An Gudanar Da Dandalin Kawancen Birane Na Kasa Da Kasa Na Shanghai
Published: 30th, May 2025 GMT
A yau Alhamis ne aka gudanar da dandalin “Kasa da kasa na tattaunawa tsakanin magadan biranen duniya na Shanghai, da dandalin kawancen birane na kasa da kasa na Shanghai na shekarar 2025.”
Magadan birane da wakilai daga birane 26 dake cikin kawancen, daga sassan kasashen duniya 22, sun hallara a bakin kogin Huangpu, domin tattaunawa, da musaya game da yanayin makomar birane a nan gaba, da hadin gwiwa, inda suka mayar da hankali kan “Bunkasa birane masu korayen itatuwa, da karancin fitar da iskar carbon, da ci gaba da kirkire-kirkire”.
Kazalika a yau din, birnin Shanghai ya sanya hannu kan takardun bunkasa kawance da musaya tare da Tbilisi na Georgia, da Vientiane na Laos da sauransu. A shekarun baya bayan nan, biranen kasa da kasa dake shiga kawance da birnin Shanghai na ta karuwa. Inda ya zuwa yanzu, birnin ya gina kawance tare da birane 95 na kasashe 59 dake fadin duniya. (Mai fassara: Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Jami’an Kasashen Rasha, China, Iran Sun Gudanar Da Taron Hadin Gwiwa A Tehran
Kasashen Iran, Rasha, da China sun gudanar da wani taro a birnin Tehran, inda suka tattauna batutuwan da suka shafi Shirin Iran na nukiliya da kuma dage takunkumin da aka kakaba mata.
Taron kasashen ya tabbatar da aniyarsu ta ci gaba da yin hadin gwiwa da tuntubar juna a cikin lokuta masu zuwa.
Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya bayar da rahoton cewa, a wannan Talata 22 ga watan Yuli 2025, aka gudanar da taron tawagogin kasashen uku.
Mahalarta taron a karkashin inuwar ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran, sun tabbatar da aniyar kasashensu na ci gaba da yin hadin gwiwa tare da yin musayar ra’ayi kan batutuwan da suka shafi yarjejeniyar nukiliyar.
Sun kuma jaddada muhimmancin ci gaba da wannan shawarwari domin biyan muradun kasashen uku wajen tinkarar manufofin kasashen yamma, musamman takunkuman Amurka.
Tawagogin sun amince su ci gaba da bude hanyoyin karfafa alakokinsu da kuma ci gaba da gudanar da taruka a nan gaba a matakai daban-daban a cikin makonni masu zuwa, a wani bangare na abin da suka bayyana da “kokarin hadin gwiwa na tallafawa zaman lafiyar yankin da inganta hadin gwiwa bisa manyan tsare-tsare.”