2025-09-17@23:24:26 GMT
إجمالي نتائج البحث: 84
«Asusun yara ta majalisar dinkin duniya»:
Hukumar Kula da Inshorar Lafiya ta Kasa (NHIA) a ranar Laraba ta kaddamar da shirin bayar da kulawar lafiyar gaggawa kyauta ga yara a Asibitin Koyarwa na Aminu Kano (AKTH), Kano. Shirin, a cewar Darakta a hukumar, Dr. Salahudeen Sikiru, wani bangare ne na fadada shirin lafiyar iyaye da NHIA ke aiwatarwa zuwa ga yara...
Dukkanin kamfanonin sun roƙi abokan hulɗarsu da su yi haƙuri, inda suka ce injiniyoyi na aiki don gyara wutar. Hukumomi sun tabbatar da cewa ana ƙoƙarin gyara wutar lantarkin yanzu haka. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga...
A ƙoƙarinta na daƙile matsalar cin zarafin yara, rundunar ’yan sandan Jihar Kebbi ta ce ta samu nasarar kama wasu mutum biyu da ake zargi da yi wa ƙananan yara fyaɗe a makon jiya. Wakilinmu ya ruwaito cewa, wata yarinya ’yar kimanin shekaru 10 da ke Unguwar Bedi a ƙaramar hukumar Zuru, ta faɗa mummunan...
Dakarun sojin Najeriya sun kashe wani kasurgumin dan ta’adda wanda aka fi sani da suna Kachalla Bala da yaransa biyar a Jihar Kogi. Sojojin Birget ta 12 da ke Lakwaja, hedikwatar jihar sun kuma yi nasarar ceto wasu mutanen da gungun ’yan bindigar suka yi garkuwa da su. Mukaddashin kakakin rundunar, Laftanar Hassan Abdullahi ya...
Kasashe takwas, ciki har da Pakistan, Morocco, Syriya, Libya, Jordan, Lebanon da kuma Masar, sun himmatu wajen bayar da fifikon kula da cutar kansa ta yara, ta hanyar kula da ka’idojin kasa, ta hanyar yin gwajin cutar da a kan lokaci, samar da ingantattun magunguna da kuma samar da kudade don bai wa iyali kariya....
Gwamnatin Jihar Gombe tare da haɗin gwiwar ƙungiyar Rotary International sun ƙaddamar da shirin aikin jinya domin rage mace-macen mata da yara a faɗin jihar. Shirin da aka gudanar a Ƙananan hukumomi uku da suka haɗa: Gombe da Kaltungo da Yamaltu-Deba, inda aka yi wa jama’a gwaje-gwaje, jinya da wayar da kai a unguwannin Yelenguruza...
Ya yi alkawarin cewa, gwamnatinsa za ta kara hada kai da hukumomin tsaro domin dawo da zaman lafiya, tare da samar da kayayyakin agaji da tallafi ga wadanda abin ya shafa. Majiyoyin yankin sun ce al’ummar yankin sun sha fama da hare-hare akai-akai a ‘yan makonnin da suka gabata, lamarin da ya tilastawa mazauna...

Gwamnati Ta Fara Aikin Gyara Na’urar Watsa Shirye-shirye Mai Gajeren Zango Ta Gidan Rediyon Muryar Nijeriya
Idris ya gode wa Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu bisa hangen nesan sa da jajircewar sa wajen zamanantar da kayan aikin yaɗa labarai a Nijeriya. A cewar sa: “Yayin da muke ɗaukar wannan babban mataki na ƙaddamar kwangilar gyara tiransimitar ‘shortwave’ ta Muryar Nijeriya mai ƙarfin kilowat 250, ya dace mu nuna ɗimbin godiyar...
Yara 2 sun mutu wasu 6 sun jikkata bayan tashin bom a yankin Ƙofa Biyu da ke Ƙaramar Hukumar Konduga a Jihar Borno. Shaidu a garin sun shaida wa wakilinmu cewa bom ɗin ya tashi ne bayan yaran sun kawo shi gida bisa rashin sani. Sun shaida wa wakilinmu cewa yaran sun kawo bam ɗin...
Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya shawarci matasan da ake ribatarsu a matsayin ’yan daban siyasa da suka tuba da su guji tashin hankali, yana tabbatar musu da shirye-shiryen gwamnatinsa na gyara tarbiyarsu tare da mayar da su cikin al’umma. Gwamnan ya yi wannan alkawari ne a taron wuni ɗaya da aka gudanar tare da...
Majalisar zartarwa ta karamar hukumar Sule Tankarkar dake Jihar Jigawa ta amince da gudanar da muhimman ayyuka a bangarorin kiwon lafiya da sauran aikace-aikacen ci gaban al’umma. Taron majalissar bisa jagorancin shugaban Karamar Hukumar, Alhaji Tasi’u Adamu, ya kuma amince da gina makarantun Tsangaya guda 3 na zamani da za’a sanyawa sunayen wasu fitattun...
Majalisar zartaswar jihar Sokoto a karkashin jagorancin Gwamna Ahmed Aliyu ta amince da kashe kudade wajen ayyuka a sassa daban daban nufin tabbatar da amana da aka dora wa gwamnati. Da yake karin haske ga manema labarai yayin taron da ya saba gudanarwa, kwamishinan yada labarai Alh. Sambo Bello Danchadi ya ce majalisar ta...
Amincewar Gwamnatin Tarayya da kashe Naira biliyan 712 biliyan don gyaran Filin Jirgin Sama na Murtala Muhammed da ke Legas ya haifar da ce-ce-ku-ce a faɗin Najeriya. Wannan gagarumin kashe kuɗi, da Majalisar Zartarwa ta Kasa ta amince da shi a ranar Alhamis da ta gabata, ya sanya masana harkar jiragen sama, ’yan adawa, da...
Ma’aikatan agajin gaggawa a lardin Hebei na arewacin kasar Sin da ambaliya ta aukawa, sun karfafa kokarin gyara tituna da gadojin da suka lalace, domin tabbatar da isar da kayayyakin agaji da na aikin ceto ba tare da tangarda ba. Ruwan sama dake ci gaba da sauka a kwanakin baya-bayan nan ya haifar da ambaliya...
Asusun kula da Ƙananan Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF, ya ce Najeriya ce ƙasa ta biyu da aka fi samun ɓullar cutar kwalara a yammacin Afirka da tsakiyar Afirka. Darektan Hukumar UNICEF mai kula da yammacin Afirka da Afirka ta tsakiya, Gilles Fagninou ne ya bayyana hakan tare da cewar annobar kwalara ta zama...
Wani rahoto daga ƙungiyar likitocin ƙasa da ƙasa wato Medecins Sans Frontiere na nuni da cewa sama da yara 650 ne suka mutu bayan fuskantar ƙarancin abinci mai gina jiki a Jihar Katsina. Medicins Sans Frontiere wadda ta fara aiki a Katsina tun shekarar 2021, ta ce ta samu ƙaruwar yara masu fama da yunwa...
Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau Jibril, ya kaddamar da zaman jin ra’ayoyin jama’a na yankin Arewa maso Yamma kan sauya kundin tsarin mulkin Najeriya a Kano. Yayin gabatar da jawabinsa na bude taron, Sanata Barau ya yi maraba da manyan baki da suka halarci zaman, yana mai cewa: “Ina alfahari da zuwanku wannan zama...
Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya ce sake gyaran kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999 dole ne, ya taimaka wajen haɗa kan ƙasa, kyautata mulki, da bunƙasa tattalin arziƙi. Ya buƙaci a gudanar da wannan aiki cikin adalci, gaskiya da kuma bisa ra’ayoyin jama’a gaba ɗaya. HOTUNA: Shugaban Gambiya ya kai wa iyalan Buhari...
Aƙalla mutum 14; ciki har da mata da ƙananan yara ƙanana ne, suka rasu a wani sabon hari da aka kai a Jihar Filato. Harin ya faru ne da yammacin ranar Alhamis a Gundumar Mangor da ke Ƙaramar Hukumar Bokkos. Sarkin Katsinan Gusau ya rasu Yadda aka mayar da yaran da aka sace a Kano...
