2025-09-17@23:24:36 GMT
إجمالي نتائج البحث: 9010
«Hukumar JAMB»:
A ƙoƙarinta na ƙara wayar da kan jama’a game da harkokin lafiya a birane da karkara na Malam Madori, majalisar ƙaramar hukumar ta horar da mata da ‘yan mata 50 kan tsafta a lokutan al’ada domin kare kansu daga cututtukan mahaifa. Jami’in shirin, Malam Ali Haruna, ya ce an zaɓi mahalarta horon ne daga kowace gunduma ta yankin A cewarsa, manufar horon ita ce koyar da mahalarta yadda za su samar da kariya yayin al’ada da kansu domin rage kashe kuɗi da kuma kare kansu daga kamuwa da cututtukan mahaifa. Shi ma shugaban sashen ruwa da tsafta, Malam Shehu Sani Gwadayi, ya bayyana cewa tsafta na da matuƙar muhimmanci ga rayuwar ɗan adam domin inganta rayuwa da ƙarfafa...
A wani yunkuri na inganta kula da mata masu juna biyu da sauran ayyukan kiwon lafiya a jihar Jigawa, Asusun Kula da Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF tare da hadin gwiwar Karamar Hukumar Kirikasamma sun mika kayayyakin aiki da wasu muhimman kayayyaki ga cibiyar kiwon lafiya ta farko a Kirikasamma. Mai kula da cibiyar kiwon lafiya ta farko, Kabiru Musa, ya bayyana cewa kayayyakin sun haɗa da gadajen haihuwa, zannuwan gado, kayan aikin jinya, matashin kai da sauransu, kuma za a rarraba su zuwa wuraren kiwon lafiya a fadin karamar hukumar. A cewarsa, kayan da UNICEF da karamar hukumar suka samar za su inganta yadda ake gudanar da ayyukan kiwon lafiya a yankin. Yayin mika kayayyakin ga mai...
Daga ranar 14 zuwa 15 ga wata, an gudanar da sabon zagayen shawarwari kan harkokin tattalin arziki da cinikayya a tsakanin Sin da Amurka a birnin Madrid, babban birnin kasar Spaniya, inda bangarorin biyu suka yi musayar ra’ayoyi a kan harkokin cinikayya da ke janyo hankalinsu, tare da cimma daidaito ta fannin daidaita batutuwan da suka shafi Tiktok, da rage shingayen zuba jari, da sa kaimin hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayya a tsakaninsu. Taron shawarwarin ya kasance zagaye na hudu da sassan biyu suka gudanar cikin watanni biyar da suka wuce. Kwatankwacin shawarwarin da aka gudanar a baya, a karo na farko, an sanya Tiktok cikin batutuwan da aka tattauna a shawarwarin na wannan zagaye. Yadda Sin da Amurka...
Fitattun dalibai akalla 12 ne daga makarantun gwamnati suka samu guraben tallafin karatun sakandare a ƙarƙashin Asusun Tallafin Karatu na Jihar Kwara (Kwara-ETF). A wajen taron gabatarwa ga waɗanda suka fara cin moriyar shirin, Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq ya bayyana cewa ci gaban harkar ilimi a Najeriya abu ne mai tsada kuma ya zama wajibi kowa ya bayar da gudummawarsa. Ya roƙi masu masu hannu da shuni da kungiyoyi masu zaman kansu da su tallafa wajen gina makarantu ko kuma su ɗauki nauyin daliban da suka nuna bajinta da jajircewa a harkar karatu. A cewarsa, an zabo daliban 12 ne sakamakon bajintar da suka nuna a matakai daban-daban na tantancewa da Kwara ETF ta gudanar. Gwamnan ya bayyana cewa tallafin ya...

Yawan Kadarorin Kamfanoni Mallakar Gwamnatin Sin Ya Wuce Yuan Triliyan 90 a Lokacin Shirin Raya Kasa Na 14 Na Shekaru 5
Ofishin yada labarai na majalisar gudanarwa ta kasar Sin ya shirya taron manema labarai a yau 17 ga wata, inda aka bayyana cewa, tun daga fara aiwatar da shiri na 14 na shekaru 5 na raya kasa, wato daga shekarar 2021 zuwa ta 2025, karfin kamfanoni mallakar gwamnati ya kara karuwa, kuma jimillar kadarorinsu ta wuce yuan tiriliyan 90, kwatankwacin sama da dalar Amurka tiriliyan 12.6. Darektan kwamitin sa ido kan kadarori mallakar gwamnati na majalisar gudanarwa ta kasar Sin, Zhang Yuzhuo ya bayyana cewa, tun daga shekarar 2021 har zuwa yanzu, jimillar kadarorin kamfanoni mallakar gwamnati ta karu daga kasa da yuan tiriliyan 70, kwatankwacin dalar Amurka kimanin tiriliyan 10, zuwa sama da yuan tiriliyan 90, kwatankwacin sama da...
Gwamnan Sakkwato, Dakta Ahmad Aliyu, ya ƙaddamar da jiragen ruwa na zamani guda 20, tare da riguna ruwa (life jackets) 2,000, domin rage haɗurran da ke aukuwa sakamakon ambaliya da nutsewar jirage a sassan jihar. An ƙaddamar da jiragen ne a ƙaramar hukumar Wamakko a ranar Laraba, inda gwamnan ya bayyana cewa wannan mataki na daga cikin shirin gaggawa na tallafa wa al’ummar da ke fama da illar ambaliya da haɗurra a ruwa. Microsoft ya ƙwace shafukan wasu kamfanoni 340 a Najeriya An kama ɗaya daga cikin manyan kwamandojin IPOB “Mun dauki wannan mataki bayan rahotannin da muke samu na yawaitar hatsarurruka da rasa rayuka da dukiya sakamakon jiragen katako da mutane ke amfani da su,” in ji Gwamna Ahmad...
Wata sanarwa da Daraktan Yada Labarai da Hulda da Jama’a na Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya, Folasade Boriowo, ya fitar, ta ce a karon farko cikin shekaru da dama, daliban Nijeriya za su ci gaba da karatun tarihin Nijeriya tun daga Firamare 1 zuwa karamar Sakandare 3 yayin da daliban SSS 1 – 3 za su koyi sabon darasin da aka samar na ‘Civic and Heritage Studies’, wanda ya hada tarihin Nijeriya da Ilimin zamantakewar Jama’a. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp

Yakin Haraji Da Cinikayya Ba Zai Gurgunta Fifikon Da Sin Ke Da Shi A Fannin Raya Masana’antun Sarrafa Hajoji Da Kasar Ta Gina A Tsawon Lokaci Ba
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Lin Jian, ya ce alkaluman baya bayan nan da aka fitar cikin Mujallar Economist, sun shaida yadda hada-hadar cinikayyar fitar da hajoji ta kasar Sin ke kara bunkasa cikin sauri a shekarar nan ta bana, inda fannin ke samun karuwar abokan hulda, da daidaiton matsayi cikin tsarin samar da hajojin masana’antu na kasa da kasa. Kakakin ya kara da cewa, kasashen duniya suna maraba da hajojin kasar Sin, kuma yakin ciniki da haraji ba su yi wani babban tasiri kan kasar Sin ba. A fannin hada-hadar cinikayya, sanya shinge ba alama ce ta karfin gwiwa ba, kuma katangar da Amurka ke ginawa kanta, daga karshe za ta illata karfinta ne. Lin Jian, wanda ya...
Kwamatin kananan hukumomi na majalisar dokokin jihar Jigawa ya bukaci ma’aikatar kananan hukumomi da ta karfafa matakan yiwa kananan hukumomin jihar 27 jagoranci akan sha’anin mulki da harkokin kudi domin inganta ayyukan su. Shugaban Kwamatin, Alhaji Aminu Zakari ya yi wannan kiran a karshen ziyarar kwanaki 3 da kwamatin ya yi a ma’aikatar kananan hukumomi ta jihar a Dutse. Alhaji Aminu Zakari wanda shi ne wakilin mazabar Gwiwa a majalisar dokokin jihar Jigawa, ya ce ziyarar kwamatin na da nufin tantance yadda ma’aikatar ta ke gudanar da ayyukan ta, ta fuskar harkokin mulki da na kudi da kuma dangantakar aiki tsakanin ta da kananan hukumomin jihar 27 kamar yadda tsarin mulki ya dorawa majalisa nauyi. A nasa jawabin, mataimakin shugaban...
Gwamnatin Jigawa ta amince da sabon tsarin ka’idojin aiki domin aiwatar da shirin kula da lafiyar mata masu juna biyu, da jarirai da ƙananan yara kyauta a cibiyoyin lafiya na jihar. Kwamishinan Yaɗa Labarai, Alhaji Sagir Musa Ahmed, ya bayyana haka bayan zaman majalisar zartarwa da aka gudanar a gidan gwamnati Dutse. Ya ce ka’idojin za su taimaka wajen inganta nagartar hidima, fayyace karewar ma’aikata, da kuma tabbatar da gaskiya, da bin doka da tsari a asibitoci. Kwamishinan ya ƙara da cewa matakin ya dace da manufar gwamnatin jihar na rage mace-macen mata da yara da kuma tabbatar da samun ingantacciyar kulawa ga kowa. Ya ce za a fara aiwatar da tsarin nan take, tare da horas da shugabannin asibitoci...
Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya sanar da janye dokar ta-baci a Jihar Rivers daga ƙarfe 12 na daren 17 ga watan Satumban 2025. Shugaban Ƙasar, a wata sanarwa da ya sanya wa hannu, ya ce dokar ta-bacin da ta dakatar da Gwamna, Mataimakiyarsa, da ‘yan majalisar dokokin jihar na tsawon watanni shida ta cimma manufarta na dawo da zaman lafiya a jihar. Tinubu ya bayyana cewa ya yi amfani da Sashe na 305 na Kundin Tsarin Mulkin 1999 ne a watan Maris na 2025 sakamakon durƙushewar mulki a Jihar Rivers. A cewarsa, rashin jituwa tsakanin Gwamna Siminalayi Fubara da Majalisar Dokokin Jihar, da kuma lalata muhimman kadarorin gwamnati sun jefa jihar cikin rikici. “Lamarin ya kai ga Babbar Kotun...

