HausaTv:
2025-07-26@08:48:29 GMT

Ruwa Kamar Da Bakin Kwarya Ya Ci Rayukan Mutane 25 A Jihar Rivers

Published: 30th, May 2025 GMT

 Mamakon ruwan sama da ya sauka a jihar Rivers ta Najeriya ya yi gyara, tare da daukar rayukan mutane 25,kamar yadda hukumar agajin gaggawa ta kasar ta sanar.

Ruwan da ya sauka a garin Okrika ya haddasa zaizayar kasa,wacce ta binne gidaje da dama, da kuma yin awon gaba da mutane.

Masu ayyukan ceto sun ce har yanzu ana ci gaba da gano gawawwakin mutane a karkashin baraguzai.

Haka nan kuma mutane da dama sun rasa matsugunansu.

Duk da cewa ana ci gaba da ayyukan ceto said ai har yanzu da akwai yankuna da ba za a iya shiga cikinsu ba saboda sun yi lungu.

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

Anacláudia Rossbach: Ya Kamata Kasashen Afirka Su Koyi Darasi Daga Sin Na Kawar Da Talauci Da Kyautata Kauyuka Zuwa Birane

Kwanan nan, darektar zartaswa ta hukumar kula da matsugunan dan Adam ta MDD, Anacláudia Rossbach, ta yi hira da wakilin babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na Sin wato CMG, a hedkwatar hukumar kula da matsugunan dan Adam ta MDD dake Nairobi, babban birnin Kenya.

Yayin da aka ambato sakamakon da ya fi jawo hankali da Sin ta samu yayin kyautata kauyuka zuwa matsayin birane da garuruwa, Rossbach ta bayyana cewa, Sin ta cimma nasarar kawar da talauci ga mutane miliyan 800, da kuma tafiya a kan hanyar kyautata kauyuka zuwa birane da garuruwa, kuma wannan darasi ne da ya cancanci kasashen Afirka wadanda suke fuskantar kalubalen kyautata kauyuka zuwa birane su yi koyi da shi.

Ta ce, nan da shekaru 25 masu zuwa, mutane kusan miliayn 800 na kasashen Afirka da na Latin Amurka za su yi kaura zuwa birane, kuma kasashen Asiya da dama su ma suna fuskantar kalubalen fama da talauci. A cewarta, birane na da muhimmanci sosai wajen kawar da talauci, kuma ba ma kawai ya kamata a ba da wurin kwana ga mutane a cikin birane ba, har ma ya dace a ba su damammakin samun ilmi, da guraben ayyukan yi da sauransu, da kuma samun hidimomin kiwon lafiya don kiyaye koshin lafiyarsu, kana ta ce, wannan shi ne muhimmin abun da za mu ci gaba da gudanarwa da kuma tattaunawa a kai. (Safiyah Ma)

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Mutanen A Netherlands Suna Zaman Dirshen Saboda Gaza
  • An kai hari a ƙauyuka uku da kashe mutum 7 a Imo
  • ‘Yan Tawayen Sudan Ta Kungiyar Rapid Support Forces Sun Kashe Mutane 27 A Yammacin Jihar Kordofan Ta Kasar Sudan
  • Syria: Mutane Da Dama Sun Mutu Da Kuma Jikkata Sanadiyyar Gobara A Rumbun Ajiyar Makamai
  • Anacláudia Rossbach: Ya Kamata Kasashen Afirka Su Koyi Darasi Daga Sin Na Kawar Da Talauci Da Kyautata Kauyuka Zuwa Birane
  • Ruwa da iska sun kashe mutum 5, sun raba sama da 5,000 da muhallansu a Yobe
  • Ruwa da iska sun kashe mutum, sun raba sama da 5,000 da muhallansu a Yobe
  • Masu Zuba Jari Na Kasa Da Kasa Sun Gamsu Zuba Jari A Sin Dama Ce Ta Cimma Nasarar More Riba A Nan Gaba
  • Cutar Amai Da Gudawa Ta Hallaka Mutane 13 A Neja
  • Tursasawa Kasashen Afirka Karbar Bakin Haure Daga Amerika Kuskure Ne