Rundunar ‘Yan Sandan jihar Bauchi ta ce ta kama wata budurwa ‘yar shekara 19 mai suna Esther Gambo bisa zargin sace yara da yin garkuwa da su sannan ta kashe su. Rundunar ta ce wadannan kananan yara biyu mata ne ‘yan shekara bakwai, lamarin da ya jawo tarzoma da kona coci. Kakakin Rundunar, CSP Mohammed...
Asusun Kula da Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya (UNICEF) ya nuna damuwa kan halin da yara ke ciki a jihar Kano, yana mai kira ga gwamnatin jihar da ta ƙara zuba jari a fannin lafiya, ilimi, da abinci mai gina jiki ta hanyar kasafin kuɗi da ya danganci makomar yara. Shugaban ofishin UNICEF na Kano,...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba A duk lokacin da aka ce an kammala zangon karatu, dalibai kan samu hutu don hutawa da yin wadansu abubuwa na daban da kuma ba su damar shakuwa da ’yan uwa da abokan arziki. Kamar yadda masana harkar harkar ilimi suka saba fadi, yawan karatu kan taho da...
Asusun kula da ƙananan yana na Majalisar Ɗinkin Duniya UNICEF, ya ce ya wani sabon bincike da ya gudanar ya banƙado yadda cin zarafin ƙananan yara da kuma kulle su ba bisa ƙa’ida ba ke ci gaba da bazuwa a Nijeriya. A cikin rahoton da ya fitar ranar Litinin, UNICEF ya ce har yanzu akwai...
Rundunar ’yan sandan Jihar Filato a ranar Alhamis ta gurfanar da wasu mutane 22 da ake zargi da kashe matafiya bikin aure da a unguwar Mangun da ke Ƙaramar hukumar Mangu ta Jihar Filato. An kashe mutum 13 daga cikin matafiyan, yayin da wasu da dama suka jikkata sakamakon harin da wasu da ake zargin...
Kananan yara uku sun rasu yayin da wasu da shidan ke kwance a asibiti sakamakon sake bullar cutar nan ta mashako a garin Zariya da ke Jihar Kaduna. Wani mazaunin unguwar Kwarbai a yankin na Zariya, Mallam Bashir Magaji wanda ya rasa ’yarsa sakamakon barkewar cutar wadda a turance ake kira Diphtheria, ya bayyana yadda...
Sanatan ya bayyana cewa gwamnonin yankin na farko sun ba da gagarumar gudunmuwa wajen jagorantar hadin kai wajen cimma muradun yankin daga kan ikon sarrafa albarkatun kasa zuwa matsalolin muhalli da sauransu. A kan wannan ya yi kira ga gwamnoni.masu ci a yanzu da su ci gaba da wannan al’adar, kuma su kara kokari kan...

Taron Ashura Ya Zama Lamari Mafi Girma Da Cinkoson Jama’a, Inda Masu Ziyara Daga Sassan Duniya Suka Isa Karbala
Gangamin Ashura ya zama lamarin mafi girma da cunkoson jama’a inda tattakiin Tuwairij yake gudana tare da faɗaɗa da ba a taɓa ganin irinsa ba Tattakin Tuwairij na bana zuwa birnin Karbala na fuskantar hallara da cunkoson jama’a da ba a taba ganin irinsa ba, inda dimbin masu ziyara daga sassan duniya ke tururuwa zuwa...
Hukumomi a Jihar Texas ta Amurka sun ce gomman mutane sun riga mu gidan gaskiya ciki har da kananan yara sakamakon wata mummunar ambaliyar ruwa a ranar Asabar. Sai dai ya zuwa yau Lahadi, adadin wadanda suka mutu sun kai 50 ciki har da kananan yara 15 yayin da ake ci gaba da aikin ceto...
Hukumar Bayar da agajin gaggawa ta Jihar Gombe (SEMA) ta bayyana cewa, ambaliya da iska mai ƙarfi sun rushe da lalata gidaje 171 a yankunan jihar cikin watanni biyu da suka gabata, lamarin da ya haddasa asara da kuma mutuwar yara huɗu. Sakataren zartarwa na Hukumar SEMA, Malam Abdullahi Haruna Abdullahi ne ya bayyana hakan...
