Kungiyar Tarayyar Afirka Ta Yi Tofin Allah Tsine Kan Shirin Korar Falasdinawa Daga Gaza
Published: 16th, February 2025 GMT
Kungiyar Tarayyar Afirka ta yi Allah Wadai da duk wani Shirin tilastawa Falasdinawa gudun hijira daga muhallinsu
Batun neman tilastawa Falasdinawa gudun hijira daga kasarsu ta gado yana ci gaba da fuskantar tofin Allah da Allah wadai a duk fadin duniya da kuma a taruka daban-daban, kuma batun Falasdinu shi ne kan gaba a ajandar taron kolin Afirka karo na 38 da aka yi a birnin Addis Ababa fadar mulkin kasar Habasha.
A yayin bude zaman taron kolin kungiyar tarayyar Afirka, shugaban hukumar Tarayyar Afirka, Moussa Faki, ya yi gargadi game da kiraye-kirayen da ake yi na tilastawa Faladinawa gudun hijira, yana mai jaddada cewa ci gaba da tauye wa Falasdinawa ‘yancinsu abin kunya ne ga bil’Adama, yana mai sukar shirun da kasashen duniya suka yi dangane da halin da ake ciki a Gaza da kuma jaddada ci gaba da goyon bayan kungiyar Tarayyar Afirka ga Falasdinawa. Shugaban Hukumar Tarayyar Afirka Moussa Faki ya ce: Sun ga yadda duniya ta yi shiru duk da wannan mummunan yanayi da al’ummar Gaza ke ciki, har ma wasu daga cikinsu na yin kira da a kori Falasdinawa daga muhallinsu, lamarin zai kara ta’azzara mummunan kangin da Falasdinawa suka shiga.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: a Falasdinawa
এছাড়াও পড়ুন:
EU Tace Zata Dakatar Da HKI Daga Cibiyar Bincikenta Saboda Gaza
Kungiyar tarayyar Turai tana shirin jingine aiki da HKI na wani lokacin, a cibiyoyin binciken ilmin da suke da su a nahiyar ta Turai saboda ayyukan kissan kare dangi da kuma hana abinci shiga gaza da take yi.
Tashar talabijan da Presstv a nan Tehran ta nakalto majiyar EU tana fadar haka, ta kuma kara da cewa kasashen turai sun gargadi HKI da ta daina hana abinci shiga gaza, amma ta yi taurine kai. Don haka a halin yanzu majalisar gudanar da na kungiyar tana shirin haramtawa HKI amfanina da wani bangare na ayyukan bincike na kasashen kungiyar, musamman wadanda suka shafi kirkirenren fasaha wato AI don kada ta yi amfani da su wajen yakar falasdinawa a gaza da ita.
Wannan shi ne karon farko wanda tarayyar Turai take daukan wani mataki, wanda shima bai taka kara ya karya ba, kan HKI.
Amma tun lokacinda aka fara yakin a ranar 7 ga watan Octoban shekara ta 2023 mafi yawan kasashen turai musamman kuma kasashen Jamus da Burtania suna goyon bayan HKI, suna kuma tallafa mata da makamai don ci gaba da kissan Falasdinawa a Gaza. A yanzu al-amarin ya kaiga duniya gaba daya ta tabbatar da cewa abinda HKI take yi a Gaza kisan kiyashi ne, sai suka ce bari su yi wani abu, wanda zai zama hajjace ta kare kansu idan an ce basu yi kome ba. Amma duk da haka kungiyar tarayyar Turai tana tare da HKI 100% kan kissan Falasdinawa a Gaza.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label Name* Email* Website Label Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Ma’aikatar Leken Asirin JMI Ta Ce Ta Gano Shirin Kashe Manyan Mutane 35 a kasar July 29, 2025 Najeriya: Likitoci a Lagas Sun Shiga Yajin Aiki July 29, 2025 Wani Dan Majalisar Iran Ya Yi Kira Ga A Yi Siyasar Kin Gabatar Da Bayanai A Tattaunawa Da Kasashen Turai July 29, 2025 Sojojin HKI Sun Ci Gaba Da Kashe Kawunansu July 29, 2025 Kasar Holland Ta Hana MInistocin HKI Biyu Shiga Cikin Kasarta July 29, 2025 Manjo Janar Musawi: Ko Kadan Ba Mu Yarda Da Amurka Ba July 29, 2025 Araqchi: Iran Zata Mayar Da Martanin Da Ba Zai Yiwu A Boye Ba Kan Duk Wani Harin Wuce Gona Da Iri Kanta July 29, 2025 Kasar Iran Ta Musanta Yin Katsalandan A Tattaunawar Neman Tsagaita Bude Wuta A Gaza July 29, 2025 Rasha Ta Mayar Da Martani Ga Shugaban Amurka Kan Gindaya Wa’adin Kawo Karshen Yakin Ukraine July 29, 2025 Kasar Faransa Ta Yi Allah Wadai Da Harin Ta’addancin Da Aka Kai Birnin Zahedan Na Kasar Iran July 29, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci