Duniyarmu A Yau: Wasikar Lawyoyi 800 Ga Firay Ministan Kasar Burtaniya Kan Gaza
Published: 29th, May 2025 GMT
Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake dasuwa a cikin shirimmu na duniyarmu a yau shiri wanda yake kawo maku labarai masu muhimmaci a makon da ya gabata, wanda suka shafi siyasa tattalin arziki zamnatakewa tsaro da sauransu. Inda muka yi masu karin bayani sannan mu ji ra’ayin masana dangane da su da fatan masu sauraro zasu kasance tare da mu a cikin wannan shirin.
///…Masu sauraro shirimmu na yau zai yi magana dangane da zaben majalisun dukoki na kasa da kuma larduna a kudancin kasar Lebanon inda kungiyar Hizbullah da kuma Amal ta mabiyan mazhabar iyalan gidan manzon All..suka fi rinjaye. Inda zamu ga yadda Hizbullah ta lashe dukkan bazabun da yakamata ta lashe haka ma kungiyar Amal.
Idan akwai lokaci zamu dubi yadda ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya mayarwa shugaban kasar Faransa martani kan yadda yake amfani da sunan kare hakkin bil’adama don dushe hasken Iran a gasar fina-finai ta Hannes da aka kammala. Da fatan masu sauraro zasu kasance tare da mu.
Kamfanin dillancin labaran Parstoday na kasar Iran ya nakalto wani mai sharhin labaran siyasa na kasar Lebanon na fadar cewa, sakamakon zaben yan majalisar dokoki ta kasa da kuma na larduna da aka gudanar a kudancin kasar Lebanon abin kungiya ne kuma gazawa ce ga HKI da Amurka a kudancin kasar Lebanon, don sakamakon zaben ya nuna cewa kungiyar Hizbullah da kuma Amal suna da karfinsu a yankin kuma kokarinda HKI da Amurka suka yi sayan wasu yan takaran don suyi masu aiki a wadannan majalisu basu kai labara ba.
Sakamakon zaben ta nuna cewa haryanzun kungiyar Hizbullah tana da karfi don yan takaranta ne suka lashe dukkan kujerun da ake son cikewa a zaben, na majalisar kasa ko na larduna.
A ranar Asabar 24 ga watan Mayu ne aka gudanar da zaben larduna da kuma na majalisar dokokin kasa a kudancin kasar Lebanon wanda shi ne na hudu kuma na karshe a kasar. An gudanar da zabubbukan ne a yankunan Chaqra, Joya, Aitaroun, da kuma Nabatieh a lardunan kudanci da Nabatieh na kasar ta Lebanon.
Nasser Nasser al-Din wani mai sharhin labaran siyasa a tashar talabijin ta Al-Alam dake nan birnin Tehran ya bayyana cewa, sakamakon zaben ya bayyana irin majalisar dokokin da za’a samar a kasar nan gaba. Wanda zai shafi yadda za’a kafa gwamnati a kasar da kuma majalisar ministoci. Mai yuwa har da zaben shugaban kasa. Har’ila yau sakamakon zai yi tasiri a majalisar idan wani wakilin HKI ya gabatar da wani abu na bukatar HKI a cikin kasar Lebanon. Don duk wani kuduri ko bukatar da aka gabatar a majalisar wanda wakilan Hizbullah da kuma Amal basu yard aba, bukatar ba zata wuce ba.
Nasser Nasser al-Din ya bayyana a cewa a zaben da ua gabata, ofisoshin jakadancin kasashen da dama a kasar Lebanon sun dauki nauyin yan siya wadanda suka yarda su yi masu aiki a cikin majalisar idan ci zabe, daga cikinsu har da ofishin jakadancin Amurka wacce ta kulla yarjeniyar da wasu yan siyasan kasar Lebanon kan cewa zasu yi mata aiki a cikin majalisar dokokin kasar ta Lebanon idan sun ci zabe. Amma dukkan wadannan ya takara basu sami nasara ba duk tare da kudaden da wadannan kasashe suka basu. Saboda mutane suke zaba, su kuma ba’a sayansu da kudi, ko yaudara. Sun san abinda ya dace su yi , sun san wadanda zasu zaba.
Ya kara da cewa tare da wannan goyon bayan, hatta bayan shahadar Sayyid Hassan Nasarallah, da kuma zaben sheikh Na’em Kasim kungiyar ta sake fardadowa don fuskantar duk wani kokarinda HKI zata yin a sake mamayar kasar Lebanon.
Mutanen kasar Lebanon sun san cewa gwamnatin kasar Amurka yar yaudare ce, ba abin amincewa bane. Kamar yadda a cikin yan kwanakin da suka gabata tana yin kira ga gwamnatin kasar Lebanon ta yi kokarin tabbatar da doka da order a kasar, amma a dayan bangaren kuma ba zaka taba jin tana allawadai da HKI kan hare-haren keta yarjeniyar sulhu da ta cimma da kungiyar Hizbullah ba. Mai lamba 1701 ba. Tun lokacin sulhun ya zuwa yanzu HKI ta keta yarjeniyar har fiye da 3000 a kudancin kasar Lebanon, kuma da ta san cewa mayakan Hizbullah ba zasu iya tareta ba da ta yi kokarin sake kutsawa cikin kasar Lebanon. Amma tasan kungiyar tana a madakata.
Don haka ko a yanzun idan tana ganin zata kutsa cikin kasar Lebanon ba tare da wani wanda zai tare ta ba da tayi. Don haka dole ne mu yi hattara mu kuma cikin shiri dare da rana.
Nasser Nasser al-Din ya ce, a shekarum baya kungiyar Hizbullah ta kare kauyun kiristocin kasar Lebanon daga yan ta’adda wadanda suke samun goyon bayan HKI da Amurka a kan iyakokin Siriya. A lokacin dakarun hizbullah sun kare kauyukan kiristoci da suke yankin daga yan ta’addan. Don haka kiristoci a wadannan yankuna da suke kan iyaka da kasar siriya sun hada kansu a wannan zaben don tabbatar da cewa kungiyar Hizbullah ta ci gaba da kasancewa cikin karfinta a siyasa da kuma karfin soje.
Don haka akwai kiristoci da dama wadanda suke goyon bayan kungiyar Hizbullah a wannan zaben. Sannan mutanen kasar Lebanon gaba daya sun san irin nasarorin da kungiyar Hizbullah ta samu a kan sojojin HKI shekaru 25, inda suka kore yahudawan daga kasar Lebanon sannan yake-yake guda biyu da suka gabata, wato a shekara ta 2006 da kuma shekara ta 2024 sojojin yahudawan sun yi kokarin sake mamayar kasar Lebanon amma dakarun Hizbullah sun zama katangar karfe wacce ta hana yahudawan sake komawa cikin kasar Lebanon.
Don haka a fadin shugaban masu gwagwarmaya, kuma shahid Sayyid Hassan Nasarallah, makaman hizbullah, a ko yauce dole su kasance cikin shiri, don kare kasa daga HKI, su kuma kasance tare da sojojin kasar ta Lebanon.
A wani labarin kuma lawyoyi fiye da 800 suka sanya hannu kan wata takarda ta tilastawa gwamnatin kasar Burtaniya ta dorawa HKI takunkuman tattalin arziki saboda kissan kiyashin da take aikatawa a Gaza.
Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta bayyana, cewa a wata wasika wacce ta yi kamada mai tilastawa Firai ministan kasar Burtaniya, Keir Starmer, wacce kuma fitattun lawyoyi a kasar suka sanyawa hannu, daga ciki har da tsoffin, alkalai ta bukaci, a sanyawa HKI takunkuman tattalin arziki da gaggawa, don hana kissan kiyashin da take aikatawa a Gaza saboda kuma kiyaye dokokin kasa da kasa.
Lawyoyin sun bukaci wannan takunkuman ne saboda yadda suka damu da hannu dumu dumu wanda kasar Burtaniya take da shi a cikin kisan kiyashin da HKI take aikatawa a Gaza, inda suke nuna bukatar kula da dokokin kasa da kasa wacce ta haramta yin hakan da kuma taimakawa duk wata kasa da take hakan.
A cikin wasikar lawyoyin sun tabbatar da cewa , gwamnatin kasar Burtania ta kasa yin kome, a cikin kissan mutane akalla 53,000 wadanda HKI ta kashe a zirin Gaza a cikin shekara daya da rabin da suka gabata. Banda ma haka kasar Burtaniya tana goyon bayan HKI a wannan babban laifi wanda bai bukatar zuwa kotu don tabbatar da laifin HKI a cikinsa. Sun ce yin shiru ko rashin daukar mataki ya nuna cewa gwamnatin kasar Burtaniya tana zagon kasa ga dokokin sharia na kasa da kasa kuma tana taimakawa wajen habaka aikata laifi a fagen kasa da kasa.
Lawyoyin sun kara da cewa dole ne gwamnatin kasar burtania ta dorawa dukkan ministocin HKI takunkuman tattalin arziki sannan tayi maganar korarta daga MDD don ta kare dokokin kasa da ka na asali.
Wasikar ta kara da cewa akwai shaidu ba su da iyaka wadanda suka tabbatar da cewa HKI ta aikata laifukan yaki, a kissan kiyashin da ke faruwa a gaza, daga ciki harda fadin ministan kudi na HKI Bezalel Smotrich kan cewa zasu shefe al-ummar falasdinu a Gaza.
Lawyoyin sun fadawa Stammer kan cewa wajibi ne a kan kasashen duniya gaba daya, daga ciki har da kasar Burtaniya, da su dauki dukkan matakan da zasu iya, don hana kissan kiyashi, sannan su hukunta wanda yayi hakan, amma abinda gwamnatin kasar Burtania , ya zuwa yanki ta kasa aikata wani abu wanda ya yi dai-dai da abinda dokokin kasa da kasa suka bukaci ta yi.
