2025-07-07@19:17:14 GMT
إجمالي نتائج البحث: 5367
«madatsun ruwa»:
Wannan lamari ya buɗe sabon shafi a siyasar ƙasar nan, inda ƴan adawa suke ci gaba da cewa zuwan sabuwar jam’iyyar wani sauyi ne da za a samu a cikin ƙasar. Wani mai sharhi a kan siyasa, Sani Kabo, ya bayyana abin da ya samu shafin yanar gizon jam’iyyar a matsayin wata ƴar manuniya ga irin buƙatar da ake da ita wajen sauya sheƙa da kuma haɗin kan ƴan adawa, inda ya misalta abin da yake faruwa da shekara ta 2013, lokacin da aka samar da jam’iyyar APC wadda ta kawo karshen mulkin jam’iyyar PDP a wancan lokaci. Shima wani masanin siyasa a Nijeriya wanda ya buƙaci a sakaya sunansa ya ce wannan ya nuna yadda al’ummar ƙasar suke buƙatar...
Kananan yara uku sun rasu yayin da wasu da shidan ke kwance a asibiti sakamakon sake bullar cutar nan ta mashako a garin Zariya da ke Jihar Kaduna. Wani mazaunin unguwar Kwarbai a yankin na Zariya, Mallam Bashir Magaji wanda ya rasa ’yarsa sakamakon barkewar cutar wadda a turance ake kira Diphtheria, ya bayyana yadda take bazuwa cikin sauri a kwanakin nan. Kira ga Haƙuri: A Dakatar da Ƙirƙirar Sabbin Masarautu a Jihar Bauchi Amurka za ta ɗauki nauyin ’yan tawaye domin yaƙi da ta’addanci A cewarsa, ’yarsa da ta nuna alamun kamuwa da cutar na kumburin wuya da sarkewar numfashi, an gaggauta mika ta Asibitin Koyarwa na Jami’ar Ahmadu Bello da ke Shika, amma daga bisani ta ce ga...
Kamfanin jirgin sama mallakar jihar Enugu, wato Enugu Air, ya fara aiki a hukumance ranar Litinin bayan ƙaddamar da shi a filin jirgin sama na Akanu Ibiam, Enugu. Mutane da dama sun halarci bikin ƙaddamarwar tare da Ministan Sufurin Jiragen Sama, Festus Keyamo, da sauran manyan baki da suka halarci bikin ƙaddamarwar. APC Ta Tafka Asara, Wani Jigo Ya Fice A Enugu Masu Gida Sun Yi Ruwan Kwallaye A Enugu Enugu Air wani ɓangare ne na hangen nesa da ƙudurin Gwamna Peter Mbah, don inganta harkar sufuri da mayar da Enugu cibiyar jiragen sama a Nijeriya. Kamfanin ya fara aiki da jirage uku na Embraer E170 da E190, wadanda suka dace da zirga-zirgar cikin gida. Jirgin zai fara tashi tsakanin...
Kamfanin dillancin labarun “Reutres” ya bayyana cewa; Cibiyar da take tafiyar da ayyukan agaji a Gaza, wacce Amurka ta kafa ta, ta bayar da wata shawarar da take cewa; a kafa wa mutanen Gaza hemomi na wucin gadi da za su zama masomin yin hijirarsu zuwa wani wuri daban, a cikin yankin ko a wejensa. Rahoton kamfanin dillancin labarun na Reuters ya ambato wata majiya mai karfi tana cewa; An gabatarwa da shugaban kasar Amurka shawarar tilastawa mutanen Gaza yin hijira, kuma a cikin kwanakin nan an tatauna wannan batu a fadar mulkin Amurka ta “White House.” Har ila yau rahoton ya kunshi cewa,tun daga watan Febrairu cibiyar ta fara kokarin tara kudaden da za su kai dalar Amurka biliyan...
A yau Litinin ne kungiyar ta Hizbullah ta fitar da sanarwa wacce ta kunshi yin Allawadai da harin ta’addancin da HKI ta kai wa kasar Yemen, wanda ya shafi tasoshin jiragen ruwa da muhimmacin cibiyoyin kasar. Bayanin na Hizbullah ya kuma ce; Makiya suna tsammanin cewa ta hanyar wannan irin harin na wuce gona da iri za su yi hana Yemen ci gaba da matakin da take dauka na daukaka wajen taimakawa Gaza, ta daina kai hare-hare masu tsanani da take kai musu. Haka nan kuma Hizbullah ta ci gaba da cewa: Har yanzu ‘yan sahayoniya sun kasa fahimtar dabi’ar mutanen Yamen masu hakuri da juriya akan tafarkin jihadi, domin akida ce, cewa gaskiya ita ce wacce ta cancanci a...
Rahotanni da suke fitowa daga kasar ta Kenya sun ce tun safiyar yau Litinin ne ‘yan sanda su ka rufe muhimman hanyoyin da su ka nufi tsakiyar babban birnin kasar Nairobi da kuma muhimman cibiyoyin kasuwanci. Kafafen watsa labarun kasar ta Kenya sun ce da akwai jami’an ‘yansanda masu yawa da aka girke su a cikin muhimman wurare da shatale-tale a cikin birnin da kuma hanyoyin da suka nufi fadar gwamnati. Dubban mutane ne su ka fito titunan birnin Nairobi domin nuna kin amincewarsu da salon Mulki William Ruto wanda suke zargi da cin hanci da rashawa da kuma kama karya. Zanga-zangar ta yau dai ana ba ta sunan; 7/7, wacce ta samo asali a 1990 da al’ummar kasar su...
Tashar talabijin din ‘almayadin’ ta bayar da labarin cewa; kungiyar leken asirin HKI ta cikin gida, “Shabak” ta kama shugaban ofishinta a Falasdinu dake karkashin mamaya Nasir al-Lahham, a gidansa da yake a garin Beithlaham. Majiyar ta kara da cewa; Jami’an kungiyar leken asirin ta “Shabakh” sun dade suna binciken dakin watsa labarin da Lahham yake watsa shirye-shiryensa. Tashar ta “Almayadin’ dai ta bayyana cewa kamun da aka yi wa ma’aikacin nata yana a karkashin Takura mata ne da HKI take yi, domin a cikin watan Oktoba na 2023 ma dai jami’an tsaron sun kai hari cikin gidansa, su ka ci zarafin maidakinsa da kuma kama ‘ya’yansa Basil da Baasil.

Firaministan Kasar Sin: Kasarsa Ta Kimtsa Tsaf Wajen Inganta Aikin BRI Da Bunkasa Kasuwanci Da Zuba Jari Tare Da Habasha
A nasa bangaren, Abiy ya ce Habasha da Sin amintattun kawaye ne na manyan tsare-tsare a dukkan fannoni, kuma kasarsa tana mika tsantsar godiya ga kasar Sin saboda goyon bayan da ta dade tana bai wa Habasha a fannin raya tattalin arziki da zamantakewa. Yayin da yake nuni da irin muhimmiyar rawar da kasar Sin take takawa a harkokin kasa da kasa, musamman a fannin raya ci gaban duniya, Abiy ya ce Habasha a shirye take ta rubanya mu’amala a matakin koli da kasar Sin da kuma zurfafa amincewa da juna ta fuskar siyasa. (Mai Fassara: Abdulrazaq Yahuza Jere) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye...