Bisa ga sanarwar, wannan wani sashe ne na sabon yunkuri na ba da cikakken ‘yanci ga majalisar kananan hukumomi 774 na kasar nan. Haka kuma a kan gyaran kananan hukumomi, wata kudirin doka da ke neman kirkiro wata hukumar zabe mai zaman kanta ta kananan hukumomi (NALGEC), wanda za ta dunga shiryawa, gudanar da kuma...
Wata Babbar Kotu a Jihar Kano, ta yanke wa wasu mutum shida hukuncin zaman gidan yari na tsawon shekaru 120, bisa samun su da laifin satar yara da kuma sayar da su. Mutanen da aka yanke wa hukuncin sun haɗa da Mercy Paul, Ebere Ogbono, Emmanuel Igwe, Loise Duru, Monica Oracha, da Chinelo Ifedigwe. PDP...
Akwai yiwuwar ƙasar Koriya ta Arewa mai ƙarfin makaman nukiliya za ta taimaka wajen gyara tashoshin nukiliyan Iran da hare-haren Amurka suka lalata da kuma gina sababbin masana’antun ƙera makamai masu linzami masu gudun walƙilya a Iran. Wani masani mai suna Ankit Panda daga cibiyar zaman lafiya ta kasa da kasa ta da ke Amurka,...
Don girmama ziyarar shugaban ƙasa, gwamnatin jihar ta ayyana ranar Laraba a matsayin hutu domin bai wa mazauna yankunan damar halarta taron da kuma bin diddigin abubuwan da suka shafi ziyarar. Wannan ita ce ziyarar farko da Tinubu ya kai Jihar Benuwe tun bayan da rikicin ya ƙara tsananta. Jama’a da dama na kallon wannan...
A ranar dimokuraɗiyyar Najeriya ta 2025, Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, a ranar Alhamis, ya yi afuwa ga fursunoni 66 a babbar Cibiyar gyaran hali da ke Maiduguri. Ziyarar da Gwamna Zulum ya kai a gidan yari a ranar 12 ga watan Yuni, 2025, ya yi amfani da ikon da sashe na 212 na...
A ranar dimokuraɗiyyar Najeriya ta 2025, Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, a ranar Alhamis, ya yi afuwa ga fursunoni 66 a babbar Cibiyar gyaran hali da ke Maiduguri. Ziyarar da Gwamna Zulum ya kai a gidan yari a ranar 12 ga watan Yuni, 2025, ya yi amfani da ikon da sashe na 212 na...
Jimillar fursunoni: 80,879 Adadin cibiyoyin gyaran hali: 256 Kashi na rijista da aka kammala: 74% Umar ya jaddada cewa sauran fursunonin da ba a yi wa rijistar ba za a cigaba da yi musu, kuma an kafa duk wasu hanyoyi da za su tabbatar da nasarar kammala aikin cikin sauki. Hukumar ta bayyana wannan aikin...
Jakadan kasar Iran a Mosco ya bayyana cewa shugaban kasar Rasha Vladimir Putin zai kawo ziyarar aiki Tehran nan ba da dadewa ba. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran. Labarin ya kara da cewa kasashen biyu sun kulla yarjeniyoyi masu yawa a tsakanin daga ciki har da masu dogon zango. Kazem Jalali ya bayyana...
An gano gawar yara bakwai a yankin Mokwa, da ke Jihar Neja, bayan ambaliyar ruwa da ta afka wa garin mako guda da ya wuce. Yawan adadin waɗanda suka rasu kawo yanzu ya kai mutum 160, amma wasu jami’ai sun ce za a iya gano gawar sama da mutum 200. Kotu ta aike da ɗan...
Kasashen Larabawa karkashin jagorancin Saudiyya sun bayyana rashin jin dadinsu ga Isra’ila, kan hana su ziyartar yankunan Falasdinawa Ministocin harkokin wajen kasashen Larabawa sun bayyana rashin jin dadinsu ga gwamnatin Isra’ila, game da rashin amincewa da tawagar kungiyar kasashen ta ziyarci yankin da aka mamaye a Gabar Yamma da kogin Jordan don tattaunawa da shugaban...
Babbar jami’a a hukumar kiwon lafiya ta kasar Sin Shen Haiping, ta ce a shekarun baya bayan nan koshin lafiyar yaran kasar Sin na kara inganta. Jami’ar wadda ta bayyana hakan ga wani taron manema labarai a yau, ta ce a shekarar 2024, alkaluman mace-macen jarirai a kasar ya ragu zuwa jariri hudu cikin duk...
Majalisar Dokokin Jihar Kaduna ta amince da dokoki guda biyu masu muhimmanci, wadanda suka hada da kafa sabuwar cibiyar karatu ta gaba da sakandare, da kuma yana gyara dokar kotunan gargajiya na jihar. Dokar farko ta tanadi kafa Kwalejin Fasahar Noma, da ke Samaru Kataf, bisa dokar kafa Kwalejin Fasahar Noma ta shekarar 2024. ...
Kafin tashinsa zuwa kasar Oman shugaban kasar Iran ya bayyana cewa: Suna neman kyakkyawar dangantaka da maƙwabtansu Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya tabbatar kafin ya tashi daga filin tashi da saukar jiragen sama na birnin Tehran zuwa birnin Muscat a yammacin yau Talata cewa: Makasudin ziyarar tasa zuwa kasar Oman ita ce kulla kyakkyawar...
Ga shi abin ci ya yi tsadar da samun a ci sau uku yana da wajala, balle kuma a nemi mai gina jiki. Kwananan masu sayar da ƙwai suka koka saboda rashin ciki, masu kifi dai haka abin yake balle kuma masu nama. Duk da hakan bai hana yara murmushi ba wataƙila saboda ba su...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Najeriya tana cikin ƙasashen da suka fi yawan yara a duniya, a cewar Hukumar Kula da Kananan Yara ta Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF). Sai dai a cewar Hukumar ta UNICEF, kusan rabin wadannan yara suna fuskantar kalubale, kama daga cin zarafi zuwa rashin samun kulawa da dai sauran...
Firaministan Pakistan Muhammad Shehbaz Sharif ya na ziyara a birnin Tehran domin inda yake ganawa da manyan jami’an kasar kan muhimman batutuwan da suka shafi kasashen biyu, shiyya-shiyya da kuma duniya baki daya. A yau litinin ne Sharif ya jagoranci tawaga a Tehran bisa gayyatar da shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya yi masa. Da...
Bincike ya yi nuni da cewa an bar dukkan al’ummomi ba tare da ingantattun makarantu ba a jihohi kamar Borno, Yobe, da Adamawa. Sama da makarantu 1,500 ne aka lalata tun farkon rikicin Boko Haram, inda sama da malamai 19,000 suka rasa matsugunansu, kuma da yawa ma suna fargabar komawa. ‘Yan mata suna cikin hadari,...
Kawamcen jam’iyyun siyasa na kasar Ivory Coast ya bukaci a sake lalen yadda aka tsara yadda ake ristar jam’iyyu a hukumar zaben kasar, ganin yadda ta hana rijistar wasu jam’iyyun saboda dalilai daban daban. Shafin yanar gizo na labarai Afirka news ya bayyana cewa an kafa kawancen ne wanda aka sanyawa suna CAP-CI a farkon...
Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadin cewa: Gaza na gaf da afkawa cikin babbar masifa saboda zaluncin ‘yan mamayar Isra’ila A yayin da gwamnatin mamayar Isra’ila ke ci gaba da killace Zirin Gaza sama da watanni biyu, abubuwan da ke faruwa a kowace rana, abubuwa ne da suke yadda bala’i ke shafar kowane gida, kowane...
Hukumar lafiya ta Duniya WHO, ta nuna matukar kaduwa game da halin da ake ciki a Gaza. Abin da ke faruwa a Gaza “ba abinda za’a lamunta da shi ne ba,” in ji Mike Ryan, mataimakin darekta-janar na Hukumar Lafiya ta Duniya, yayin wani taron manema labarai. Mista Ryan, ya nuna fushinsa matuka game da...
“Muna kira ga sauran kungiyoyi, ‘yan siyasa, masu hannu da shuni tare da gwamnatoci, cewa kofarmu a bude take wajen neman taimakon kayan abinci, tufafi da makamantan su.” In ji Goni Alhaji Goni ya kara da cewa, gungiyar su ta direbobi, ta na da mambobin sama da 30,000 a fadin jihar Yobe. Ya ce,...