Kuri’ar Jin Ra’ayin Jama’a Ta CGTN: Baje Kolin Sin Da ASEAN Ya Fadada Matsayar Bai Daya Ta Cudanyar Sassa Daban Daban
A yau Laraba ne aka bude bikin baje koli karo na 22, na Sin da kasashe membobin kungiyar ASEAN ko (CAEXPO), da kuma taron dandalin kasuwanci da juba jari na Sin da ASEAN ko CABIS, a birnin Nanning na jihar Guangxi ta kabilar Zhuang mai cin gashin kai dake kudancin kasar Sin. A shekarun baya bayan nan, Sin da kungiyar ASEAN, sun ci gaba da cimma manyan nasarori tare a fannin bunkasa dunkulewar tattalin arzikin shiyyarsu, da fadada damar bai daya ta cudanyar mabambantan sassa, a gabar da ake fuskantar yanayin tangal-tangal a duniya. Wata kuri’ar jin ra’ayin jama’a da kafar CGTN ta kasar Sin ta gudanar, ta shaida yadda kaso 92.8 bisa dari na masu bayyana ra’ayoyi suka amince...
Saboda wannan baiwa daga Allah, iyalai da ‘yan uwan mai akuyar suka sanar da shirye-shiryen gudanar da bikin murnar haihuwar ‘ya’yan akuyar a ranar Lahadi mai zuwa a Garun Dakasoye, karamar hukumar Garun Malam ta Jihar Kano, inda za a yi musu suna da kuma karatun Alkur’ani mai girma. A nasa bangaren, mahaifin budurwar, Malam Aliyu dake Garin Dakasoye, ya tabbatar da cewa za su gudanar da bikin domin nuna godiya ga Allah Madaukakin Sarki bisa wannan ni’ima da ya ba su. Ya kara da cewa: “Mun gode wa Allah bisa wannan arziki, kuma muna sa ran gudanar da bikin tare da sanya musu suna domin nuna godiya ga Allah mai daukaka.” Daga kanmu, magana ta ƙare....
Da safiyar yau 17 ga watan Satumba, aka bude dandalin tattauna batutuwan tsaro na Xiangshan karo na 12 da zai dauki kwanaki 3, daga raneku 17 zuwa 19 ga wannan nan, bisa jigon “daukaka tsarin duniya da inganta neman ci gaba cikin lumana”, a nan birnin Beijing. Tawagogi sama da 100 na gwamnatocin kasashe daban-daban da yankuna da wakilan kungiyoyin kasa da kasa ne ke halartar taron, inda yawan masu rajista ya wuce 1,800. Da safiyar yau, taron ya shirya tarukan tattaunawa guda 6 bisa jigon “ma’anar cimma nasarar yakin duniya na kin tafarkin murdiyya” da “madaidaitan hanyoyi da manyan kasashe za su bi na yin mu’ammala”, da “hanyoyin warware rikice-rikicen shiyya-shiyya”, da “cika shekaru 80 da kafuwar MDD: samun...
A yayin samamen, kakakin ‘yansandan Neja ya ce an kama mutane shida a wurin da ake hakar ma’adinan yayin da wasu kuma suka tsere. Abiodun ya bayyana sunayen wadanda ake cafken da Aliyu Rabiu, Samaila Ibrahim, Sadiku Auwal, Ibrahim Babangida, Musa Adamu da Sani Hassan. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp

Iran Ta Yi Nasarar Gwajin Tauraron Dan’adam ” Nahid 2″ Da Zai Samar Wa Yankunan Karkara Hanyar Sadarwa Ta “Internet”
Ministan sadarwa na Iran Sitar Hashimi ya bayyana cewa, an sami nasara a gwajin da aka yi na sabon tauraron dan’adam, mai suna “Nahid 2” wnada aikinsa shi ne samar da hanyoyin sanarwa na internet masu nagarta. Ministan sadarwar ya kuma ce dukkanin bangarorin tauraron dan’adam din sun yi aiki yadda ake so a yayin gwajin da hakan yake a matsayin wani ci gaba a fagen sadarwa a Iran. Har ila yau ministan Sadarwar Sitar Hashimi ya kuma ce; A tsakanin kauyuka 10,000 da ba su da hanyoyin sadarwa, yanzu an rage su da 2000, kuma ana ci gaba da aiki tukuru domin isa ga kauyunan da suke nesa,masu wahalar zuwa. Ministan sadarwar na Iran ya kuma kara da cewa;...
A ranar Lahadi mai zuwa ne za a kada kuri’ar raba gardama akan sabon kundin tsarin mulkin kasar Guinea,wanda zai bai wa shugaban soja mai ci Mamadi Domboya damar tsayawa takara. Kamfanin dillancin labarun Reuters ya nakalto cewa; A yau Laraba ne zai zama ranar karshe ta wayar da kai akan kada kuri’ar,wanda hakan zai zama wani mataki mai matukar muhimmanci a wannan kasa ya yammacin Afirka. Jim kadan bayan juyin mulkin da aka yi a wannan kasa a watan Disamba na 2021, an yi dokar da majalisar Mulki ta soja ta amince da ita, wacce ta kunshi cewa; Dukkanin ‘yan majalisar Mulki ta soja ba su da hakkin tsayawa takara a fadin kasa da kuma a matakin yankuna. Sai...
Babban sakataren majalisar koli ta tsaron jamhuriyar musulunci ta Iran Dr. Ali Larijani ya bayyana cewa; Za a bunkasa aiki tare a tsakanin Iran da Saudiyya a fagagen tattalin arziki da kuma tsaro. Dr. Larijani ya bayyana hakan ne jim kadan bayan fitowar daga ganawar da ya yi da Yarima mai jiran gado na Saudiyya Mu8hammad Bin Salman. Bugu da kari Dr. Ali Larijani ya ce a yayin ganawarwa da Yarima mai jiran gado na Saudiyya Muhammad Bin Salman, sun tattauna hanyoyin bunkasa alakar kasashensu ta fuskoki mabanbanta, da kara girman wannan alakar ta fuskar tattalin arzki da tsaro fiye da yadda take a yanzu.” Haka nan kuma ya ce, za a yi aiki domin kawar da dukkanin abubuwan da...
Har kullum, Sin za ta ci gaba da martaba ka’idojin kare hakkokin kamfanoninta. Duba da cewa manhajar TikTok ta shafe tsawon shekaru tana aiki a Amurka, ta kuma samar da dumbin ayyukan yi ga tarin Amurkawa, tare da bayar da gudummawa ga tattalin arzikin kasar, ya kamata gwamnatin kasar ta baiwa manhajar damar cin gajiya daidai da sauran makamantanta dake kasar. Kamar dai ko da yaushe, burin Sin shi ne wanzar da daidaito da cimma moriyar bai daya tare da Amurka. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe...
Ƙungiyar Malaman Makarantu ta Najeriya (NUT) reshen Jihar Gombe, ta ziyarci shugaban ƙungiyar shugabannin ƙananan hukumomi na jihar, Barista Sani Ahmad Haruna, a ofishinsa da ke Gombe. Shugaban ƙungiyar, wanda shi ne shugaban Ƙaramar Hukumar Gombe, ya bayyana cewa gwamnati da shugabannin ƙananan hukumomi za su ci gaba da yin duk mai yiwuwa wajen inganta walwalar malamai. Tinubu ya janye dokar ta-ɓaci da ya sanya a Ribas Saudiyya ta saki ’yan Najeriya 3 da ta kama kan zargin safarar miyagun ƙwayoyi Ya ce: “Ba za mu taɓa barin malamai su shiga cikin matsanancin hali ba. Za mu duba matsalolinsu domin tabbatar da walwalarsu da ci gaban ilimi a jihar.” Sani, ya kuma yaba da yadda NUT ke tattaunawa cikin lumana...
Hukumar tarayyar turai ta gabatar da shawara ga kasashe mambobi da su jingine aiki da yarjejeniyar da aka kulla ta kasuwanci da HKI saboda yakin Gaza. A yau Laraba ne dai hukumar tarayyar turai din ta bijiro da wannan shawarar ga kasashen mambobi,sai dai kuma babu cikakken goyon baya daga mafi yawancin kasashen kungiyar da zai sa a yi aiki da shi. Ita kuwa jami’ar harkokin wajen ta tarayyar turai din Kaya Kalas ta gabatar da shawarar a kakaba takunkumi akan wasu ministoci biyu na HKI da kuma ‘yan share wuri zauna da suke amfani da akrfi akan Falasdinawa. Da akwai kungiyoyin kare hakkin bil’adama guda 84 da suke yin kira a yanke duk wata alaka ta kasuwanci da zuba...
Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya janye dokar ta-ɓaci da ya ayyana ta tsawon watanni shida a Jihar Ribas. Tinubu, ya ayyana dokar tun a ranar 18 ga watan Maris, 2025, saboda rikicin siyasa da ya haifar da tsaiko a harkokin mulki tsakanin ɓangaren Zartarwa da Majalisar Dokokin jihar. NECO ta saki sakamakon jarabawar 2025 Saudiyya ta saki ’yan Najeriya 3 da ta kama kan zargin safarar miyagun ƙwayoyi A jawabin da ya gabatar a Fadar Shugaban Ƙasa a ranar Laraba, Tinubu ya ce matakin dokar ta-ɓacin ya cimma manufarsa, kuma ba za a tsawaita ba ƙarewar wa’adin da aka gindaya. “Ina farin ciki yau game da bayanan da ke hannuna, an samu yanayin fahimta a tsakanin dukkanin masu ruwa...
A yau, 17 ga watan Satumba, Shugaba Tinubu ya ɗage dokar ta-ɓaci da ya ƙaƙaba wa al’ummar jihar Ribas biyo bayan rashin jituwa da yaƙi ci yaƙi cinyewa da ya dabaibaye ɓangaren zartarwa da na dokokin jihar. Cikakken bayani na nan tafe… Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp

Guterres: Jerin Shawarwarin Da Sin Ta Gabatar Sun Cika Ka’idar Kundin Tsarin Majalisar Dinkin Duniya
Babban sakataren MDD António Guterres, ya bayyana a jiya Talata cewa, jerin shawarwarin da Sin ta gabatar wato shawarar raya duniya, shawarar tabbatar da tsaron duniya, shawarar raya wayewar kan al’ummun duniya, da kuma jagorantar harkokin duniya, sun dace da ka’idar kundin tsarin MDD. Guterres ya bayyana hakan ne yayin da yake amsa tambayoyin ‘yan jarida a wani taron manema labarai da aka yi a ranar. Ya ce shawarwarin da Sin ta gabatar sun mutunta manufar kasancewar bangarori da dama, kuma sun goyi bayan MDD a matsayin cibiyar hadin gwiwar kasa da kasa, tare da dukufa kan inganta hadin gwiwa tsakanin kasashe daban daban da warware rikice-rikice cikin lumana. Guterres ya kara da cewa, yanzu ana fuskantar rarrabuwar kawuna a...
Hukumar Shirya Jarabawa ta Ƙasa (NECO), ta fitar da sakamakon jarabawar kammala sakandare (SSCE) na shekarar 2025. Daga cikin ɗaliban da suka zana jarabawar guda 818,492, kashi 60.26 sun ci aƙalla darusa biyar da suka haɗa da Lissafi da Turanci. Saudiyya ta saki ’yan Najeriya 3 da ta kama kan zargin safarar miyagun ƙwayoyi Gwamnati ta fara duba yara marasa galihu kyauta a asibitin Aminu Kano Shugaban NECO, Farfesa Dantani Ibrahim Wushishi, ya ce ɗalibai 1,367,210 suka yi rajistar jarabawar; maza 685,514 da kuma mata 681,696. Amma daga cikinsu, ɗalibai 1,358,339 ne suka zana jarabawar. Ya ce ɗalibai 1,144,496, wanda ya kai adadin kashi 84.26, sun samu darusa biyar ba tare da cin Lissafi da Turanci ba. Sai dai an...
Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya yabawa Hukumar Makarantun Kimiyya da Fasaha ta Jiha bisa ƙirƙirar Kyautar Malami Mafi Nagarta, yana mai bayyana hakan da ɗaya daga cikin manyan manufofin da za su ƙarfafa koyo da koyarwa a fadin jihar. A cikin wata sanarwa da Babban Jami’in Yaɗa Labaran sa, Hamisu Mohammed Gumel, ya fitar, gwamnan ya bayyana cewa bikin na farko na bada lambar yabo da aka gudanar a Dutse ya dace domin girmama malamai da suka yi fice ta hanyar jajircewa da sadaukar da kai. Ya ƙara da cewa wannan mataki zai ƙara kwarin gwiwa, ya samar da gasa mai kyau, tare da inganta darussa a makarantu. Namadi ya jaddada cewa ingancin ilimi bai tsaya kan gina...
Gwamnatin Kano ta raba kayayyakin aiki na zamani na kimanin Naira Miliyan 250 ga cibiyoyin horas da sana’o’in hannu biyu da ke Kofar Mata da Gwale, domin yaƙi da shan miyagun kwayoyi da aikata laifuffuka a tsakanin matasa, ta hanyar samar da aikin yi. Kwamishinan Kimiyya da Fasaha, Dakta Yusuf Kofarmata, ya ce an amince da tallafin ne bisa umarnin Gwamna Abba Kabir Yusuf don bunƙasa tsare-tsaren ƙarfafa matasa a jihar. Ya bayyana cewa an samar da injinan sarrafa fata guda 26 domin cibiyoyin wadanda al’ummar yankunan suka kafa, amma ba su da isassun kayayyakin aiki. Ya ce Gwamna Yusuf ne ya gina Cibiyar Horaswar ta Gwale kasancewar nan ce mazabarsa, yayin da Dakta Yakubu Adam ya taka rawa...
Shugaban Ƙaramar Hukumar Birnin Kano, Alhaji Salim Hashim Idris Gwangwazo, ya kaddamar da shirin kula da ido kyauta domin tallafawa jama’a da ke fama da ‘Glaucoma’ da ke lalata rijiyoyin ido, da ‘Cataract’ wato yanar ido da sauran cututtukan ido. An gudanar da shirin ne a Asibitin Kwalli tare da haɗin gwiwar gwamnatin jihar, ƙarƙashin Gwamna Abba Kabir Yusuf, da Hukumar Lafiyar Farko ta Jiha, da ƙaramar hukumar da masu bada tallafi daga kasashen waje. Shirin ya haɗa da gwaje-gwajen lafiyar ido, da bayar da magunguna da kuma rarraba tabarau kyauta, musamman ga marasa ƙarfi a cikin al’umma. Shugaban ƙaramar hukumar, ta bakin Kwamishinan Lafiya Alhaji Mustapha Darma, ya bukaci jama’a da su ci gaba da tallafawa gwamnati wajen samar...
Hukumomin a Ƙasar Saudiyya, sun saki wasu ’yan Najeriya uku da aka kama a Jeddah kan zargin safarar miyagun ƙwayoyi. Waɗanda aka saki sun haɗa da Hajiya Maryam Hussain Abdullahi, Hajiya Abdullahi Bahijja Aminu, da Malam Abdulhamid Saddieq. Tinubu bai shirya gudanar da sahihin zaɓe ba a 2027 – Buba Galadima Gwamnati ta fara duba yara marasa galihu kyauta a asibitin Aminu Kano Sun shafe makonni huɗu a tsare kafin aka tabbatar da cewa ba su da laifi. A wajen taron manema labarai a Abuja, mai magana da yawun Hukumar Yaƙi da Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi (NDLEA), Femi Babafemi, ya ce sakin ya biyo bayan tttaunawa da Shugaban NDLEA, Janar Mohamed Buba Marwa (mai ritaya), tare da Hukumar Hana...
An garzaya da shi zuwa babban Asibitin Gwamnatin Tarayya da ke Birnin Kebbi, inda daga bisani likitoci suka tabbatar da rasuwarsa. An yi jana’izarsa a babban masallacin Sarkin Gwandu, sannan aka binne shi a makabartar Dukku da ke kan hanyar Makera zuwa Kangiwa. Jana’izar ta samu halartar jami’an kwas5tan, ‘yan uwa, abokai da sauran mu5sulmi daga sassa daban-daban na jihar. Har yanzu al’ummar garin Filgila da kewaye na cikin tashin hankali da fargaba, kasancewar hare-haren Lakurawa na jefa su cikin zulumi. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga...
Jigo a jam’iyyar NNPP, Buba Galadima, ya yi zargin cewa gwamnatin Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ba ta da niyyar gudanar da sahihi kuma ingantaccen zaɓe a 2027. Galadima ya bayyana hakan ne ranar Talata a wata hira da aka yi da shi a shirin Prime Time na gidan talabijin na Arise TV, inda ya ce gwamnatin da jam’iyyar APC ke jagoranta ta kankane cibiyoyin gwamnati don amfaninta. Gwamnati ta fara duba yara marasa galihu kyauta a asibitin Aminu Kano Tun Tinubu yana Gwamna ba abin da ya fi shahara da shi kamar tara haraji – Adebayo “Wannan gwamnati ba ta shirya gudanar da zaɓen adalci ba. Daga yadda suke tafiyar da al’amura, za ka gane yadda suke tarwatsa jam’iyyun siyasa....
Hukumar Kula da Inshorar Lafiya ta Kasa (NHIA) a ranar Laraba ta kaddamar da shirin bayar da kulawar lafiyar gaggawa kyauta ga yara a Asibitin Koyarwa na Aminu Kano (AKTH), Kano. Shirin, a cewar Darakta a hukumar, Dr. Salahudeen Sikiru, wani bangare ne na fadada shirin lafiyar iyaye da NHIA ke aiwatarwa zuwa ga yara masu rauni da masu bukata ta musamman. Tun Tinubu yana Gwamna ba abin da ya fi shahara da shi kamar tara haraji – Adebayo Ana zargin mace da kashe ’yar uwarta a kan N800 din barkono Ya ce an fara shirin fiye da shekara ɗaya da ta gabata da nufin rage mace-macen jarirai ’yan kasa da shekaru biyar. “Mun fara wannan shiri fiye da shekara...
Ma’aikatar shari’ar kasar Iran ta sanar da zartar da hukuncin kisa kan wani ba’iraniye dan leken hukumar Mossad ta Isra”ila A safiyar yau Laraba ne ma’aikatar shari’ar kasar Iran ta sanar da zartar da hukuncin kisa kan Babak Shahbazi, dan leken asirin Mossad da aka samu da laifin hada kai da yahudawan sahayoniyya a fannin leken asiri da kuma harkokin tsaro da kuma musayar bayanai da jami’an Mossad. An zartar da hukuncin kisar ta hanyar rataya a safiyar yau bayan kammala matakan shari’a kuma kotun kolin kasar ta amince da hukuncin. Babak Shahbazi, dan Rahmatullah, ya yi aiki a matsayin dan kwangilar kere-kere da sanya kayan masana’antu ga kamfanonin da ke da alaka da cibiyoyin tsaro, sojoji, da cibiyoyin sadarwa...