Saboda matsin lamba na doka da kuma la’akari da mahimman batutuwan siyasa, ya zama dole Gwamnatin Jihar Bauchi ta dakatar da duk wani ci gaba na aikin kwamitin da aka kafa a ranar 4 ga Yuli 2025 domin duba yiwuwar ƙirƙirar sabbin masarautu ko sauye-sauye ga tsarin majalisun gargajiya—musamman a yankunan da har yanzu ke fuskantar shari’a a kotu. Ci gaba da wannan lamari mai sarkakiya alhali wasu muhimman ƙarar shari’a na ci gaba a kotuna, ba wai kawai zai saɓa wa kundin tsarin mulki da ikon shari’a ba, har ila yau, zai iya haddasa tayar da jijiyoyin wuya a cikin al’umma, musamman a yankunan da ke da tarihi na rikice-rikicen ƙabilanci kamar Tafawa Balewa da kewaye. Wannan kira na...
A ƙarshe, lauyoyin Majalisar sun ja hankalin lauyoyin Sanata Akpoti-Uduaghan da su yi taka-tsantsan don kauce wa yi wa kundin tsarin mulki kutse ko sanya rikici a majalisa. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
A ƙarshen makon da ya gabata ne fitacciyar ’yar TikTok wacce aka fi sani da Babiana ta fitar da wani sabon bidiyo tana rusa ihu tana kira ga Shugaba Bola Tinubu da wasu mawaƙan kudancin Najeriya da su shiga tsakaninta da ’yan Arewa a kan abin da tace suna yi mata na cin zarafi tun bayan bayyanar bidiyo tsiraicinta a shekarar 2024. Babiana ta yi bidiyon ne cikin harshen Ingilishi inda ta ce ba a yi mata adalci a Arewa kuma ana barazana da rayuwarta. Sojan Isra’ila ya kashe kansa saboda firgicin yaƙin Gaza Wata bas mai daukar fasinja 56 ta yi hatsari a Jos Ta bayyana cewa tsawon shekara ɗaya ta yi tana raɓe-raɓe saboda ba ta son maganganun...
Rahotanni sun bayyana cewa mazauna wasu jihohin Nijeriya uku na cikin shirin ko-ta-kwana, sakamakon ƙaruwar fargabar samun ambaliya saboda yiyuwar sakin ruwan Madatsar Lagdo ta Kamaru. A cewar wani rahoto da jaridar Punch ta wallafa, jihohin da mazauna ke cikin zaman ɗar-ɗar sun haɗar da Benuwe da Edo da kuma Bayelsa, waɗanda tuni suka fara shiri don kauce wa barazanar ambaliyar. Sojan Isra’ila ya kashe kansa saboda firgicin yaƙin Gaza Wata bas mai daukar fasinja 56 ta yi hatsari a Jos Sai dai Ma’aikatar Albarkatun Ruwa ta Nijeriya ta yi watsi da rahotonnin da ke cewa an buɗe madatsar ruwan, a yayin da tuni jihohin suka fara shirya wa barazanar. Gwamnatin Benuwe ta ce ta fara aikin wayar da kan...
Wani sojan ko-ta-kwana na Isra’ila ya kashe kansa sakamakon tsananin firgici da damuwar da ya shiga a yaƙin Gaza wanda Isra’ila ke aikata kisan-kiyashi. Shafin labarai na Isra’ila, Walla, ya bayyana cewa Daniel Adri mai shekaru 24, wanda ya yi aiki a Gaza da Lebanon, ya kashe kansa bayan doguwar gwagwarmayar da ya yi da matsaloli masu alaƙa da damuwa da kuma rasa abokai biyu a yaƙin na Gaza. Wata bas mai daukar fasinja 56 ta yi hatsari a Jos ’Yan Boko Haram sun kashe mutum 9, skun Jikkata 4 a Borno TRT ya ruwaito cewa an gano gawar sojan a cikin wani daji kusa da birnin Safed a arewacin Isra’ila bayan ya kasa samun sukuni da yadda zai yi...
