Gwamnati Ta Taya Tinubu Murna Kan Goyon Bayan Da Ya Samu Don Komawa Takara
Published: 25th, May 2025 GMT
Daga Bello Wakili
Mataimaki na Musamman ga Shugaban Kasa kan Harkokin Yada Labarai da Ayyuka na Musamman, Mista Tunde Rahman, ya bayyana jerin goyon bayan da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ke samu daga cikin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a matsayin shaida mai karfi kan tsare-tsaren da gwamnati ta aiwatar cikin shekaru biyu da suka gabata.
A yayin wata tattaunawa da ya yi da Radio Nigeria a Abuja, Mista Rahman ya ce goyon bayan da ke fitowa daga gwamnoni na APC, ‘yan majalisar dokoki da shugabannin jam’iyya, na nuna karuwar amincewa da sauye-sauyen tattalin arzikin da Shugaba Tinubu ya aiwatar. Ya ce wannan ya hada da cire tallafin fetur da daidaita farashin canjin kudade.
“Wadannan goyon bayan suna da matukar muhimmanci. Su ne jinjina ga jarumtaka da kwarin gwiwar Shugaban kasa, musamman wajen daukar matakai masu wahala tun farkon wa’adinsa, kamar cire tallafin man fetur a ranar 29 ga Mayu, 2023,” in ji shi.
A cewarsa, tasirin wadannan matakai ya fara haifar da sakamako mai kyau, ciki har da farfadowar tattalin arziki, saukin darajar Naira da kuma dan saukin farashin kayan abinci.
Ya kara da cewa shugabannin jam’iyya da mambobinta sun fahimci amfanin wadannan tsare-tsare, shi ya sa suke marawa Shugaban kasa baya.
Da aka tambaye shi ko wannan amincewar baiyi wuri ba alhali sauran kusan shekaru biyu kafin zabe, Mista Rahman ya ce hakan ba sabon abu ba ne a siyasar Najeriya, domin har jam’iyyun adawa sun riga sun fara shirin tunkarar zabe.
“Baiyi wuri ba. APC na mayar da martani ne ga abubuwan da ke faruwa a siyasa. Abin da ke faruwa yanzu wani nau’in tantancewa ce ta wa’adin gwamnati,” in ji shi.
Mista Rahman ya kuma ambaci sauya shekar gwamnan Jihar Delta zuwa APC tare da wasu daga cikin mambobin majalisar dokoki da masu rike da mukamai a gwamnatinsa a matsayin karin hujjar karuwar goyon bayan da Shugaba Tinubu ke samu.
Ya kammala da cewa a yi tsammanin karin goyon baya da sauya sheka daga gun wainda ba yan jamiyar APC ba nan gaba kadan yayin da gwamnatin ke ci gaba da nuna nasara da kwanciyar hankali a kasar.
BELLO WAKILI
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Goyon Bayan Takara goyon bayan da
এছাড়াও পড়ুন:
Sojoji Sun Kashe Ƴan Boko Haram 16 A Borno Bayan Sun Kawo Hari Barikinsu
Mataimakin Daraktan Ayyuka na Operation Haɗin Kai, Kyaftin Reuben Kovangiya, ya tabbatar da kashe ‘yan ta’addan, yana mai cewa Sojojin na ci gaba da kai hare-hare kan ‘yan ta’addan.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp