Kazalika, tashar teku ta Duisburg dake kasar Jamus ta kasance cibiyar sufurin layin dogo a tsakanin Sin da yammacin Turai, inda yawan kwantenonin da ake hada-hadarsu a tashar duk shekara suka kai miliyan hudu. Bugu da kari, sufurin layin dogo da ya sada Sin da Turai ya kara bude hanyoyin zuba jarin kamfanonin Sinawa a Duisburg.

Sannan ana ci gaba da inganta sufurin dogo ta hanyar sabbin tsare-tsaren da ake kawowa kamar su na jirgin Tea Train da na dakon motocin sabbin makamashi da ake fitarwa zuwa waje, watau New Energy Vehicle Export Train, domin raya cinikayyar Sin da Turai.

Har ila yau, layin dogo na Budapest zuwa Belgrade da ya sada kasashen Serbia da Hungary mai kusan tsawon kilomita 350 a karkashin kawancen BRI wani sabon yunkuri ne na cimma muradun kasar Sin da yankin Turai a kan amfani da makamashi mai tsafta a karkashin kawancen na BRI.

Akwai kuma karin kamfanonin Sin dake aikin inganta amfani da makamashi mai tsafta a tashar tekun Piraeus ta kasar Girka, kana a yankin kudu maso gabashin kasar Malta, kauyen kamun kifi na Marsaxlokk da ya sha fama da matsalar gurbacewar yanayi sakamakon gina tashar lantarki tun a farko-farkon shekarun 1990, a halin yanzu ya samu waraka tun bayan da wani kamfanin Sin ya gyara tashar tare da jan ragamar tafiyar da ita, inda aka samu raguwar hayaki mai gurbata muhalli da ake fitarwa. Duka wadannan misalai, suna nuna yadda kawancen Sin da yankin Turai ke kara armashi da kuma kawo haske ga tattalin arziki. (Abdulrazaq Yahuza Jere)

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Ana Iya Samun Masu Samar Da Kayayyaki Iri-Iri Cikin Awa Daya A Kasar Sin

“Ba kawai girma tsarin samar da kayayyaki na kasar Sin yake da shi ba, har ma ya hade dukkanin fannoni, tare da amsawa da sauri kwarai da gaske.”

“Daga kulla kwangila zuwa samun wurin gudanarwar ayyuka bai wuce watanni 3 ba, lamarin da ya ba mu mamaki sosai!”

A ranar 20 ga wata, an rufe bikin baje kolin samar da kayayyaki na kasa da kasa karo na uku a birnin Beijing. A yayin bikin na wannan karo, kamfanonin kasashen ketare da suka hada da Honeywell, da Louis Dreyfus, da Corning, da kuma Wacker Chemie AG da dai sauransu, sun jinjinawa tsarin samar da kayayyaki na kasar Sin mai inganci. Sun ce, za su ci gaba da raya ayyukansu a kasar Sin, tare da hada kai da kasar Sin da ma sauran baki ’yan kasuwa wajen kyautata tsarin samar da kayayyaki na duniya. (Mai Fassara: Maryam Yang)

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Al’ummar Fegin Mahe Sun Yi Zanga-zanga Kan Kisan Jama’a Da ‘Yan Bindiga Ke Yi
  •  Fiye Da  Kungiyoyin 100 A Duniya Sun Yi Gargadi Akan Halin Yunwa Da HKi Ta Jefa Mutanen Gaza A Ciki
  • Yahudawan Sahayoniyya Sun Bullo Da Dabarar Kisa Kan Falasdinawa Musamman ‘Yan Gudun Hijira
  • Shugaban Amurka Trump Ya Bukaci Gurfanar Da Tsohon Shugaban Amurka Barack Obama A gaban Kuliya
  • Pezeshkian: Tunanin Kawo Karshen Shirin Nukiliyar Iran Ya Yi Kama Da Tabuwa
  • Taron Kolin Sin Da EU Zai Bayar Da Damar Zurfafa Hadin Gwiwar Sassan Biyu
  • Kasar Sin Na Fatan EU Za Ta Yi Aiki Da Ita Bisa Alkibla Guda Da Tsara Hadin Gwiwa Na Shekaru 50 Masu Zuwa
  • Ana Iya Samun Masu Samar Da Kayayyaki Iri-Iri Cikin Awa Daya A Kasar Sin
  • Gwamnatin Zamfara Ta Kira Babban Taron Tsaro Tare Da Bayyana Sabbin Dabaru Na Yakar ‘Yan Bindiga.
  • Ministocin Tsaron kasashen Rasha Da JMI Sun Hadu A Birnin Mosco