ranar Arfa da su sun ne Hausa da Fulatanci da kuma Yarbaci. Harsunan huda uku na daga cikin  karin harsunan duniya guda 34 da...
    A ganin kasar Sin, kafuwar hukumar za ta ba da damar kara shigar da kasashe masu tasowa cikin aikin kula da al’amuran duniya, da tabbatar da daidaita rikici ta wata hanya mai adalci, da bai wa kasashe masu tasowa karin ikon fadin albarkacin bakinsu.   A shekarun baya, kasar Sin ta taimaka wajen tabbatar da...
    Ƙungiyar Gwamnonin Nijeriya (NGF) ta bayyana baƙin ciki da alhini kan mummunan haɗarin mota da ya yi ajalin wasu ‘yan wasa daga jihar Kano, yayin da suke dawowa daga gasar wasanni ta ƙasa da aka kammala a jihar Ogun. Shugaban NGF kuma gwamnan jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq, ya fitar da wata sanarwa da ya sanya...
    Aƙalla mutum 20 ne aka tabbatar sun mutu sakamakon wani mummunan hatsarin mota da ya rutsa da tawagar Jihar Kano da ke dawowa daga gasar wasannin motsa jiki ta ƙasa (NSF) da aka kammala a Jihar Ogun. Lamarin na ban tausayi ya faru ne a ranar Asabar a garin Dakatsalle, kimanin kilomita 50 daga Kano,...
    Aƙalla ‘yan wasa 20 daga tawagar jihar Kano ne suka rasu, yayin da da dama suka jikkata,  sakamakon mummunan hatsarin mota da ya faru a gadar Dakatsalle, sa’ilin da suke dawowa daga Gasar Wasanni ta Kasa da aka kammala kwanan nan a Abeokuta. Shugaban Hukumar Wasanni ta Jihar Kano, Umar Bala Fagge, ya tabbatar da...
    Kyaftin din tawagar Super Eagles ta Nijeriya Ahmed Musa, ya auri matarsa ta 4, Asmau Moriki, a wani biki na sirri da aka gudanar a jihar Kano, Musa da amaryarshi Asmau sun zama mata da miji watanni kadan bayan haduwarsu, Musa ya bar sansanin tawagar Super Eagles dake birnin Landan domin ya halarci bikin wanda...
    A kwanan baya, tsohuwar firaministar kasar New Zealand, Madam Jennifer Shipley, ta yi hira da wakilin CMG, inda ta ce, ya dace a koyi ingantattun dabarun kasar Sin a fannin raya kasa. Ta ce yadda kasar Sin ta gabatar da shawarar tabbatar da ci gaban duniya, da bai wa sauran kasashe dabaru da fasahohin da...
    A wancan lokacin, sojojin Nijeriya sun musanta batun Shehun Borno, amma wasu na ganin cewa akwai kashan gaskiya dangane da wannan al’amari, sakamakon irin yadda ‘yan ta’addan ke cin karensu babu babbaka a wadannan yankuna. Shi ma a nasa bangaren, mai sharhi kan kungiyoyin ta’addanci a Cibiyar Tony Blair, Barista Bulama Bukarti, ya ce, “A...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Wannan shi ne babban abin alfahari da Ministan Harkokin Waje, Ambasada Yusuf Maitama Tuggar ke jagoranta. A yayin tattaunawar manyan jami’an biyu a Berlin tare da ministan harkokin wajen Jamus Johann Wadephul, Tuggar ya nuna bajinta. “Ba manufar Nijeriya bace ta fitar da mutane zuwa wasu kasashen waje ba, sai don nuna gwanayenta,” in ji...
    Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, ya soki tsarin shugabanci na Najeriya na yanzu, inda ya bayyana cewa ‘’yan bindigar birni’ sun karɓe ragamar mulkin ƙasar. Ya yi wannan jawabi ne a ranar Asabar a Abuja, yayin taron lacca na cika shekaru 60 da haihuwar tsohon Gwamnan Jihar Rivers, Rotimi Amaechi, mai taken ‘Amfani...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Wadanda ake zaton mawallafin wasikar sun yi jayayya cewa ya kamata a janye tuhumar da ake yi wa Giwa saboda “adalci, daidaito, da aiki mai kyau.” Giwa, tare da mai kula da kadarorin Cecil Osakwe da sauran su, za a gurfanar da su a gaban kuliya bisa tuhume-tuhume guda tara da suka hada da fitar...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Adadin mutanen da suka mutu a mummunar ibtila’in ambaliya a Jihar Neja ya karu zuwa mutum 151. Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Neja (NSEMA) ce ta sanar cewa mutane 11 sun jikkata, yayin da mutane 3,018 suka rasa matsuguninsu a ibtila’in na ƙaramar hukumar Mokwa a safiyar Asabar. Kakakin hukumar, Ibrahim Hussaini, ya...