Kungyar Hamas ta bayyana cewa: Gmanatin mamayar Isra’ila ta ƙirƙiri ƙarya don kare kisan gillar da ta yi a Gaza Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas ta tabbatar da cewa: Zargin da kakakin rundunar sojin mamayar Isra’ila ya gabatar dangane da yin amfani da hasumiyai a birnin Gaza domin aikin soji ba komai ba ne illa karairayi na zahiri da suke nufin kare laifukan da ake aikatawa da kuma boye barnar da ake yi a birnin Gaza, kamar yadda a baya sojojin mamaya suka lalata garuruwan Rafah, Khan Younis, Jabaliya, Beit Hanoun, da Beit Lahiya. A cikin wata sanarwa da kungiyar Hamas ta fitar ta bayyana cewa, zargin mamaya na cewa kungiyar Hamas na amfani da fararen hula a matsayin garkuwar...
Gwamnatin Jihar Jigawa ta amince da ƙarin kasafin kuɗi na Naira Biliyan 75 na shekarar 2025, ga gwamnatin jiha da kuma ƙananan hukumomi 27. Kwamishinan Yaɗa Labarai, Matasa, Wasanni da Al’adu na jihar, Alhaji Sagir Musa Ahmed ne ya bayyana haka jim kaɗan bayan zaman majalisar da aka gudanar a gidan gwamnati dake Dutse, babban birnin jihar. Ya bayyana cewa, wannan ƙarin kasafin kuɗi ya samo asali ne daga ƙarin kuɗaɗen shiga domin biyan buƙatun kuɗaɗen da suka taso, da kuma ƙarfafa manyan fannoni da za su kawo ci gaba mai ɗorewa a faɗin jihar. Alhaji Sagir Musa Ahmed ya ce, majalisar ta amince da Naira Biliyan 58 ga gwamnatin jiha da kuma Naira Biliyan 17 ga Kananan Hukumomi 27,...
Ya ce ya sayi layin wayar ne daga hannun wani Audu, ɗan kungiyar Vikings wanda ya tsere yanzu. A wani lamari kuma, ‘yansanda sun kama wasu mutum huɗu da suka shiga gonar wani mutum a Lapai Gwari, inda suka saci kifi da darajar kuɗinsu ta kai Naira 750,000. Babban wanda ake zargi, Hussaini Garba, ya amsa laifi tare da bayyana Ahmed Yusuf, Ibrahim Musa da Abdulazeez Bawa a matsayin mutanen da suke sayen kifin idan ya sato. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Gwamnatin kasar Iran ta bayyana wasu abubuwan da bata amince da su ba, a jawabin bayan taro na musamman na kungiyar kasashen musulmi ta (OIC) wanda aka gudanar a birnin Doha na kasar Qatar a ranar litinin 15 gawatan Satumba da mukeciki. Sannan ta kara tabbatar da goyon bayanta ga gwagwarmayan da Falasdinawa suke yi da HKI don kwatar kasarsu da ta mamaye. A cikin wani bayanin da ma’aikatar harokokin wajen kasar Iran ta fitar a yau Laraba, Jumhuriyar Musulunci ta Iran, tana kara jaddada goyon bayanta ga al-ummar Falasdina, kuma tana kara jaddada tir da allawai da kissan kiyashin da HKI take yi a Gaza da kuma sauran yankunan falasdinawa da ta mamaye. Kuma tana godewa mutanen kasar Iran...
Majalisar dokokin kasar Chadi ta amince da gyare-gyaren kundin tsarin mulkin kasar da zai tsawaita wa’adin shugabancin kasar daga shekaru biyar zuwa bakwai da kuma baiwa shugaban kasar damar ci gaba da mulki na tsawon wa’adi maras iyaka. Majalisar dokokin kasar Chadi ta amince da sabon kundin tsarin mulkin kasar a ranar Litinin da kuri’u 171, yayin da aka kada kuri’a daya tilo da taki amincewa da hakan. A ranar 13 ga watan Oktoba ne aka shirya kada kuri’ar karshe a majalisar dattawa, a cewar sanarwar da shugaban majalisar Ali Koloto Chaimi ya fitar, kamar yadda kamfanin dillancin labaran Reuters ya ruwaito. Sannan kuma shugaban kasar zai sanya hannu kan kundin tsarin mulkin sannan ya zama doka. Shugaban kasar Chadi,...
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Isma’ilBagaei ya yi tir da samar da duk wata hulda da HKI sannan tana ganin yin haka yana dai-dai da taimaka mata ko halatta mata ayyukan ta’addancin da take aikatawa a Gaza. Kamfanin dillancin labaran Tasnem na kasar Iran ya nakalto Bagaei yana fadar haka a yau Laraba, a taron mako-mako da ya saba a ma’aikatsa a nan Tehran. Ya kuma kara da cewa, Iran tana kira ga dukkan kasashen duniya musamman kasashen yankingabas ta tsakiya da su kauracewa Haramtacciyar kasar Isra’ila (HKI) ko ta ina. Ya ce kasashen musulmi da dama, har ma da wasu wadandaba musulmi ba sun dade da katse dangantakarsu da haramtacciyar kasar, babu dangantakar diblomasiyya babu na kasuwanci da...
Kafin ya zama mataimakin shugaban jam’iyyar APC, Barde ya taɓa zama Shugaban riƙo na Karamar Hukumar Wamba a zamanin tsohon Gwamnan Jihar Umaru Tanko Al-Makura. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Sun jaddada cewa dole ne manyan kafafen sada zumunta su kare ‘yancin yin magana. Sun kuma yi kira ga ‘yan Nijeriya, ‘yan jarida, da masu fafutukar kare haƙƙin bil’adama su tashi tsaye don hana abin da suka kira yunƙurin mayar da Nijeriya “mulkin kama-karya a intanet.” Lamarin ya biyo bayan wa’adin sati guda da DSS ta bai wa Sowore da ya goge wasu wasu rubuce-rubuce game da Shugaba Bola Tinubu, wanda ya ƙi amincewa. Hakan ya sa hukumar ta shigar da shi ƙara a kotu. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya...
Hukumar NDLEA ta bayyana cewa wata ƙungiyar masu safarar miyagun ƙwayoyi ce a filin jirgin sama na Kano ta boye jakunkunan ƙwayoyi a cikin kayan matafiyan. An kama shugaban ƙungiyar, Ali Abubakar Mohammed (wanda aka fi sani da Bello Karama), tare da wasu abokan aikinsa. Hukumar ta ce mutanen ukun ba su da laifi kuma an zalunce su ne kawai. An saki su ne bayan bincike da kuma ƙoƙarin diflomasiyya na tsawon makonni. Lamarin ya tayar da hankali kan tsaro a filayen jirgin sama a Nijeriya da yadda masu aikata laifuka ke amfani da fasinjoji marasa laifi. Hukumar ta ce za a ɗauki ƙarin matakai don hana faruwar irin wannan lamari. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun...
Kwamitin bincike mai zaman kansa na Majalisar Dinkin Duniya, ya fitar da wani rahoto mai zargin Isra’ila da laifin aikata kisan kiyashi a zirin Gaza. A cikin sabon rahoto da ta gabatar a ranar Talata, MDD ta zargi shugaban kasar Isra’ila Isaac Herzog, da firaministan kasar Benjamin Netanyahu, da kuma tsohon ministan tsaro Yoav Gallant da “kimsa kisan kiyashi.”. Rahoton ya tattara batutuwan da suka shafi farar hula kai tsaye, ciki har da yara, ya kuma bayyana cewa kisan kiyashin da ake yi ya fi yawa fiye da yadda aka yi tashe-tashen hankula a baya. Masu binciken sun kuma tabbatar da cewa da gangan Isra’ila ta haifar da yanayin da ke barazana ga rayuwar Falasdinawa ta hanyar toshe hanyoyin samun...
Kasashen Iran da Saudiyya sun bukaci hadin kan hadin kan Musulmi game da halin da ake ci a yankin Wannan bayannin ya fito ne a yayin ganawar sakataren majalisar koli ta tsaron kasar Iran Ali Larijani da yarima mai jiran gado na kasar Saudiyya Mohammed bin Salman a birnin Riyadh inda suka tattauna kan dangantakar dake tsakanin kasashen biyu da kuma halin da ake ciki a yankin. Ganawar dai ta nuna wani muhimmin mataki a huldar diflomasiyya ta tsakanin Tehran da Riyadh. Larijani ya tafi Saudiyya ne bisa gayyatar da ministan tsaron kasar ya yi masa, inda ya jagoranci tawagar da ta hada da mataimakin sakataren harkokin kasa da kasa Ali Bagheri Kani da mai ba da shawara kan harkokin...
Kasashen duniya na ci gaba da yin tir da sabon farmakin soji da Isra’ila ta kaddamar kan Gaza. Kasashen Biritaniya, Faransa, Italiya, Masar, Jordan, Qatar, Spain, duk sun yi tir da farmakin kan Gaza suna masu cewa zai kara dagula halin kunci da ake ciki. Kungiyar tarayyar Turai, ta bakin Jami’ar kula da harkokin wajen ta, Kaja Kalas, ta yi kira da a sanyawa Isra’ila takunkumi domin matsa wa gwamnatin lamba ta kawo karshen hare-haren da take kaiwa Gaza, tana mai gargadin cewa al’amuran jin kai na kara ta’azzara. “Hare-haren da Isra’ila ta kai a Gaza zasu haifar da mummunan sakamako game da halin da ake ciki da karin hasarar rayuka, da barna & hijira na jama’a,” in ji Kalas...