A taron ƙungiyar BRICS na karo na 17 da aka gudanar a Brazil, ƙasashen mambobi da suka haɗa da China, India, Rasha, Saudi Arabia, Iran da wasu sun soki hauhawar haraji da manufofin kariya ta ciniki da wasu ƙasashe ke aiwatarwa. A sanarwar da suka fitar, sun nuna damuwa kan rikicin Gabas ta Tsakiya, amma sun kaucewa sukar Rasha kai tsaye dangane da rikicin Ukraine. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Hukumar Kula da Muhalli ta Jihar Jigawa (JISEPA) ta yi kira ga al’umma da su ba da hadin kai wajen tabbatar da tsafta da kuma bayar da rahoton duk wani da ake sayarwa da ba bisa ka’ida ba, ko kuma cikin rashin tsafta. Babban Daraktan Hukumar, Alhaji Adamu Sabo ne ya bayyana hakan yayin taron manema labarai da aka gudanar a Dutse, babban birnin jihar Jigawa. A cewarsa, wannan kira ya zama wajibi sakamakon nasarar da hukumar ta samu na kwace gurbatattun kayayyakin na sama da naira miliyan 14 a lokacin sintiri da binciken kayayyaki a fadin jihar daga watan Janairu zuwa Yuni na shekarar 2025. Alhaji Adamu Sabo ya kara da cewa, mafi yawancin kayayyakin da aka kwace na...
Wata babbas bas din haya kirar Macarpollo dauke da fasinjoji ta yi hatsari a garin Jos, hedikwatar Filato. Motar mai daukar fasinjoji 56 ta yi hatsari ne bayan isowarta Mahadar Vom da Anguldi da ke Jos, daga Fatakwal, babban birnin Jihar Ribas. Hatsarin ya auku ne kimanin milomita 10 kafin motar ta isa inda za ta tsaya bayan doguwar tafiyar mai nisan kilomita. Wakilinmu ya gano cewa hatsarin ya auku ne da misalin karfe 4 na asubahin ranar Litinin din nan, inda motar ta lalata kusan daukacin shagunan da ke wurin da ta yi hatsari. ’Yan Boko Haram sun kashe mutum 9, skun Jikkata 4 a Borno Turji: Gwamnatin Sakkwato ta ba da sharadin sulhu da ’yan ta’adda Wani mazaunin...
Hukumar Gyaran Hali ta Najeriya reshen jihar Kano, ta bayyana cewa Fursunoni 58 suna rubuta Jarrabawar Kammala Sakandare ta Kasa NECO ta shekarar 2025. Wannan ci gaba ya samu ne bayan biyan kudin rajista da gwamnatin jihar Kano karkashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf ta yi. Jami’in hulda da jama’a na hukumar, Musbahu Kofar-Nasarawa, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar ga manema labarai a Kano. Ya ce wannan karamci na gwamnatin jihar Kano shaida ce ta jajircewarta wajen kula da walwalar fursunoni, gyaran dabi’unsu da kuma dawo da su cikin al’umma yadda ya kamata. “Biyan kudin rajistar jarrabawa da gwamnatin Kano ta yi alama ce ta jajircewarta wajen samar da dama ga fursunoni domin su...

Araqchi Ya Gana Da Babban Malamin Yahudawa Mai Adawa Da ‘Yan Sahayoniyya A Gefen Taron Kungiyar BRICS
Ministan harkokin wajen kasar Iran ya gana da babban malamin yahudawa rabbi mai adawa da ‘yan sahayoniyya a gefen taron BRICS a Brazil Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya gana kuma ya zanta da wani babban malamin yahudawa mai adawa da ‘yan sahayoniyya a gefen taron kasashen BRICS a kasar Brazil. Rabbi Yisrael Dovid Weiss, wanda ya je Brazil domin ganawa a gefen taron BRICS, ya gana da ministan harkokin wajen Iran, inda suka yi musayar ra’ayi da shi. Wani abin lura shi ne cewa a baya malamin ya ziyarci ofishin jakadancin Jamhuriyar Musulunci ta Iran da ke kasar Brazil bayan bude littafin ta’aziyya ga shahidan da yahudawan sahayoniyya da suke kai wa hari a kasar hari. A...