    Adadin mutanen da suka mutu a mummunar ibtila’in ambaliya a Jihar Neja ya karu zuwa mutum 151. Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Neja (NSEMA) ce ta sanar cewa mutane 11 sun jikkata, yayin da mutane 3,018 suka rasa matsuguninsu a ibtila’in na ƙaramar hukumar Mokwa a safiyar Asabar. Kakakin hukumar, Ibrahim Hussaini, ya...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Hukumomi na roƙon mazauna yankunan da ambaliya ta shafa da su bi umarnin kwashe jama’a daga yankunan da ke cikin haɗari tare da haɗa kai da jami’an agaji don tabbatar da tsaron lafiyar kowa da kowa. A cikin sanarwar, Gwamnatin Tarayya ta miƙa saƙon ta’aziyya ga iyalan waɗanda suka rasu, tare da jaddada cewa al’ummar...
    Limamin da ya jagoranci sallar Jumu’a a birnin Tehran ya jaddada cewa: Ba za su taba yin watsi da ‘yancin su na mallakar makamashin nukiliya na zaman lafiya ba Limamin da ya jagoranci sallar Juma’a a birnin Tehran fadar mulkin Jamhuriyar Musulunci ta Iran, Ayatullah Sayyid Ahmad Khatami, ya jaddada cewa: Iran ba ta neman...
    Mazauna Babban Birnin Tarayya za su fuskanci katsewar ruwan sha na tsawon makonni biyu, kamar yadda Hukumar Kula da Ruwa ta yankin ta sanar. Rashin ruwan, wanda ya fara ranar Juma’a, 30 ga Mayu, ana sa ran za ta ci gaba har zuwa ranar Juma’a, 13 ga Yuni. Matsalar ta samo asali ne daga ayyukan...
    Likitocin Iran sun yi bikin murnar nasarar da ta samu na dasa na’urar dawo da ji da inganta shi ga masu matsalar kurmantaka da raunin ji a lardin Khuzestan na kasar Ƙaunar sana’a, dagewa, da sadaukarwa sune sirrin nasarar kowane aiki da hidimar jin kai. Waɗannan kalaman ne Farfesa Nadir Al-Saki ya fara bude jawabinsa...
    Bangarorin ‘yan gwagwarmayar Falasdinawa sun kai hari kan sojojin mamaya a wani farmakin hadin gwiwa da suka kai a Khan Yunus Dakarun Sarayal-Quds bangaren sojin kungiyar Jihadul-Islami da kuma dakarun Izzuddeen Al-Qassam bangaren sojin kungiyar gwagwagrmayar Musulunci ta Hamas sun tabbatar da cewa: Sun yi nasarar kashe sojojin mamayar Isra’ila tare da raunata wasu a...
    Dakarun gwagwarmayar kasar Yemen sun bayyana cewa: Za su mayar da jiragen saman yakin gwamnatin mamayar Isra’ila abin ba’a Shugaban majalisar koli ta siyasar kasar Yemen Mahdi al-Mashat, ya tabbatar da cewa: Tsaron sararin samaniyar sojojin kasar Yemen zai iya tunkarar jiragen saman yakin gwamnatin mamayar Isra’ila da suke kai hare-haren wuce gona da iri...
    Cutar kwalara ta yadu a Sudan, kuma ‘yan tawayen dakarun kai daukin gaggawa sun kai hare-hare kan asibitoci biyu a Jihar El Obeid na kasar Sudan na ci gaba da fama da tabarbarewar yanayin tsaro da lafiya bisa la’akari da abubuwan da ke faruwa a baya-bayan nan. A bangaren tsaro kuma, Dakarun Kai Daukin Gaggawa...
    Haka zalika, ya kara da cewa; gwamnatinsa ta bayar da kimanin Naira biliyan biyu, domin noma hekta 1,000 na gonaki ta hanyar amfani da na’urar noman rani mai amfani da hasken rana a garin Baga. Gwamna Zulum ya ci gaba da cewa, kwanan nan ya tura wata tawagar bincike, don yin bincike tare da gano...
    Jami’ar Jos ce ta zama gwarzon gasar wasannin ma’aikatan jami’o’in Nijeriya karo na 14 (NUSSA), wadda Jami’ar Bayero da ke Kano ta karɓi bakuncinta. Jami’ar ta Jos ta lashe lambobin yabo guda 13, ciki har da Zinare 7, Azurfa 3 da Tagulla 3, wanda ya ba ta damar darewa saman teburin nasarori. A matsayi na...