Falasdinawa 78 ne aka kashe a yau a Gaza, mafi yawansu a birnin Gaza a yayin da Isra’ila ke ci gaba da kai hare-hare a kasa da kuma umarnin tilastawa mazauna Gaza yin kaura. An bayar da rahoton karin mutuwar mutane uku sakamakon yunwa da killace yankin. Mazauna Gaza sun bayyana tashin bama-baman a matsayin abun tashin hankali da kuma yunkurin shafe wata al’umma. Sojojin Isra’ila sun zafafa kai hare-hare a birnin Gaza, inda suka kai hari kan unguwannin da ke da yawan jama’a. Katangar da Isra’ila ta kakaba mata da kuma karancin abinci na ci gaba da zurfafa rikicin jin kai. Yakin da Isra’ila ta kwashe watanni ana yi a Gaza ya janyo hasarar rayukan fararen hula da dama....
Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar Ondo ta tabbatar da kama wata mata mai suna Iluyemi Bosede bisa zargin kashe yayarta, Tewogboye Omowumi, a Akure, babban birnin jihar. A cewar sanarwar da Jami’in Hulɗa da Jama’a na rundunar, Olayinka Ayanlade, ya fitar a ranar Talata, ya ce lamarin ya faru ne a ranar shida ga Satumba, 2025, bayan wata sa’insa da ta kaure tsakanin matar da marigayiyar kan Naira 800. Tun Tinubu yana Gwamna ba abin da ya fi shahara da shi kamar tara haraji – Adebayo DAGA LARABA: Dalilan Tashin Farashin Doya A Wasu Kasuwannin Najeriya Jami’in ya bayyana cewa Bosede ta ture ’yar uwarta har ta faɗi ƙasa, lamarin da ya haifar da mutuwarta. Ya ce, “Binciken farko ya...
Hukumar NDLEA ta bayyana cewa wata ƙungiyar masu safarar miyagun ƙwayoyi ce a filin jirgin sama na Kano ta boye jakunkunan ƙwayoyi a cikin kayan matafiyan. An kama shugaban ƙungiyar, Ali Abubakar Mohammed (wanda aka fi sani da Bello Karama), tare da wasu abokan aikinsa. Hukumar ta ce mutanen ukun ba su da laifi kuma an zalunce su ne kawai. An saki su ne bayan bincike da kuma ƙoƙarin diflomasiyya na tsawon makonni. Lamarin ya tayar da hankali kan tsaro a filayen jirgin sama a Nijeriya da yadda masu aikata laifuka ke amfani da fasinjoji marasa laifi. Hukumar ta ce za a ɗauki ƙarin matakai don hana faruwar irin wannan lamari. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun...
Dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar SDP a zaben 2023, Adewole Adebayo, ya ce Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ba shi da burin da ya wuce na tara haraji tun yana Gwamna a Legas. Adebayo ya bayyana hakan ne a wata hira da aka yi da shi a shirin Politics Today na gidan talabijin na Channels. Sojoji sun harbe mayaƙan ISWAP 8 a Borno DAGA LARABA: Dalilan Tashin Farashin Doya A Wasu Kasuwannin Najeriya A cewarsa, “Kowa ya san cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu sananne ne wajen karbar haraji. Amma wannan tsarin karbar haraji ya fi tsarin da ya tarar da shi wanda ba shi da tsari. “Ya yi hakan a Legas, sannan ya zo Abuja domin ya dora daga...
Kakakin ma’aikatar tsaron kasar Sin Jiang Bin, ya ce a baya bayan nan babban jirgin ruwan dakon jiragen sama na kasar Sin mai suna Fujian, ya doshi yankin tekun kudancin kasar, inda ya ratsa ta zirin Taiwan, a kan hanyarsa ta gudanar da gwaje-gwaje da samar da horo. Jami’in wanda ya bayyana hakan a Talatar nan, ya ce hakan bangare ne na ayyukan da aka saba gudanarwa lokaci-lokaci a wani bangare na kirar jirgin. Jiang Bin, ya yi tsokacin ne yayin da yake amsa wata tambaya mai nasaba da hakan da aka yi masa, yana mai cewa, bulaguron jirgin ya dace da dokokin kasa da kasa da ayyuka masu nasaba, kuma ba shi da wata nasaba da tunkarar wani sashe....
Ya ce, masu garkuwa da mutanen sun afka gidansa ne a daren Lahadi a lokacin da mazauna gidan ke shirin kwanciya barci. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Ƙungiyar shugabannin ƙananan hukumomin Jihar Yobe (ALGON) ta karrama Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni, da lambar yabo ta karramawa bisa himmar ayyukan raya ƙasa da gwamnatinsa ke gudanarwa a faɗin jihar. Karramawar, wacce aka bayyana a matsayin irinta ta farko a tarihin Jihar Yobe, shugabannin ƙananan hukumomi 17 na jihar suka ba da ita ga gwamna. Gwamnatin Kano ta gayyaci Mai Dubun Isa da Shehi Tajul-Izzi kan shirya muƙabala Sojoji sun harbe mayaƙan ISWAP 8 a Borno Da yake jawabi, shugaban ƙungiyar ALGON a Jihar Yobe, kuma shugaban ƙaramar hukumar Damaturu, Alhaji Bukar Adamu, ya yaba da yadda Gwamna Buni yake gudanar da harkokin mulki na bai ɗaya. Ya ce nasarorin da aka samu sun haɗa da fannoni na...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Gwamnatin Tarayya ta ce Najeriya na rasa sama da Dala Biliyan 10 duk shekara sakamakon asarar amfanin gona bayan girbi. Ministan Noma Sanata Abubakar Kyari ne ya bayyana haka a wajen kaddamar da shirin Hanyar Inganta Noma da Kayayyakin Mire Rayuwa a Yankunan Karkara G.R.A.I.N a ƙaramar hukumar Birnin Kudu ta Jihar Jigawa. Ya ce asarar na faruwa ne saboda rashin ingantattun wuraren ajiya, karancin ababen more rayuwa, sauyin yanayi da kuma ambaliya. Kyari ya bayyana cewa noma na bada gudunmawar kashi 24 bisa 100 na Jimillar Darajar Kayayyaki da Ayyuka da Kasa ta Samar a Cikin Shekara GDP, inda ƙananan manoma ke samar da sama da kashi 70 bisa 100 na abincin da ake ci a ƙasa....
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Sojojin Najeriya sun kashe aƙalla mayakan ƙungiyar ISWAP 8, ciki har da manyan kwamandojinta biyu a Jihar Borno. Wata majiyar leƙen asiri daga rundunar haɗin kai ta OPHK ta bayyana cewa an kashe ’yan ta’addan ne a wata arangama da suka yi da sojojin a kan hanyar Maiduguri zuwa Baga a safiyar ranar Litinin. DSS ta maka Sowore da Facebook a Kotu kan cin zarafin Tinubu Gwamnatin Kano ta gayyaci Mai Dubun Isa da Shehi Tajul-Izzi kan shirya muƙabala A cewar majiyoyin, an yi arangamar ce a kusa da Garin Giwa da ke gab da ƙauyen Kauwa, lokacin da ’yan ta’addan suka yi wa dakarun da ke sintiri kwanton ɓauna. “A yayin wannan artabu, an kashe ’yan ta’adda takwas, ciki...
Danja ya ce, sojojin a yayin da suke aiki da sahihan bayanan sirri dangane da shirin kai hari kan al’ummar Chanchangi da kungiyar ta’adda ta Bojo ke shirin yi a ranar 15 ga Satumba, 2025, sun yi artabu da ‘yan ta’addan a kan hanyar Demeva zuwa Chanchangi. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Yakin da aka kwashe fiye da shekara ana yi yankin zirin Gaza ya haifar da mummunar asara rayukan fararen hula, yayin da lamura ke ci gaba da dagulewa a yankin inda Isra’ila ke ci gaba da kisan kare dangi ta hanyar kai hare-hare ta sama da kasa da kuma tana amfani da yunwa a matsayin wani makami na kisan mummuke, hakan ya jawo damuwa sosai a mataki na kasa da kasa na irin laifukan yaki da kuma cin zarfin dan adam da Israila ke yi. Tun watan oktoban shekara ta 2023 sojojin isr’ila sun kai hare-hare da yayi sanadiyar shahadar falasdinawa sama da 64964 tare da jikkatar sama da 165312, kamar yadda ma’aikatar lafiya ta yankin gaza ta bayyana. Kungiyoyin...
Majiyar sojojin kasar Yamen sun sanar cewa a ci gaba da hare-haren wuce gona da iri da HKi ke yi, Jiragen yakin HKI sun kai hari kan tashar jirgin ruwan hudaidai dake kasar kuma sun samu nasarar kakkabo makaman. Kakakin sojin kasar yamen yahya Saree ya fadi a cikin shafinsa na x cewa makaman kariya da muke dasu sun kalubalanci hare haren da Isra’ial ta kai a tashar jirgin ruwa na Hudaida, Isra’ila ta harba makamai masu linzami 12 a tashoshin jiragen ruwanta guda 3. Gidan rediyo isra’ila ya sanar cewa babban dalilin kai harin shi ne don a hana gudanar da ayyuka na tsawon makwanni, bayan gyara wuraren da suka lalace a hare-haren baya bayan nan da aka kai,...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Shugaban ya yaba da abinda ya kira kwarewa da juriya irin na Amusan, tare da cewa aikinta ya sake misalta irin daukakar da yan Nijeriya za su iya samu ta hanyar aiki tukuru da nuna kwazo, Tinubu ya yi fatan Gumel da Amusan su ci gaba da samun nasara a ayyukansu tare da ba su tabbacin gwamnati za ta ba su cikakken goyon baya. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Rahotanni sun bayyana cewa kasar iran ta bayyana sabbin kayayyaki guda 5 da ta kera a wajen babban taron kere-kere na kasa da kasa karo na 23,kuma dukkansu kamfanonin kasar iran ne suka yi su domin rage dogaro da kayyakin kasashen waje. Taron ya samu halartar mataimakin shugaban hukumar kula da kimiya da fasaha ta kasa da sauran shuwagabannin kamfanoni inda ya nuna irin karfin iran wajen kere-kere da kuma mayar da hankali kan kamfanoni dake filin shakatawa na pardis technology park. Daga cikin magungunan da aka gabatar a wajen akwai Sirolimus wanda Zist takhmir company ya kera, kuma magungunan rigakafi ne da ake amfani da su wajen hana dashen gabobin jiki da kuma kula da cututtuka da ba kasafai...
Mohammad Islami shugaban hukumar kula da makamashin nukiliya na Iran ta fadi a bayan taron da hukumar ta IAEA dake gudanarwa a Vienna yanzu haka cewa yana neman hukumar ta IAEA ta goyi bayan kudurin da ta fitar kuma ta yi Tir da harin wuce gona iri da hki ta kai kan tashoshin nukiliyarta. Wakilai guda 180 a hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya ne suka hallara abirnin viyana daga ranar 15-19 domin gudanar da taron kasa da kasa karo na 69 da hukumar ta duniya ke shiriya a hedkwatarta dake Vienna na kasar Austeria Yace mun bayyana cewa alummar Iran basu da rauni wajen fuskantar duk wata barazana, kuma basu da niyyar mika wuya, ,ya kara da cewa...
Tsohon Shugaban Ƙasar najeriya, Goodluck Jonathan, ya isa birnin Accra, na Ƙasar Ghana, domin halartar taron Democracy Dialogue na 2024 da Gidauniyarsa ta shirya tare da hadin gwiwar gwamnatin kasar. Taron na bana, mai taken “Dalilan Da Ke Sa Dimokuraɗiyya Ta Mutu”, zai hada shugabanni da masana don tattauna ci gaba, kalubalen, da makomar dimokuradiyya a Yammacin Afirka ke fuskanta. Jonathan ya ce yana fatan wannan tattaunawa za ta karfafa dimokuraɗiyya a yankin tare da kawo zaman lafiya, tsaro da kyakkyawan shugabanci. Taron Democracy Dialogue ya zama muhimmin dandali a kowace shekara a Yammacin Afirka don tattauna makomar dimokuradiyya, inda a baya ya kan jawo ’yan siyasa, kungiyoyi, da abokan hulda na kasa da kasa. A wannan karon ana sa...
Hukumar Tace Fina-Finai da Dab’i ta Jihar Kano ta haramta shirya duk wata muƙabala tsakanin mawaƙan yabon Annabi (S.A.W), tare da gayyatar mawaƙa Usman Maidubun Isa da Shehi Mai Tajul’izzi su bayyana a gabanta. Hukumar ta kuma gayyaci mawaƙan ne tare da sauran waɗanda suka jagoranci muƙabalar da fitattun mawaƙan biyu suka yi ranar Litinin, da su bayyana a gabanta cikin sa’o’i 24. Kukan al’umma kan lalacewar hanyar Dukku DSS ta maka Sowore da Facebook a Kotu kan cin zarafin Tinubu Hakan na zuwa ne ƙasa da kwana ɗaya bayan ɓullar wata muhawara da aka yi tsakanin Usman Maidubun Isa da Shehi Mai Tajul’izzi kuma ta karade shafukan sada zumunta, wacce hukumar ta bayyana a matsayin karya dokokin aikinta. Shugaban...
Hukumar Tsaron Farin Kaya a Nijeriya DSS, ta gurfanar da fitaccen ɗan gwagwarmayar nan, Omoyele Sowore a kotu. A ƙunshin ƙarar da DSS ta gabatar a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, ta haɗa da shafukan sada zumunta na X da kuma Facebook, inda take zarginsu da ba da ƙofar aibata Shugaba Bola Ahmed Tinubu. Bida Poly ta sa sojoji kula da jarrabawar ɗalibai Kukan al’umma kan lalacewar hanyar Dukku Darekan shigar da ƙara na Ma’aikatar Shari’a ta Tarayya, M.B Abubakar da wasu lauyoyi huɗu —M.E. Ernest da U.B. Bulla da C.S. Eze da kuma E.G. Orubor, ne suka shigar da ƙarar a madadin Gwamnatin Tarayya da kuma hukumar ta DSS. DSS wadda ta kafa hujja da sashe na...
“Bayan karbar mukaminsa na sabon kwamandan hukumar NSCDC na jihar Kano, kwamared Bala Bodinga ya umurci jami’ansa da su sadaukar da kansu ga muhimmin aiki na tabbatar da amincin muhimman kadarori da ababen more rayuwa na kasa. “Kwamandan jihar ya ba da umarnin cewa, ba dare ba rana, cikin sa’o’i 24, dole jami’an hukumar su rika yin sintiri da sanya ido domin dakile ayyukan barayi da masu aikata laifuka a lunguna da sako na jihar,” inji shi. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Yadda kasashen yammacin duniya suka ki sauke nauyin dake wuyansu, ya danne wa kasashe masu tasowa hakkinsu. Misali, a lokacin da ake samun bazuwar annobar COVID-19, dimbin kasashen yamma sun yi ajiyar alluran rigakafi a gida, inda suka hana fitar da su zuwa ketare, da musayar fasahohi masu nasaba da su. Sai dai a lokacin, hukumomi masu kula da harkokin kasa da kasa, kamar su Hukumar Lafiya ta Duniya, da Majalisar Dinkin Duniya dukkansu sun kasa tilasta musu sauya manufofinsu. Wannan tsarin kasa da kasa, idan mun bar shi haka ba tare da wani sauyi ba, to, wata rana za mu ga an koma tsarin zalunci na zamanin mulkin mallaka, wanda zai yi barazana ga hakkin rayuwa, da raya kai...
Shugaban kasar Iran ya bayyana cewa: Saudiyya na iya taka muhimmiyar rawa wajen hadin kan kasashen musulmi Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya jaddada cewa: Gwamnatin sahayoniyya ba za ta kuskura ta kai hari ko kai wa wata kasa ta Musulunci hari ba matukar kasashen musulmi suka hade kansu; kuma Saudiyya za ta iya taka muhimmiyar rawa a tafarkin hadin kan kasashen musulmi. A yayin ganawarsa da yarima mai jiran gado na Saudiyya Mohammed bin Salman a gefen taron Doha, Pezeshkian ya bayyana jin dadinsa da yadda dangantakar dake tsakanin kasashen biyu ke kara bunkasa, yana mai cewa: Zurfafa da karfafa hadin gwiwar dake tsakanin kasashen Iran da Saudiyya zai kare muradun kasashen biyu, da kuma muradun al’ummomin kasashen biyu,...
Shugaban kasar Iran ya bayyana cewa: Ta’addancin yahudawan sahayoniyya kan Qatar zalunci ne ga diflomasiyya Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya bayyana cewa: Harin wuce gona da iri kan kasar Qatar, wani hari ne da kungiyar yahudawan sahayoniyya ta shirya kai wa, da nufin dakile yunkurin diflomasiyya na kawo karshen kisan kiyashin da ake yi a Gaza. Shugaba Pezeshkian ya bayyana hakan ne a jiya Litinin a yayin taron gaggawa na shugabannin kasashen kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta OIC da kungiyar hadin kan kasashen Larabawa dangane da harin da gwamnatin mamayar Isra’ila ta kai kan Qatar. Shugaban ya kara da cewa, wannan cin zarafi na diflomasiyya ya wuce matsayin laifi kawai; ya zama sanarwar aikin rashin kunya da ya...
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran ya tabbatar da haƙƙin kasashe na haɓakawa da amfani da makamashin nukiliya na zaman lafiya Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Jamhuriyar Musulunci ta Iran, Isma’il Baqa’i, ya yi ishara da shawarar da Iran ta gabatar na daftarin kudurin da ya haramta kai hare-hare kan cibiyoyin makamashin nukiliyar kasashe masu zaman lafiya, yana mai cewa: Dukkanin kasashe na da hakkin yin amfani da makamashin nukiliya don zaman lafiya da kuma hakkin samun ingantacciyar kariya daga duk wani hari ko barazanar kai hari. A cikin sakon da ya aike ta dandalin X a yau Talata, Ismail Baqa’i ya yi ishara da shirin Iran a babban taron hukumar kula da makamashin nukiliya ta kasa da kasa (IAEA) da ake...
Kungiyar kare hakkin bil’adama ta Human Rights Watch ta ce: Laifin da Isra’ila ta yi na kashe ‘yan jaridun Yemen babban ta’addanci ne Kungiyar kare hakkin bil’ adama ta Human Rights Watch ta tabbatar da cewa: Harin da yahudawan sahayoniyya suka kai a ranar 26 ga watan Satumba kan ‘yan jaridun kasar Yemen, wanda ya yi sanadiyar mutuwar ‘yan jarida sama da 30, laifi ne da ba za a iya kubutar da girman laifin kan wanda ya aikata ba. A cikin rahoton baya-bayan nan, kungiyar ta fitar ta bayyana cewa, ta tattara bayanan harin da makiya yahudawan sahayoniyya suka kaddamar a ranar 10 ga watan Satumba kan hedkwatar kafafen yada labarai a kasar Yemen, kuma ta yi la’akari da wannan...

Kungiyar Kare Hakkokin Bil’Adama Ta Siriya Ta Bankado Karin Fararen Hula Da Aka Kashe A Rikicin Suweida
Kungiyar Kare Hakkokin Dan Adam ta Siriya ta bayyana sabbin mutanen da suka mutu sakamakon harin Suweida Kungiyar kare hakkin dan adam ta Siriya (SOHR) ta bayyana wasu sabbin fararen hula tara da aka ci zarafinsu a lokacin abubuwan da suka faru a Suweida a watan Yulin da ya gabata. Hukumar da ke sa ido kan lamarin ta bayyana cewa, wadanda aka kashen da suka hada da mata biyu, an kashe su ne a filin wasa a lokacin da wasu ma’aikatun tsaro da na cikin gida na gwamnatin rikon kwarya suke lardin na Suweida, tare da halartar mayakan ‘yan kabilar Larabawan Bedouin. Hukumar da ke sa ido kan lamarin ta ce adadin mutanen da suka mutu a watan Yulin da...