Sun kammala da cewa, gazawar kasashen duniya wajen tabbaka dokokin kasa da kasa irin wannan, kan HKI da kuma abinda ya shafi hakkin Falasdinuwa a gaza, hakan zai taimaka wajen wargajewar tsarin zamantakewa a duniya gaba daya, kuma yin burus da wadannan dokoki, bude kofa ne ga zama babu tsare, ko kuma abinda ake kira dokar daji, inda mai karfi yana cinya marasa karfi. Wanda kuma zai rushe dukkan dokokin kasa da kasa da muke da su. Daga karshe suka bayyana cewa, dole ne gwamnatinka ta fara aiki kan haka a yanzu, kafin lokaci ya kure.
Wannan ake ta tarjamar ko kama da tarjamar wasikar da lawyoyi fiye da 800 a kasar Burtaniya, wadanda suka hada da tsoffin alkalai wadanda suka yi ritaya da al0kalai da babban kotuna da alkalai masu ci a yanzu, suka rubutawa firai ministan kasar Burtania Keir Starmer, dangane da abinda ke faruwa a zirin gaza na kasar Falasdinu da aka mamaye. Inda suka bukaci, dakatar da yaki da gaggawa, a kuma maida ayyukan bada agaji na gaggawa, burtaniya ta dakatar da harkokin kasuwanci a HKI.
Lawyoyin sun bayyana cewa wannan dan karamin takunkuma da suka dorawa HKI bai wadatar ba.
Sannan sun bayyan cewa zaman lafiya fa ba zata samu ba a duk fadin duniya ba tare da kwatanta a dalci.
Sai dai masana wadanda sukan kasan kasar Burtaniya suka kuma san kasashen yamma sun sann cewa gwamnatin kasar Burtaniya ba zata iya aiwatar da abinwa wadannan lawyoyi suke bukata ba, ba don kome ba, wadannan kasashen yamma, musamman kasar Burtraniya ita ce ta kafa HKI tun farko, a shekara ta 1948. Kuma kowa ya sani tun randa aka kafa HKI tana kissan kisan kiyashi iran wanda suke aikatawa a Gaza, ta shiga yake da kasashen larabawa sau da dama, wadannan kasashen musamman Amurka suke suke taimakawa HKI kan wadannan kasashe. Ta yaya zasu aiwatar da abinda ya cikin wannan kasikar al-hali su ne kashin bayan kafuwar HKI?
Don haka wadannan kasashen yamma sun kai matsayinda ba zasu iya dawowa su rabu da HKI don su suka kafata shekaru fiye da 75 da suka gabata. Don haka duk abinda zai faru da HKI nan gaba kan abinda take aikatawa a Gaza sai ya samesu suma.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: a kudancin kasar Lebanon a cikin kasar Lebanon kungiyar Hizbullah ta take aikatawa a Gaza kasar Burtaniya ta a kasar Burtaniya tattalin arziki gwamnatin kasar wadanda suka masu sauraro kiyashin da goyon bayan a majalisar tabbatar da
এছাড়াও পড়ুন:
Shugaban Kasar Iran Ya Kai Ziyara Zuwa Kasar Oman don Karfafa Kyakkyawar Alakar Kasashen Biyu
Kafin tashinsa zuwa kasar Oman shugaban kasar Iran ya bayyana cewa: Suna neman kyakkyawar dangantaka da maƙwabtansu
Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya tabbatar kafin ya tashi daga filin tashi da saukar jiragen sama na birnin Tehran zuwa birnin Muscat a yammacin yau Talata cewa: Makasudin ziyarar tasa zuwa kasar Oman ita ce kulla kyakkyawar alaka da kasashe makwabta, kuma alaka tsakaninsu tana bunkasa kowace rana.
Shugaba Pezeshkian da yake zantawa da manema labarai a filin tashi da saukar jiragen sama na Mehrabad ya bayyana cewa: A halin yanzu yawan ciniki tsakanin Iran da Oman ya kai dalar Amurka biliyan 2.3, yana mai jaddada bukatar ci gaba da karfafa dangantakar dake tsakanin kasashen biyu.
Shugaba Pezeshkian ya ce: Zai gudanar da wannan ziyara ce bisa gayyatar da Sultan Haitham bin Tariq Al Said ya yi masa a hukumance, kuma bisa ga dukkanin manufofin gwamnati da Jagoran juyin juya halin Musulunci, manufar wannan ziyara ita ce kulla alaka mai zurfi da kyakykyawan dangantaka da kasashen makwabta ciki har da masarautar Oman, haka kuma an shirya fadada dangantakar Jamhuriyar Musulunci ta Iran a dukkanin bangarori na siyasa da tattalin arziki da zamantakewa.