Leadership News Hausa:
2025-09-18@02:11:05 GMT

GORON JUMA’A 30-03-2025

Published: 30th, May 2025 GMT

GORON JUMA’A 30-03-2025

Sako daga Bilal Salisu Gabasawa:

Ina so a mikan sakon gaiswa ta zuwa ga masoyiya Habiba, abar kaunata in sha Allah har karshen rayuwa, da fatan ta yi juma’a lafiya.

Sako daga Suwaiba Lawan Jihar Kano:

Ina so a gaishe mun da mahaifana da kuma.mijina uban ‘ya’yana daya tamkar ya dubu rabin raina Nasir Muhd, Allah ya sa sakon ya isa gare shi, ina yi muku fatan alkhairi.

Sako daga Abba Ahmad Kaduna:

Ina gaishe da mahaifina da kuma mahaifiya ta, ina gaishe da kannena; Momi, ikram, sadiya, hafsa, sadik, sannan ina gaishe da duk kanin al’ummar musulmi bakidaya, Allah ya sa mu yi juma’a lafiya.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Karamar Hukumar Malam Madori Ta Horar Da Mata Kare Kai Daga Cututtukan Mahaifa

A ƙoƙarinta na  ƙara wayar da kan jama’a game da harkokin lafiya a birane da karkara na Malam Madori, majalisar ƙaramar hukumar ta horar da mata da ‘yan mata 50 kan tsafta a lokutan al’ada domin kare kansu daga cututtukan mahaifa.

Jami’in shirin, Malam Ali Haruna, ya ce an zaɓi mahalarta horon ne daga kowace gunduma ta yankin

A cewarsa, manufar horon ita ce koyar da mahalarta yadda za su samar da kariya yayin al’ada da kansu domin rage kashe kuɗi da kuma kare kansu daga kamuwa da cututtukan mahaifa.

Shi ma shugaban sashen ruwa da tsafta, Malam Shehu Sani Gwadayi, ya bayyana cewa tsafta na da matuƙar muhimmanci ga rayuwar ɗan adam domin inganta rayuwa da ƙarfafa garkuwar jiki.

A nasa jawabin, mataimakin shugaban sashen ruwa da tsafta, Malam Muhammad Abdullahi, ya yi wa mahalarta horon bayani kan muhimmancin tsafta yayin al’ada domin gujewa kamuwa da cututtuka.

Shugaban ƙaramar hukumar Malam Madori, Alhaji Salisu Sani Garun Gabas, ya shawarci mahalarta da su mai da hankali ga sashen aikace-aikace na yadda ake sarrafa audugar mata a gida yayin horon.

 

Usman Muhammad Zaria

 

 

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Karamar Hukumar Malam Madori Ta Horar Da Mata Kare Kai Daga Cututtukan Mahaifa
  • UNICEF Ya Ba Da Tallafin Kayayyakin Aiki Ga Cibiyoyin Lafiya A Kirikasamma
  • Al’ajabi: Yadda Aka Shirya Bikin Haihuwar ‘Ya’yan Awaki Biyar A Garin Dakasoye
  • Tinubu ya janye dokar ta-ɓaci da ya sanya a Ribas
  • Gwamnati ta fara duba yara marasa galihu kyauta a asibitin Aminu Kano
  • Baqa’i: Kowace Kasa A Duniya Tana Da Hakkin Mallakar Makamashin Nukiliya Na Zaman Lafiya
  • Taron Doha: Daga matakin Allawadai zuwa matakan kalubalantar laifukan Isra’ila
  • ’Yan sanda sun sasanta rikicin asibitin AKTH da KEDCO
  • KEDCO ya ƙaryata asibitin AKTH kan mutuwar majinyata saboda ɗauke wuta
  • Jami’in Kasar Yemen Ya Aike Da Sako Ga Mahalarta Taron Birnin Doha Na Kasar Qatar