An garzaya da ita asibiti, amma daga baya likitoci suka tabbatar da mutuwarta. ’Yansanda sun kama Bosede kuma suna bincike a kan lamarin. Kakakin rundunar, DSP Olusola Ayanlade, ya ce za su tabbatar da adalci. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Rikicin kwamitin gudanarwa da malaman Kwalejin Fasaha ta Tarayya da ke Bida (Bida Poly), ya ƙara ƙamari bayan da makarantar ta dakatar da ayyukan Kungiyar Malamai (ASUP) sannan ta kawo sojoji domin kula da jarrabawa da dalibai ke gudanarwa. Ƙungiyar ASUP reshen kwalejin ta shiga yajin aiki mara wa’adi, domin neman a biya su alawus ɗin ƙarin aiki na watanni 18 da suka wuce. Ƙungiyar ta umarci mambobinsu da kada su gudanar da jarrabawar zangon da ta fara ranar Litinin, 15 ga Satumba, 2025. Wani ma’aikacin makarantar ya shaida wa wakilinmu cewa sojojin an gayyace su ne domin kare ɗalibai da wasu malamai daga shirin da ASUP ke yi na hana gudanar da jarrabawa. ’Yan bindiga sun kai wa sojoji...
Duk da cewar an yi yarjejeniya tsakanin ɓangarorin biyu, rikici ya sake ɓarkewa bayan NUPENG ta ce Dangote bai cika alƙawari ba. Amma matatar ta musanta zargin, inda ta bayyana cewa ma’aikatanta na da damar shiga ƙungiya idan sun so, amma ba dole ba ne. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Wasu mutum shida sun shiga hannun ’yan sanda kan zargin satar zinari da kuɗinta ya haura Naira miliyan 109.5 a Jihar Kebbi. Sashen binciken manyan laifuka na rundunar ’yan sanda a jihar Kebbi na tuhumar su da sace sarkoƙin zinare guda biyar sauran kayan zinare daga wani gida a garin Ka’oje, Ƙaramar Hukumar Bagudo. Sauran sun haɗa da zobba huɗu da munduwar hannu tara, da nauyinsu ya kai gram 782.7 — dukkansu mallakar ’ya’ya da ’yan uwar mai gidan. Wanda ake tuhuma ya amsa laifi Bayan samun koken, jami’an suka kama Ibrahim Abubakar Ka’oje, jami’i a Hukumar Gyaran Hali ta Kasa, wanda a yayin bincike, ya amsa laifin. ’Yan ‘Mafiya’ na ƙoƙarin kashe matatar man fetur da na gina —Ɗangote...
Mai kuɗin Afrika kuma Shugaban Matatar Mai ta Ɗangote, Alhaji Aliko Ɗangote, ya zargi wasu manyan masu harkar mai da shirya maƙarƙashiya domin kashe matatarsa. Ɗangote ya yi zargin cewa miyagun ’yan kasuwan suna ƙoƙarin kashe matatar mansa mai darajar dala biliyan 20, kamar yadda aka kashe masana’antar tufafi ta ƙasar. Ya bayyana haka ne a ranar Litinin a Legas yayin bikin cika shekara ɗaya da fara samar da fetur a matatar, inda ya ce tafiyar ta kasance cike da ƙalubale tun daga farko. “A gaskiya tafiyar shekara ɗaya da ta wuce ta yi mana matuƙar wuya. Mun zo mu sauya tsarin kasuwancin man ƙasa. Amma wasu na ganin mun raba su da hanayar cin abinci bakinsu,” in ji shi....
Sojoji biyu sun ji rauni bayan wani harin kwanton baya da ’yan bindiga suka kai kan ayarin motocin Kwamandan kwamandan Rundunar Sojoji ta 382 Ƙaramar Hukumar Faskari ta jihar Katsina. Lamarin ya faru ne a ƙauyen Ruwan Godiya, kan hanyar Sheme–Kankara, lokacin da tawagar Operation Fansan Yamma (OPFY) ke wucewa. Ganau sun ce sojojin na kan hanyar ziyartar sansanonin sojoji a yankunan Faskari da Mabai da Ɗan Ali lokacin da aka kai musu hari. Sai dai sun yi nasarar tunkarar ’yan bindigar har suka kuvuta, kodayake sojoji biyu sun samu raunuka na harbi kuma aka kai su asibitin sojoji domin jinya. An kai wa sojojin harin ne a rana ɗaya da shugabannin al’ummar Faskari suka zauna da wakilan ’yan bindiga...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Matakin hana malaman da ba su da rajista hawa mumbari a Neja yana ci gaba da yamutsa hazo a ciki da wajen jihar. Yayin da wasu suke ganin wannan mataki bai dace ba, wasu kuwa gani suke faduwa ta zo daidai da zama, wato matakin ya zo a daidai lokacin da ake bukata. NAJERIYA A YAU: Yadda Wasu Al’ummomi Suke Kare Kansu Daga Barnar Ambaliyar Ruwa DAGA LARABA: Dalilan Da Suka Sa Nayi Yunkurin Kashe Kaina Har Sau Uku Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari a kan tanadin Dokar Kasa game da wannan batu. Domin sauke shirin, latsa nan
JMI ta zama zakara a gasar damben girgajiya ta kasa da kasa bayan ta fara shiga gasar shekaru 12 da suka gabata . Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi yana taya tawagar yan damben murna da nasarar da suka samu, ya kumakara da cewa wannan shi ne nasara ta wasannan kasa-da kasa har guda 6 wadanda Iran take samun lambobin zakara a cikinsu a wannan shekarar. Labarin ya kara da cewa yan damben Iran sun sami wannan nasarar kwana guda kafin a kammala gasar. An bayyana nasarar da yan damben Iran suka samu ne a jiya Litinin da yamma a birnin Zagreb inda aka gudanar da gasar. Sun sami lambobin...
An fara taron hukumar IAEA ta kasa da kashe karo na 69TH a jiya Litinin, inda a taron ne ake fayyana al-amura masu muhimmanci da ya shafi makamashin Nukliya a duniya, kuma tuni shugaban hukumar makamashin Nukliya ta kasar Iran Muhammad Eslami yakejagorantar tawagar Iran a taron. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran, ya bayyana cewa a irin wannan taron na shekara-shekara inda kuma aka tattauna abubuwa masu muhimmanci dangane da makamashin Nukliya. Kafin ya bar nan Tehran Eslami ya ce zai gabatar da al-amura wadanda suka shafi sabawa dokokin hukumar da IAEA ta kasa. Ya kuma kara da cewa JMI ba zata saba barin hakkinta tashe makamashin Uranium wanda ya zo cikin yarjeniyar NPT. Eslami ya kammala da...
Gwamnatin kasar Spaine ta soke kontaragin sayan makama daga HKI wadanda yawansu ya kai Euro Miliyon 700, saboda kissan kiyashin da ke faruwa a gaza. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa a jiya Litinin ne gwamnatin firay minister Pedro Sanchez ta bada wannan sanarwan ta kuma kara da cewa makaman su ne makamai masucilla rokoki samfurin Elbit kirar HKI. Labarin ya kara da cewa Madrid ta soke wani kontaragi wanda ya kai Eur miliyon 287 da HKI. Na sayan garkuwan tankunan yaki wadanda za’a kerasu a kasar karkashin lacicin HKI a kasar Espania. Banda haka firay minister Pedro Sanchez ya bukaci a haramta HKI daga dukkanin wasannin nakasa da kasa saboda kissan kiyashin da take aikata...
Jaragen yaki wadanda ake sarrafasu daga nesa wato Drones sun fada kan wurare masu muhimmanci a kudancin kasar Falasdinu da aka mamaye, yan sa’o’in da suka gabata. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto kakakin sojojin kasar Yemen Burgediya Janar Yahyah Saree yana fadar haka a dazo-dazon nan .Ya kumakara da cewa. hare-haren sun hada da Drons guda 4, 3 daga cikinsu sun fada kan tashar jiragen sama na Ramon da ke kusa da Ummu Rash-rash ko Ilat kamar yaddayahudawan suke kiransa. Sannan guda kumaya fada kan sansanin sojojin HKI na Negev duk a kudancin kasar. Ya ce an kai hare-haren ne don goyon bayan Falasdinawa wadanda HKI take kashewa tunkimani shekaru biyu da suka gabata. Sannan sanarwan...
Babban daraktan kamfanin dillancin labaran kasar Qatar ya bayyana cewa taron gaggawa na kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta OIC da ke tafe yana nuni da wani muhimmin sauyi na hadin kan kasashen larabawa da musulmi dangane da laifukan da ake aikatawa kan al’ummar Palastinu. A cewar Pars Today, dukkanin idanuwa a ranakun Lahadi da Litinin (15-16 ga Satumba, 2025) za su kasance a Doha, babban birnin kasar Qatar, wanda zai karbi bakuncin taron gaggawa na shugabannin kasashen Larabawa da na Islama, don ba da amsa ga baki daya kan harin da Isra’ila ta kai kan Qatar. Ana gudanar da wannan taron gaggawa ne a cikin yanayi na musamman na yanki da na duniya kuma ya biyo bayan harin da...
Ministan tsaro na kasar Venezuela Vladimir Padrino López ya gargadi gwamnatin Amurka dangane da duk wani kokari na kaiwa kasar Venuzuela hare hare saboda kifar da gwamnatin shugaba Nicolas Madoro. Tare da fakewa da fasakorin kwayoyi. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Vladimir yana cewa take-taken gwamnatin Amurka na sojojin da ta kawo a teken carebian ya yi kama da takalar yaki ne da kasar Venezuela , kuma idan haka ne, to sojojin sa a shirye suke su fuskance su, su kumakare kasarsu. Kamfanin dillancin labaran IP nakasar Iran ya bayyana cewa, Amurka ta fara kai ruwa rana da gwamnatin shugaba Madoro ne tun lokacinda shugaban Amurka Donal Trump ya bayyana shugaban kasar ta Venezuela a...