    Maƙabartar Kuka Bulukiya maƙabarta ce mai daɗaɗɗen tarihi a cikin ƙwaryar birnin Kano, wadda bayanai suka nuna an shafe sama da shekara 500 ana binne mamata a cikinta. Wannan daɗaɗɗiyar maƙabarta tana da matuƙar muhimmanci musamman la’akari da yawan unguwannin da suka kewaye ta da yawan mutanen da aka binne a cikinta da kuma fitattun...
    A jawabinsa a wajen rabbata hannun yarjejeniyar, jami’in shirin na jihar ta Gwambe, Farfesa Usman Bello Abubakar, ya danganta wannan aiki a matsayin wani babban ci gaba a jihar. Ya kara da cewa, aikin ba kawai wurin yanka dabbobi ba ne, akwai kuma batun zuba hannun jari ga ci gaban kiwon su kansu dabbobin. A...
    Sojoji sun yi nasarar cafke wani mutum da ake zargi dan ta’adda ne tare da gano ma’adanar makamai a yayin wani samame da suka yi a Ƙaramar Hukumar Bassa ta Jihar Filato. Binciken farko ya nuna cewa wanda aka kama ɗin yana da alaƙa da wata ƙungiyar masu aikata laifuka da ke da alhakin kisan...
      A wani yunƙuri na ƙarfafa ilimi mai inganci, adalci da shigar da kowa a cikinsa ga yara da matasa a Jihar Kaduna, ƙungiyar Save the Children ta shirya taron bita na kwana biyu ga yan jarida da kungiyoyi masu zaman kansu a Kaduna.   Taron ya haɗa wakilai daga sashen ilimi, kafafen yaɗa labarai...
    Shugaban na Faransa ya ce Faransa za ta iya sanya takunkumi ga gwamnatin Isra’ila matukar ba ta kawo karshen killace Gaza ba, inda kuma ya bukaci kasashen duniya da kada su jajirce wajen tunkarar matsalar karancin abinci a Gaza. A wani taron manema labarai a Singapore a ranar Juma’a, Macron ya ce dole ne Turawa...
    Ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ta kirayi babbar mai kula da harkokin kasar Ostiriya da ke birnin Tehran domin nuna rashin amincewa da zarge-zargen data danganta da na ‘’tsokana” da hukumar leken asirin cikin gidan kasar ta Turai ta yi dangane da shirin nukiliyar Iran na zaman lafiya. Shugaban ofishin sashen yammacin Turai na ma’aikatar...
    Kungiyar ‘yan ta’adda ta Daesh ta dauki alhakin kai hari kan dakarun gwamnatin Hayat Tahrir al-Sham (HTC) na kasar Siriya, wanda shi ne irinsa na farko a kan tsoffin kawayenta tun bayan hambarar da gwamnatin Bashar al-Assad na Siriya. A wata sanarwa da ta fitar kungiyar ta ce ta sanya “bama-bamai” kan motar dakarun da...
    Jami’in kula da ayyukan jin kai na Majalisar Dinkin Duniya ya ce matakin da Isra’ila ta dauka na hana agajin abinci ga Falasdinawa da ke fama da yunwa a yankin Zirin Gaza da aka yi wa kawanya ya zama laifin yaki. “Muna ganin abinci dake jibge a kan iyakoki kuma ba a ba da izinin...
    “Ya zamar mana wajbi, mu kulla wannan hadakar, musamman domoin mu tabbatar da cewa, mun tsaftace tsarin,” Inji Dantsoho. Ya kara da cewa, wannan aikin, ba wai kawai za kara habaka samar da kariya da kuma kara ingnata tsaro bane, har da kuma bayar da gagarumar gudunmawa, wajen kara ciyar da tattalin arzikin kasar nan...
    Burkina faso ta musanta labaren da ake yayatawa na aikata kisan kiyashi a arewacin kasar. Ministan Tsaron kasra na mayar da martani ne ga labarin da aka buga a wannan Alhamis, na RFI, na kisan kiyashi da kungiyar sa kai ta kasar (VDP) ta yi a kauyukan Dori da Gorgadji. Ministan Tsaron Burkina Faso ya...
    Ya ce a nemi bayani daga wurare daban-daban kamar Kungiyar Ma’aikatan Kananan Hukumomin Nijeriya (NULGE) da Ma’aikatar Kudi, ya kara da cewa sakataren gwamnatin tarayya shi ne shugaban kwamitin aiwatar da hukuncin. Abubuwan da mutane yawa suke gnin ya janyo jinkirta aiwatar da hukuncin shi ne, shigar da sabon sharadi daga Babban Bankin Nijeriya (CBN),...