Kungiyoyin gwagwarmayar Falasdinawa sun yi Allah wadai da hare-haren zaluncin da yahudawan sahayoniyya suka kai kan kasar Yemen Kungiyar Jihadin-Islami ta Falasdinawa da sauran kungiyoyin gwagwarmayar Musulunci na Falasdinu sun yi Allah wadai da hare-haren wuce gona da irin da yahudawan sahayoniyya suka kai kan tashar jirgin Ruwan Hodeida na kasar Yemen, tare da jaddada goyon bayansu ga shugabancin kasar da sojojin kasar da kuma al’ummar kasar ta Yemen. Kungiyar fafutukar ‘yantar da Falasdinu ta fitar da wata sanarwa inda ta tabbatar da cewa: “Kazamin harin wuce gona da iri da yahudawan sahayoniyya suka kai kan kasar Yamen, wanda ya shafi kayayyakin more rayuwa na fararen hula da tashoshin wutar lantarki da tashar jiragen ruwa na Hodeidah da Ras Issa...
Olubadan na Ibadan, Oba Owolabi Olakulehin ya rasu, yana da shekara 90 a duniya. Kakakin iyalan basaraken ne ya tabbatar da mutuwarsa da safiyar yau Litinin cikin wani saƙo da ya aike wa manema labarai. Kwanaki biyu da suka gabata ne basaraken ya gudanar da bikin cikarsa shekara 90 a duniya a wani ƙasaitaccen biki da aka gudanar a fadarsa. A shekarar da ta gabata ne aka naɗa Sarki Olakulehin a matsayin Olubadan na Ibadan bayan rasuwar wanda ya gabace shi Sarki Alli Okunmade II.
Mummunan lamari ya faru ne a lokacin da wata mota kirar bas ta kasuwanci da wata babbar mota ta yi taho-mu-gama da tare da daukar rayukan mutane 21 a hanyar Zariya zuwa Kano. Hadarin ya afku ne a Kasuwar Dogo, Dakatsale, wanda ya hada da wata motar kasuwanci kirar Toyota Hiace da wata tirela ta DAF. Hukumar kiyaye hadurra ta kasa (FRSC) ta bayyana cewa, binciken farko da aka gudanar ya nuna cewa direban motar bas din ya saba ka’idojin zirga-zirgar ababen hawa, lamarin da ya kai ga yin karo da babbar motar da ke zuwa. Hatsarin ya yi sanadiyar mutuwar fasinjoji 21 nan take, wadanda suka hada da manya maza 19 da manya mata 2, yayin...
Gwamnan jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq, ya ce an samar da isassun matakan tsaro domin kawar da wasu gungun miyagu da ke aikata munanan laifuka a jihar. AbdulRazaq ya bayyana hakan ne yayin da ya bayyana wa masu ruwa da tsaki daga yankin Lafiagi na jihar Kwara ta Arewa kan dimbin kokarin gwamnatin jihar a wani taro da aka gudanar a Ilorin. Gwamnan ya amince da damuwar al’ummar tare da tabbatar musu da matakin da gwamnati ke jagoranta kan lamarin. Ya ce sojojin Najeriya za su ci gaba da kai hare-hare a dazuzzukan da aka gano a matsayin sansanin ‘yan ta’adda a Kwara ta Arewa da Kudu. Gwamna AbdulRazaq ya ce ayyukan za su hada da sabbin...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Shugaban kasa Bola Tinubu ya ce gwamnatin tarayya za ta gudanar da aikin samar da wutar lantarki ga jami’ar tarayya ta Kashere da ke jihar Gombe domin tabbatar da samar da isasshen wutar lantarki domin inganta harkokin ilimi. Shugaban ya bayyana hakan ne a wajen taron hadaka karo na uku na jami’ar tarayya ta Kashere da ke karamar hukumar Akko a jihar Gombe. Shugaba Bola Tinubu ya kuma bayyana cewa ma’aikatar albarkatun ruwa ta tarayya za ta fara aikin gina madatsar ruwa a kogin Kashere domin tallafa wa shirin koyar da aikin gona na jami’ar da inganta samar da ruwa ga al’ummomin da ke kewaye. Ya jaddada kudirin gwamnatinsa na inganta samar da ingantaccen ilimi ta hanyar...
