Gwamnatin Kano ta haramta liƙa hotuna ko rubutu marasa ma’ana a A-Daidaita-Sahu
Published: 31st, May 2025 GMT
Hukumar Tace Fina-finai ta Jihar Kano ta sanar da haramta rubuce-rubuce ko liƙa hotuna “marasa ma’ana” ko na batsa a kan baburan A-Saidaita-Sahu a fadin jihar.
Wannan mataki, wanda Shugaban Hukumar, Abba El-Mustapha ya jagoranta, yana da nufin tabbatar da ɗa’a da kuma tabbatar da cewa abubuwan da ake nunawa a bainar jama’a sun dace da ƙa’idojin hukumar.
A cewar Abdullahi Sani Sulaiman, Jami’in Hulɗa da Jama’a na hukumar, an ɗauki wannan mataki ne a sakamakon ƙorafe-ƙorafen al’ummaar Kano game da yadda masu A-Daidaita-Sahu sahu ke ado da hotuna da rubuce-rubuce masu ban haushi a bainar jama’a.
Abba El-Mustapha ya jaddada cewa dokar da ta kafa Hukumar ta ba ta cikakken iko don sa ido da gurfanar da masu laifi. Don tabbatar da bin doka, El-Mustapha ya jagoranci wata tawaga ta musamman a wani gangamin wayar da kai zuwa manyan tituna a Kano, ciki har da Titin Maiduguri, Titin Zaria, da Titin Sani Marshal.
Mai neman aiki ya suma bayan matarsa ta haifi ’yan uku Mutanen da suka mutu a ambaliyar Neja sun ƙaru zuwa 88 —NSEMAA yayin aikin, ya nanata cewa hukumar ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba wajen hukunta duk wanda aka samu da laifin karya ka’idojinta, ba tare da la’akari da matsayinsa ba.
El-Mustapha ya ƙara da cewa, bisa ga umarnin hukumar, duk wani aikin adabi ko na fasaha dole ne a miƙa shi ga Hukumar ta tantance shi kafin a fitar da shi ga jama’a.
Ya yi kira ga al’umma da su ba hukumar cikakken goyon baya da haɗin kai don ci gaban Jihar Kano.
Wannan sabon mataki ya biyo bayan wani shiri na wayar da kai da aka yi a baya inda hukumar ta tattauna da fiye da masu adaidaita sahu 20, inda ta yi musu gargaɗi game da sabbin dokokin. Hukumar ta bayyana cewa sabuwar dokar ta fara aiki cikakke.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: El Mustapha ya
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamnati ta ƙaddamar da jiragen ruwa na zamani 20 a Sakkwato
Gwamnan Sakkwato, Dakta Ahmad Aliyu, ya ƙaddamar da jiragen ruwa na zamani guda 20, tare da riguna ruwa (life jackets) 2,000, domin rage haɗurran da ke aukuwa sakamakon ambaliya da nutsewar jirage a sassan jihar.
An ƙaddamar da jiragen ne a ƙaramar hukumar Wamakko a ranar Laraba, inda gwamnan ya bayyana cewa wannan mataki na daga cikin shirin gaggawa na tallafa wa al’ummar da ke fama da illar ambaliya da haɗurra a ruwa.
Microsoft ya ƙwace shafukan wasu kamfanoni 340 a Najeriya An kama ɗaya daga cikin manyan kwamandojin IPOB“Mun dauki wannan mataki bayan rahotannin da muke samu na yawaitar hatsarurruka da rasa rayuka da dukiya sakamakon jiragen katako da mutane ke amfani da su,” in ji Gwamna Ahmad Aliyu.
Gwamnan ya miƙa godiya ga shugabar hukumar bayar da agajin gaggawa ta ƙasa (NEMA), Hajiya Zubaida Umar, bisa hadin kai da goyon bayan da hukumar ke bayarwa domin tabbatar da tsaron rayuka da dukiya, tare da inganta ayyukan ceto da agaji a jihar.
Aminiya ta ruwaito cewa, an horar da direbobin jiragen ruwan da za su riƙa kula da su, kafin a raba su zuwa ƙananan hukumomi goma (10) da suka fi fuskantar barazanar ambaliya da suka haɗa da: Goronyo, Shagari, Sabon-Birni, Wurno, Rabah, Wamakko, Silame, Kebbe, Tambuwal da Isa.
Gwamnan ya kuma yi gargaɗin cewa za a hukunta duk wani da ya ɗauki lodi fiye da ƙima a cikin jiragen, yana mai cewa “wannan jirage da rigar ruwa na jama’a ne, kuma wajibi ne shugabannin ƙananan hukumomi su tabbatar da kula da su yadda ya kamata.”
Sai dai wasu daga cikin mazauna yankunan da za a rabawa jiragen sun bayyana ra’ayinsu dangane da lamarin, inda wani Tanimu Goronyo, daga karamar hukumar Goronyo, ya ce: “Gwamnatin Sakkwato ta kauce hanya.
“Abin da muke bukata a yanzu shi ne hanyoyin mota da magudanan ruwa. Ambaliya tana mamaye yankunan mu ne saboda babu hanya. Idan gwamnati ta kashe wannan kuɗi wajen gina hanya, sai an fi cin moriya.”
Shi ma wani Muhammad Kabiru, daga Silame, ya bayyana farin cikinsa da sayen jiragen, sai dai ya roƙi gwamnati da ta mai da hankali wajen gina hanyoyin mota saboda abin da suka fi buƙata ke nan.
“Mu a Silame jirgi yana da amfani, amma hanyar mota ita ce babbar buƙatar mu. Idan aka samar da ita, ambaliya ba za ta hana mu zirga-zirga ba.”
Yayin da gwamnatin Sakkwato ke ɗaukar matakan gaggawa don rage hatsarurruka da ambaliya ke haifarwa, al’umma na ci gaba da neman tsarin da zai magance tushen matsalar – musamman samar da ingantattun hanyoyi da magudanan ruwa a karkara.