Pezeshkian: Ya kamata kasashen musulmi su yanke alaka da gwamnatin sahyoniya tare da kiyaye hadin kai
Shugaban kasar Iran yana mai jaddada cewa wajibi ne kasashen musulmi su karfafa hadin kai da hadin kai don mayar da martani ga ayyukan gwamnatin sahyoniyawan, inda ya ce: Wajibi ne kasashen musulmi su tsaya tsayin daka tare da daukar matakai na zahiri a fagen tattalin arziki, al’adu da zamantakewa, yanke alakarsu da gwamnatin sahyoniyawan. Masoud Pezeshkian shugaban kasar Iran a jiya litinin kafin ya tashi zuwa kasar Qatar domin halartar taron gaggawa na kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta OIC da kungiyar hadin kan kasashen larabawa dangane da harin da gwamnatin sahyoniyawan ta kai wa birnin Doha, ya bayyana cewa: “Gwamnatin yahudawan sahyoniya ba ta amince da wani iyaka ga kanta ba, kuma tare da goyon bayan Amurka, ta...
Ya ce kuma kayan da ake fitarwa zuwa waje waɗanda ba man fetur yanzu su kusa yin kai da kai da fetur. Ya ƙara da cewa ajiyar kuɗaɗen ƙasar a waje ya haura kusan dala biliyan 42, daga biliyan 32 lokacin da Tinubu ya hau mulki. Har ila yau, ya ce an biya bashin da ya haura biliyan bakwai, ciki har da miliyan 800 da ake bin jiragen saman Nijeriya. Fadar Shugaban Ƙasa ta ce yanzu jihohi na iya biyan albashi da fansho a kan lokaci, sannan suna da rarar kuɗi don ayyukan raya ƙasa, abin da ba a saba gani ba a baya. “Bayan shekara biyu da watanni biyar kacal a ofis, Shugaba Tinubu ya cimma abubuwa da dama....

Hadin Gwiwar Raya Tattalin Arziki Da Cinikayya Da Makamashi Tsakanin Sin Da Rasha Ba Abun Zargi Ba Ne
Har ila yau, Lin ya ce matsayin kasar Sin dangane da rikicin kasar Ukraine bai sauya ba, cewa tattaunawa, da gudanar da shawarwari ne kadai hanyoyi mafiya dacewa na warware rikicin. Har kullum Sin na kan turbar adalci game da rikicin, tana kuma ci gaba da ingiza bukatar komawa teburin shawara tun barkewar rikicin. (Saminu Alhassan) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp

Kakakin Majalisar Jigawa Ya Tsallake Rijiya Da Baya, Tawagar Jami’an Tsaronsa Sun Ji Rauni A Wani Hatsari A Jihar
“Sauran motocin da ke cikin ayarin, ciki har da wacce ke ɗauke da shugaban majalisar, da ƙyar suka iya tsayawa wanda tsakaninsu mitoci kaɗan ne daga wurin da haɗarin ya afku,” in ji wani ganau. Majiyoyin tsaro sun tabbatar da cewa, an garzaya da jami’an ‘yansandan da suka samu raunuka zuwa babban asibitin Gumel a sume amma daga baya sun farfaɗo. Da yake magana kan lamarin, mataimakin shugaban majalisar, Aqeel Akilu, ya yi godiya ga Ubangiji cewa, ba a rasa rayuka ba. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko...

Tawagogin Sin Da Na Amurka Sun Sake Tattaunawa Game Da Batutuwan Tattalin Arziki Da Cinikayya A Rana Ta Biyu
A yau Litinin ne tawagogin kasashen Sin da Amurka, suka sake tattaunawa a rana ta biyu, game da batutuwan tattalin arziki da cinikayya a birnin Madrid na kasar Sifaniya. A jiya Lahadi, sassan biyu sun gudanar da zaman farko ne a fadar Santa Cruz, inda ofishin ministan harkokin wajen kasar ta Sifaniya yake. A cewar kakakin ma’aikatar cinikayyar kasar Sin, sassan biyu za su tattauna batutuwan da suka hada da matakin Amurka na kakaba jerin haraji daga bangare guda, da keta matakan kayyade fitar da hajoji, da batun dandalin TikTok. (Saminu Alhassan) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don...

Sabunta Cinikin Ba Da Hidima, Masu Zuba Jari Na Waje Suna Ganin “Damar Da Kowa Ke Bukata A Kowane Lungu Na Sin”
Bikin hada-hadar ba da hidima na Sin wato CIFTIS na bana da ya kare a jiya a nan Beijing ya jawo hankalin kasashe da kungiyoyin kasa da kasa 85 da suka gudanar da baje koli da tarurruka, kusan kamfanoni 500, ciki hadda wasu daga cikin manyan kamfanoni 500 dake sahun gaba a duniya da manyan kamfanoni masu jagorantar bangarorinsu, sun halarci bikin, kuma an cimma nasara a fannoni sama da 900. A yayin da duniya ke fuskantar rashin tabbas, bikin CIFTIS ya karfafa mu’amala da kuma samun riba da juna. Alkaluma na nuna cewa, a shekara ta 2024, jimillar cinikin ba da hidima na Sin ya fara wuce dala tiriliyan 1 a karon farko, wanda ya zama sabon tarihi, kuma...
Aƙalla masallata 40 ’yan bindiga suka sace a wani masallaci da ke Gidan Turbe a Karamar Hukumar Tsafe ta Jihar Zamfara da safiyar wannan Litinin. Majiyoyi sun ce an yi awon gaba da masallatan ne zuwa dazukan Gohori da ke yankin Tsafe. Hauhawar farashi ya ragu a watan Agusta — NBS NDLEA ta kama ɗan Indiya da ƙwaya ta Naira biliyan 3 a Legas Wannan harin dai kai tsaye masu ruwa da tsaki na kallonsa a matsayin kawo ƙarshen yarjejeniyar sulhu tsakanin ’yan bindigar da mahukuntan jihohin Zamfara da Katsina. A baya-bayan nan ne jihohin Katsina da Zamfara suka ƙulla yarjejeniyar sulhu tsakaninsu da ’yan bindigar da suka addabi al’ummar jihohin arewa maso yammacin Najeriyar. Yarjejeniyar sulhu da aka cimma...
Hukumar ƙididdigar a Najeriya NBS ta bayyana cewa an samu raguwar hauhawar farashin kaya a watan Agusta idan aka kwatanta da watan Yulin da ya gabace shi. Cikin sabbin alƙaluman da NBS ta fitar a ranar Litinin sun nuna cewa an samu raguwar kashi 1.76 a watan Agustan saɓanin watan Yulin, wanda ya nuna karo na hudu ke nan a jere hauhawar farashin yana sauka. NDLEA ta kama ɗan Indiya da ƙwaya ta Naira biliyan 3 a Legas Kundin Bajinta na Guinness ya taya Hilda Baci murna Rahoton na hukumar NBS na zuwa ne kwanaki bayan da Shugaba Bola Tinubu ya bayar da umarnin karya farashin kayan abinci ƙasar. A watanin baya-bayan an riƙa samun raguwar hauhawar farashin kayyaki a...
Majalisar dattawa ta dakatar da Sanata Akpoti-Uduaghan a ranar 6 ga Maris, 2025, na tsawon watanni shida. Duk da cewa an kalubalanci lamarin a kotu, amma babbar kotun tarayya ba ta bayar da wani umarni na soke dakatarwar ba ko kuma tilasta sake dawo da ita bakin aiki. A ranar 4 ga Satumba, 2025, Sanatar ta sanar da ofishin magatakarda akan aniyar ta na ci gaba da ayyukan majalisa, nan take, ofishin ya mika wasikar ga shugabannin majalisar dattawan. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu...
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Lin Jian, ya ce Sin na kira ga Amurka, da ta gaggauta dakatar da shuka kiyayya, da haifar da tashin hankali, da rura wutar gaba a tekun kudancin kasar Sin, kana ta kyale a dawo da yanayin zaman lafiya da daidaito a yankin. Lin Jian, ya bayyana hakan ne yau Litinin, yayin taron manema labarai da aka saba gudanarwa, lokacin da aka yi masa tambaya kan batun. Wasu rahotanni daga kafofin watsa labarai sun bayyana cewa, a baya bayan nan, sakataren harkokin wajen Amurka Marco Rubio, ya fitar da sanarwa dake cewa Amurka na goyon bayan kasar Philippines, game da watsi da ta yi da tsare-tsaren kasar Sin na kafa yankin kare muhallin halittu...
Mataimakinsa kan harkokin majalisa Honarabul Attahiru Danmadi ne ya wakilci dan majalisar ya kuma tabbatarwa wadanda lamarin ya shafa kokarinsa kan daukar matakan da suka kamata domin tabbatar da tsaron rayukan su da dawowa da zaman lafiya a yankunan. Garuruwan da ‘yan bindigar suka tarwatsa a gundumar Kuchi sun hada da Fakku, sha’alwashi, tulluwa da Rafin- gora a inda mutane bakwai suka rasa rai. A gundumar Jabo kuwa kauyukan da lamarin ya shafa su ne; Gesolodi, Hilya, Guraye, Guma, Chakai, Modo, Badariya, Tafki, Balera, Gudumawa da Rafin shinka. “Mun girgiza kwarai da wannan halin da kuke ciki. A matsayina na wakilin ku, zan ci-gaba da kokarin da ya kamata a majalisa domin ganin jami’an tsaro sun kawo karshen...