Wani malamin addinin musulunci a jihar Zamfara, Sheikh Mohammed Tukur Sani Jangebe, ya yi kira ga gwamnatin tarayya da gwamnatin jihar Zamfara da su gaggauta gudanar da kananan gyare-gyare daga mahadar Maru –Mayanchi – Maradun, da ke kan hanyar zuwa wani yanki na karamar hukumar Talata Mafara. Ya ce mummunan yanayin hanyar yana ci gaba da haifar da babban kalubale ga matafiya tare da fallasa su ga hare-haren ‘yan bindiga a kan hanyar. Sheikh Jangebe ya yi wannan kiran ne a lokacin da yake zantawa da wakilin gidan rediyon Najeriya a Gusau babban birnin jihar Zamfara. Ya bayyana cewa babbar hanyar Maru zuwa Talata Mafara ta samar da ramuka sama da dari, wadanda ke hana zirga-zirgar ababen...
Hukumar kare hakkin bil’adama ta kasa (NHRC) a jihar Kano ta ce ta samu rahoton laifuka 351 na take hakkin yara daga cikin jimillar kararraki 446 da ta samu daga watan Afrilu zuwa Yuni 2025. Kodinetan NHRC na jihar Kano Alhaji Shehu Abdullahi ne ya bayyana haka a Kano. Ya bayyana cewa daga cikin jimillar korafe-korafe 446 da aka samu a cikin watanni uku 351 na da alaka da take hakkin yara. Ko’odinetan jihar ya yi nuni da cewa, sauran shari’o’in sun hada da tashin hankalin gida 19, 18 da suka shafi ‘yancin tattalin arziki da zamantakewa, da kuma biyar da suka shafi ‘yancin rayuwa. “cikin zarge zargen har na Maita da sauran shari’o’in da...
A wani yunkuri na bunkasa samar da wutar lantarki da kuma bunkasar tattalin arziki, gwamnatin jihar Kano ta kaddamar da rabon kashi na farko na taransfoma 500 ga al’ummomin karkara a fadin kananan hukumomin jihar 44. Gwamna Abba Yusuf ne ya kaddamar da shi a hukumance a Kano a wani shirin da nufin magance kalubalen rashin samar da wutar lantarki. Gwamna Yusuf ya ce samar da taransfoma wani shiri ne na bunkasa masana’antu da zaburar da harkokin kasuwanci musamman a yankunan karkara. “Wannan rabon shi ne kashi na farko na aikin samar da wutar lantarki a yankunan karkara, ba wai kawai wani aikin samar da wutar lantarki ba ne, wani muhimmin mataki ne na inganta samar da...
Ministan harkokin wajen kasar Iran wanda yake halattan taron kungiyar raya tattalin arziki ta Bricks ya yabawa kungiyar kan yin tir da Amurka da kuma HKI kan keta hurumin kasar da yaki na kwanaki 12 da kuma da kuma kaiwa cibiyoyin nukliyar kasar ta zaman lafiya wadanda suke Fordo Natanz ta kuma Esfahan. Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ya nakalti ministan yana fadar haka a taron kungiyar karo 17 wanda ke gudana a hilin yanzu a birnin Rio De jenero na kasar Brazil. A ranar 13 ga watan Yunin da ya gabata ne jiragen yaki na HKI suka kutsa cikin Iran inda suka kashe manya-manyan kwamandocin sojojin kasar da kuma masana fasahar Nukliyar kasar ga shahada. Bayan haka...
