Ahmed Musa Ya Angwance Da Matarsa Ta 4 A Kano
Published: 31st, May 2025 GMT
Kyaftin din tawagar Super Eagles ta Nijeriya Ahmed Musa, ya auri matarsa ta 4, Asmau Moriki, a wani biki na sirri da aka gudanar a jihar Kano, Musa da amaryarshi Asmau sun zama mata da miji watanni kadan bayan haduwarsu, Musa ya bar sansanin tawagar Super Eagles dake birnin Landan domin ya halarci bikin wanda aka gudanar a birnin Kano.
Dan wasan dake taka leda a kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars, ya shiga wasan da Nijeriya ta doke Ghana da ci 2-1 a minti 60 na wasan, Musa na daya daga cikin yan wasan da sukafi taka leda a tarihin tawagar kwallon kafa ta Nijeriya inda kuma ya zamo wanda yafi jefawa Nijeriya kwallaye a gasar kofin Duniya a tarihinta.
Kamfanoni Masu Jarin Waje Sun Ci Gajiyar Tsarin Kasar Sin Na Samar Da Rangwamen Gwamnati Ta Musayar Sabbin Kayayyaki Da Tsofaffi Trump Zai Shirya Liyafar Musamman Ga Manyan Ƴan CryptoMusa ya yi aurenshi na farko a shekarar 2013 inda ya auri Jamila, ma’auratan, wadanda suka haifi ‘ya’ya biyu sun rabu a shekarar 2017 bayan wata hatsaniya ta ma’aurata wadda ake alakantawa da burin da Musa kedashi na kara aure ya shiga tsakaninsu a wancan lokacin, jim kadan bayan rabuwar, ya auri Juliet Ejue, matar sa ta biyu, daga Ogoja a jihar Kuros Riba.
Har wayau aurensu da Juliet ya rabu duk da cewa ba a san takamaiman dalili ko lokacinda auren ya rabu ba, a shekarar 2021, ya auri Mariam wadda ita ce ta zama matarsa ta uku, sai yanzu kuma a ranar 30 ga watan Mayun 2025 aka daura auren Musa da Asmau Moriki wanda ya kasance aure na hudu da aka san tauraron dan wasan yayi, rahotanni sun bayyana cewa an gudanar da daurin auren cikin kwanciyar hankali a Kano kuma ya samu halartar ‘yan uwa da abokan arziki.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
A tsananta hukunci kan masu dukan mata — Sarki Sanusi
Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II, ya yi kira da a tsananta hukunci kan masu cin zarafin ’ya’ya mata, yana mai cewa babu wani musulmi nagari da zai yi wa matarsa dukan da har zai yi mata lahani.
A yayin da yake tunatar da malamai da limamai kan muhimmiyar gudunmawar da za su bayar a wannan fage domin yi wa tufkar hanci, Sarkin ya bayyana damuwa kan yadda matsalolin fyade da kuma samun magidantan da ke dukan matansu suka zama ruwan dare a Jihar Kano.
Yunwa na ƙara tsanani a Arewa maso Gabashin Nijeriya — ICRC Mutum 16 sun mutu a haɗarin jirgin sama a BangladeshSarki Sanusi na wannan furuci yayin da ya karbi bakuncin tawagar cibiyar bunkasa bincike (dRPC) da kuma cibiyar nazarin addinin musulunci ta Jami’ar Bayero da ke Kano (CCID) suka kai ziyara fadarsa ta Gidan Rumfa a birnin Dabo.
A cewar Sarkin, “ban zan taba goyon dukan mace ba, kuma duk masu yi, suna yi ba da niyyar ladabtarwa ba. Amma abin takaicin da muke gani a yau shi ne yadda ake yi wa mata jina-jina da sunan ladabtarwa.
“Musulunci yana fifita mata da daraja fiye da kowane addini kuma duk masu neman fakewa a karkashinsa don cin zarafinsu, ba su ma fahimci addinin ba.
“Duk wanda yake dukan matarsa har ya yi mata rauni ba mutumin kirki ba ne, kuma ba ni na fadi haka ba, Annabi Muhammad (SAW) ne ya fada, wadanda ba su karanta ba ne ba su sani ba.”