Aminiya:
2025-09-18@00:55:06 GMT

Sojoji sun cafke ɗan ta’adda sun ƙwato makamai a Filato

Published: 31st, May 2025 GMT

Sojoji sun yi nasarar cafke wani mutum da ake zargi dan ta’adda ne tare da gano ma’adanar makamai a yayin wani samame da suka yi a Ƙaramar Hukumar Bassa ta Jihar Filato.

Binciken farko ya nuna cewa wanda aka kama ɗin yana da alaƙa da wata ƙungiyar masu aikata laifuka da ke da alhakin kisan wani makiyayi da satar shanu 1,250 a ƙauyen Tomborong, Ƙaramar Hukumar Riyom, a ranar 27 ga watan nan na Mayu.

A safiyar ranar Juma’a, sojoji suka kama wanda ake zargin, bayan samun rahoto game da inda ake zargin ɗan bangar yake ɓoye a ƙauyen Hura.

Yayin wani bincike da aka yi a maboyar wanda ake zargin, jami’an tsaro sun gano bindigar AK-47 guda daya, tare da harsasai 26 na 5.56mm da kuɗi da wasu abubuwan da ake zargin asiri ne.

Wata majiyar soji ta bayyana cewa wanda ake zargin yana tsare a hannun jami’an tsaro kuma yana “bayar da haɗin kai ga masu bincike kan sunaye da wuraren da sauran mambobin ƙungiyar da ma’adanar makamansu suke.”

Sojoji sun tsananta ƙoƙarin gano tare da kama sauran membobin ƙungiyar da ake zargi da alhakin ayyukan laifuka a yankin.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Ɗan Ta adda da ake zargin

এছাড়াও পড়ুন:

Ƴan Bindiga Sun Kashe Sarkin Shuwaka Na Kanam A Filato

KADA ta yi gargaɗi cewa haƙurin jama’a ya ƙare, tana mai jaddada cewa shiru da halin ko-in-kula daga shugabanni ba za a ƙara yarda da shi ba. Sun yi kira da a tabbatar da adalci da kuma mayar da zaman lafiya a yankin, tare da nuna goyon baya ga iyalan mamacin da ɗaukacin al’ummar Garga.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • An kama ɗaya daga cikin manyan kwamandojin IPOB
  • ‘Yansanda Sun Kama Mutane 6 Kan Zargin Haƙar Ma’adinai Ba Bisa Ƙa’ida Ba A Neja
  • Saudiyya ta saki ’yan Najeriya 3 da ta kama kan zargin safarar miyagun ƙwayoyi
  • ‘Yansanda Sun Kama ‘Yan Ƙungiyar Asiri Da Ɓarayin Kifi A Jihar Neja
  • Saudiyya Ta Saki ‘Yan Nijeriya 3 Da Ta Kama Bisa Kuskuren Safarar Ƙwayoyi
  • Tun Tinubu yana Gwamna ba abin da ya fi shahara da shi kamar tara haraji – Adebayo
  • Sojoji Sun Harbe Wasu ‘Yan Ta’adda 2 A Taraba
  • Sin Ta Gano Wani Dutse Mai Sassaka Na Daular Qin A Kan Tsaunin Qinghai-Tibet
  • An kama tsohon minista kan zargin kisan kai domin tsafi a Nijar
  • Ƴan Bindiga Sun Kashe Sarkin Shuwaka Na Kanam A Filato