Shugaban Kungiyar Harka Islamia a tarayyar Najeriya Sheikh Irahim Zakzaky ya taya mutanen kasar murna saboda nasarar da suka samu kan HKI da kuma Amurka a yakin kwanaki 12 a cikin watan da ya gabata. Ya ce wannan nasarar bata takaita da mutanen kasar Iran kadai ba , hada har da al-ummar Musulmi da kuma da kuma masu sun yenci a ko ina suke. Ya kuma yaba da yadda gikuwan nmalamai na kasar Iran suka sami nasarar kare kasar daga mafi yawan hare-haren HKI a kan kasar. Ya bayyana cewa Iran ta sami nasara a kan kasashen yamma da makamai wadanda suka fi nasu karfi da inganci, har’ila yau sun sami nasara a kan ma;aikatan yahudawan da suke taimaka masu...
Miliyoyin yan Najeriya ne suka gudanar da tattakin Ashoora a birne daban daban a kasar a jiya Lahadi. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran, da farko ya nakalto daruwan da suka fito tattakin na Ashoora a Abuja babban birnin kasar a safiyar jiya Lahadi. A wannan karon dai masu tattakin Ashoora a Abuja sun fito ba tare da sanya bakaken kaya ba saboda kaucewa rikici da kuma kamu daga Jami’an tsaro a birnin, kamar yadda suka sabayi a shekarun da suka gabata. Labarin ya kara da cewa an gudanar da irin wannan tattakin na Ashoora a garurwa kimai 25 a duk fadin kasar, kuma an kammala ba tare da wata matsala ba. An gudanar da tattaki a jihar Bauchi...
Kasar China ta maida martani ga takunkuman tattalin arziki na wasu kayakin kiwon lafiya wadanda tarayyar Turai da dorta maya. Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto majiyar kasar ta Chaina na fadar haka ta kuma kara da cewa gwargwadon takunkuman da suka dorawa kasar gwargwadon maida martanin kasar ta China. Labarin ya kara da cewa wannan haramcin ba zai shafi kamfanonin turai da suke samar da kayakin aikin kiwo lafiya a cikin kasar China ba. A cikin watan Yunin da ya gabata ne kungiyarn EU ta hana gwamnatocin kasashe kungiyar sayan kayakin aikin likita fiye da dalar Amurka miliyon 5 tare da bukatar kasar china ta daina nuna bambanci a cikin ahrkokin kasuwanci da ke tsakaninsu.
Gwamnatin Jihar Sakkwato ta ƙalubalanci jagoran ’yan bindiga Bello Turji, wanda ke neman sulhu, da cewa idan da gaske yake yi, to ya sako duk mutanen da ya yi garkuwa da su, ya daina kai hare-hare, kafin ta zauna da shi. Mashawarci na musamman ga gwamnan Sakkwato a kan sha’anin tsaro, Kanar Ahmed Usman ne ya bayyana hakan baya yaɗuwar wani bidiyo da Turji ya saki, wanda a ciki yake neman a yi tsakaninsa da gwamnati. Ɗan ta’addan wanda ya addabi yankunan jihar da makwabta ya saki bidiyon ne kwanaki kaɗan bayan jami’an tsaro sun kashe wasu gaggan kwamandojinsa da Faransa sama da 100. Kamar Ahmed, a cikin wata sanarwa ya bayyana cewa babu yadda za a tabbatar cewa neman...
Tawagar ƙwallon ƙafar mata ta Nijeriya ta fara gasar ƙwallon ƙafa ta mata ta ƙasashen Afirika da kafar dama, bayan lallasa ƙasar Tunisia da ci 3-0 a wasan farko da suka buga yau Lahadi a filin wasa na Prince Moulay Abdellah. Asisat Oshoala da Rinsola Babajide da Chinwendy Ihezuo ne suka jefa kwallayen da suka yi sanadiyar samun nasarar ‘yan matan, yanzu Nijeriya ta dare teburin rukunin ‘B’ wanda ke ɗauke da ƙasashen Algeria da Botswana da Tunisia da Nijeriya. Ƙwallon Mata: Rivers United Ta Doke Nasarawa Amazons A Wasan Ƙarshe Na Kofin Shugaban Ƙasa Wace Nahiya Ce Ta Fi Iya Ƙwallon Ƙafa Tsakanin Turai Da Kudancin Amurka? ‘Yan matan da Madugu ke jagoranta za su haɗu da ƙasar Botswana...
