‘Yan Tawayen Sudan Sun Kashe Fararen Hula 10 A Hare-Haren Da Suka Kai Kan Birnin Kordofan
Published: 29th, May 2025 GMT
Fararen hula 10 ne suka rasa rayukansu sakamakon harin da jiragen yaki mara matuki suka kai kan birnin Kordofan na kasar Sudan
Kafofin yada labarai na cikin gidan kasar Sudan sun rawaito cewa: Akalla fararen hula 10 ne suka rasa rayukansu, wasu kuma suka jikkata sakamakon hare-haren da dakarun kai daukin gaggawa na Rapid Support Forces suka kai kan jihohin Yamma da Kudancin Kordofan.
Shafin yanar gizo na Sudan Tribune ya watsa rahoto cewa: Dakarun kai daukin gaggawa na Rapid Support Forces sun zafafa kai hare-hare ta sama a garuruwa da biranen yankin Kordofan tun farkon wannan wata.
Yankin dai ya sha fama da tashe tashen hankula tsakanin bangarorin da ke gaba da juna, inda kungiyar Rapid Support Forces ke da nufin dakile yunkurin sojojin Sudan da ke samun ci gaba a garuruwa da dama na Arewa, Yamma, da Kudancin Kordofan.
Shafin yanar gizo ya nakalto majiyar kasar na cewa: Akalla mutane 8 ne suka rasa rayukansu kana wasu 12 suka jikkata bayan da wani jirgin sama mara matuki na kungiyar Rapid Support Forces ya kai hari a kasuwar garin Al-Khawi da ke yammacin jihar Kordofan. Hakazalika an kai wani hari makamancin haka a wata unguwa da ke birnin Al-Dabaibat a jihar Kordofan ta Kudu, inda ya kashe fararen hula biyu tare da jikkata wasu biyar na daban. Haka nan jiragen yakin sun kai hari a wani sansanin soji a wannan birni, inda suka kashe sojoji tare da lalata motocin yaki.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: Rapid Support Forces
এছাড়াও পড়ুন:
‘Yansanda Sun Kama ‘Yan Ƙungiyar Asiri Da Ɓarayin Kifi A Jihar Neja
Ya ce ya sayi layin wayar ne daga hannun wani Audu, ɗan kungiyar Vikings wanda ya tsere yanzu.
A wani lamari kuma, ‘yansanda sun kama wasu mutum huɗu da suka shiga gonar wani mutum a Lapai Gwari, inda suka saci kifi da darajar kuɗinsu ta kai Naira 750,000.
Babban wanda ake zargi, Hussaini Garba, ya amsa laifi tare da bayyana Ahmed Yusuf, Ibrahim Musa da Abdulazeez Bawa a matsayin mutanen da suke sayen kifin idan ya sato.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp