Mutanen da suka rasu a ambaliyar ruwa a Neja sun ƙaru zuwa 151
Published: 31st, May 2025 GMT
Adadin mutanen da suka mutu a mummunar ibtila’in ambaliya a Jihar Neja ya karu zuwa mutum 151.
Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Neja (NSEMA) ce ta sanar cewa mutane 11 sun jikkata, yayin da mutane 3,018 suka rasa matsuguninsu a ibtila’in na ƙaramar hukumar Mokwa a safiyar Asabar.
Kakakin hukumar, Ibrahim Hussaini, ya bayyana cewa ambaliyar ta shafi gidaje 265 da kuma magidanta 503.
Ya ƙara da cewa yankuna uku, da suka hada da Tiffin Maza da Anguwan Hausawa, sun nutse sakamakon ruwan sama mai ƙarfi da aka yi na tsawon sa’o’i da dare a ranar Laraba.
Maƙabarta mai shekaru 500 da ta koma maɓoyar ’yan daba Sojoji sun kashe ɗan ta’adda da aka sa ladar N100m a kansa a BornoWannan lamari ya faru ne watanni biyar bayan Gwamnan Jihar Neja, Umar Bago, ya sanar da cewa jihar ta samu tallafin dala miliyan 10 daga Bankin Duniya don dakile zaizayar ƙasa a wasu sassan Mokwa.
Gwamnan ya ce an tantance kwararrun ’yan kwangila don gudanar da aikin.
A ranar Juma’a, Shugaban Ƙasa Bola Tinubu a yayin miƙa ta’aziyyarsa, ya umarci Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Ƙasa (NEMA) da hukumomin tsaro su ƙara ƙaimi wajen aikin ceto da agaji a wuraren da abin ya shafa.
উৎস: Aminiya
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamnatin Jigawa Za Ta Gina Gidaje 52 A Babban Birnin Jihar
Daga Usman Muhammad Zaria
Majalisar Zartarwa ta Jihar Jigawa ta amince da bayar da rancen kudi ga hukumar gidaje ta jihar domin gina gidaje 52 a Dutse.
A cikin wata sanarwa da kwamishinan yada labarai na jihar, Alhaji Sagir Musa Ahmed ya fitar, ya bayyana cewa gidajen za su kunshi masu dakuna uku da kuma dakuna biyu kowanne.
Ya ce aikin zai kasance a gaban tsohuwar unguwar majalisar dokoki, kusa da hanyar wucewa ta Jami’ar Tarayya da je Dutse, a matsayin wani shiri na asusun gina gidaje karkashin ma’aikatar gidaje, ci gaban birane da tsare-tsaren yankuna, ta hannun hukumar gidaje ta jihar.
Alhaji Sagir ya bayyana cewa, wannan mataki na nuna kudirin gwamnati wajen magance matsalar gidaje a babban birnin jihar, kara habaka ci gaban birane, tare da samar da ayyukan yi ga matasan jihar.
Ya ce an tsara wannan asusu ne domin tabbatar da dorewa, ta yadda za a ci gaba da zuba jari a ayyukan samar da gidaje masu araha a fadin jihar.
Haka kuma ya kara da cewa, gwamnatin jihar tana da kudirin ci gaba da inganta rayuwar al’ummarta, ta hanyar ayyuka masu amfani da jama’a, da ke inganta walwala, karfafa tattalin arziki, da tallafa wa matasa.
Kwamishinan ya kuma bayyana cewa, majalisar ta amince da bayar da kwangilar gyara da inganta gidan baki guda biyu (Malam Adamu Chiroma House da kuma Senator Francis Ella House) da ke cikin G9 Quarters a Dutse, da kudin sama da naira miliyan 219.7.
Ya ce aikin zai haɗa da cikakken gyara da inganta gine-ginen, gyaran hanyoyin ruwa da kuma girka tankokin ruwa ga kowanne daga cikin gidajen biyu.
Ya ce hakan na da nufin tabbatar da wadataccen ruwan sha mai dorewa a wuraren.
Alhaji Sagir Musa Ahmed ya kara da cewa, amincewar da aka yi da wannan kwangila na nuna jajircewar gwamnatin jihar wajen kula da dukiyar jama’a da kuma tabbatar da cewa gine-ginen gwamnati suna cikin yanayi mai kyau da nagarta.