An kammala gasar fada tsakanin mutum-mutumin inji cikin jerin gasannin mutum-mutumin inji ta kasa da kasa a ran 25 ga watan nan da muke ciki a birnin Hangzhou dake gabashin kasar Sin. Gasar ta fada tsakanin mutum-mutumin inji da aka yi a wannan karo, ita ce irinta ta farko a duniya, inda kuma ta zama wani dandali dake yi wa masu kallo a daukacin duniya karin haske game da kimiya da fasaha a wannan bangare.

An watsa gasar ga masu kallo na cikin gidan kasar Sin da ketare kai tsaye, matakin da ya ba su damar sanin gajiyar da ake ci daga kimiya da fasaha.

 

CMG ta gabatarwa al’ummun duniya wata dama mai kyau ta fahimtar kimiyyar mutum-mutumin inji duba da taron mu’ammalar masu kallo da mutum-mutumin inji da ta gudana a ran 1 ga watan nan a cikin gasar kwarewar sana’o’i ta mutum-mutumin inji, zuwa gasa irin ta fada ta wannan karo, har ma da gasar da za ta gudana nan gaba a wannan bangare. Matakin da zai gaggauta bunkasuwar sha’anin zuwa wani sabon mataki na bautawa daukacin al’ummar Bil Adam da amfani da ingantacciyar fasahar zamani. (Amina Xu)

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Majalisar Kasa Na Duba yiwuwar Dawo Da Gwamnan Jihar Rivers Fabura Kafin Cikar Wa’adin Watanni Shida.

Shugaban marasa rinjaye na Majalisar Wakilai Ali Isah, ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai na Majalisar bayan wata ganawa da mai kula da jihar Ribas Sole a Abuja.

 

Ali Isah, ya bayyana cewa mai kula da jihar ta Ribas ya kasance a gidan a wani bangare na ziyarar da ya saba yi domin yiwa kwamitin riko da ke sa ido kan al’amuran gwamnati.

 

Shugaban marasa rinjaye wanda ya jagoranci taron a madadin shugaban kwamitin wanda ya zama shugaban masu rinjaye na majalisar Farfesa Julius Ihonvere, ya bayyana gamsuwa da kokarin da mai gudanarwa shi kadai yake yi na wanzar da zaman lafiya a jihar.

 

Ya ce mai kula da jihar ya tuntubi manyan masu ruwa da tsaki kan rikicin shugabancin jihar Ribas, shugabannin cibiyoyin addini da na gargajiya, jami’an tsaro da sauran masu ruwa da tsaki don ganin an warware matsalar cikin ruwan sanyi domin ci gaban jihar.

 

Sai dai jami’in da ya gabata, ya umurci mai kula da shi kadai da ya tabbatar da cewa rikicin shugabancin jihar Ribas bai shafi biyan albashin ma’aikatan gwamnati da wadanda suka yi ritaya duk wata da fansho ba kamar yadda shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu da majalisar dokokin kasar ke yin duk mai yiwuwa don tabbatar da mulkin dimokuradiyya a kasar nan.

 

Ali Isah, ya kuma tabbatar da cewa kwamitin wucin gadi zai ci gaba da tuntubar mai gudanarwa da bangaren zartarwa don hana tsawaita dakatarwar daga wa’adin watanni shida domin samun ci gaba.

 

COV: TSIBIRI

 

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Mutum 9 sun rasu a hatsarin kwale-kwale a Jigawa
  • Samar da makamashi mai tsafta na zamani shi ne fatanmu — Guterres
  • Majalisar Kasa Na Duba yiwuwar Dawo Da Gwamnan Jihar Rivers Fabura Kafin Cikar Wa’adin Watanni Shida.
  • Hare-hare: ’Yan bindiga sun raba mutum 5,000 da muhallansu a Katsina
  • Salisu Yusuf Ya Ajiye Aikinsa Na Kocin Nasarawa United
  • Wasan Kwallon Mutum-Mutumi Ya Nuna Yadda Sin Ta Shirya Wa Karbar Bakuncin Wasanninsu Na Duniya
  • Morocco Ta Shigar Da Ƙara Kan Nasarar Super Falcons A Gasar WAFCON
  • ’Yan bindiga sun kashe mutum 5 a sabon hari a Alkaleri
  • Mutum miliyan 1.2 na fama da ciwon hanta a Kano
  • Gwamna Yusuf Ya Kafa Kwamitin Bincike Kan Mutumin Da Ake Tuhuma Da Safarar Miyagun Kwayoyi