Wani bincike da Cibiyar Bincike ta Africa Polling Institute (API), ta gudanar ya nuna cewa yawancin ’yan Najeriya ba su da ƙwarin gwiwa game da Gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, Majalisar Dokoki da kuma ɓangaren shari’a. An bayyana sakamakon Binciken Haɗin Kan Al’ummar Najeriya na 2025, a wani taron ƙasa da aka gudanar a Abuja. Elon Musk zai kafa sabuwar jam’iyyar siyasa a Amurka Tinubu ya umarci sojoji su murƙushe ’yan ta’adda a faɗin Najeriya Bincike ya nuna kashi 83 cikin 100 na ’yan Najeriya ba su yadda da Gwamnatin Tarayya da Shugaba Tinubu ke jagoranta ba. Haka kuma, kashi 82 cikin 100 ba su da ƙwarin gwiwa kan Majalisar Dokoki, wadda ke ƙarƙashin jagorancin Godswill Akpabio da Kakakin Majalisar...
“Na yi Allah- wadai da amfani da madafun iko da tsara sakamakon zabe kafin zabe ta hanyar amfani da karfin mulki da hukumomin gwamnati.” “Wajibi ne Hukumar Zabe ta samu hanyoyin magance wadannan matsalolin a wajen jefa kuri’a maimakon neman hakki a bangaren shari’a wanda daga karshe kotu za ta sanya wasu dubaru ta kori kara mai kyau ta fashin zabe.” Ya bayyana. Ya ce irin wannan matsalar na samar da mutanen da ba su ko iya cin zabe a cikin dangin su ko al’ummar su amma sune ke tinkahon lashe zabe. A cewarsa a matsayinsa na dan majalisar dattawa suna kokarin gabatar da dokokin da za su shawo kan wadannan matsalolin, ya ce sun san hukumar zabe ba za...
A cikin ‘yan kwanakin nan ne shugaban kasar Sin Xi Jinping ya mayar da jawabi ga malamai da daliban tawagar musayar al’adu ta matasan Amurka masu buga wasan kwallon pickle daga gundumar Montgomery ta jihar Maryland, wadanda suka ziyarci kasar Sin a karkashin shirin gayyatar matasan Amurkawa 50,000 zuwa kasar Sin domin yin musaya da kuma nazarin karatu a cikin shekaru biyar. Xi ya ce, makomar alakar Sin da Amurka ta dogara ce da matasa, yana mai bayyana fatan wakilan tawagar za su zama sabbin jakadu na sada zumunci a tsakanin kasashen biyu, da ba da gudummawa sosai wajen yaukaka zumuncin da ke tsakanin jama’ar kasashen biyu. (Mai fassara: Abdulrazaq Yahuza Jere) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna...
Elon Musk, wanda ya taɓa zama mashawarcin Shugaban Amurka Donald Trump, ya ce zai kafa sabuwar jam’iyyar siyasa mai suna America Party. Ya bayyana hakan ne a shafinsa na X (Twitter), makonni bayan wata taƙaddama da ta ɓarke tsakaninsa da Shugaban Amurka. Tinubu ya umarci sojoji su murƙushe ’yan ta’adda a faɗin Najeriya Mutum 21 sun rasu a hatsarin mota a kan hanyar Zariya–Kano Musk, wanda attajirin mai kuɗi sosai, ya ce jam’iyyarsa za ta kasance wata hanya ta daban daga jam’iyyu biyu da ake da su yanzu, wato Republican da Democrat. Amma har yanzu ba a bayyana ko hukumar zaɓen Amurka ta amince da rajistar jam’iyyar ba. Amma Musk bai bayyana wanda zai jagoranci jam’iyyar ko irin manufofinta ba....
Kungiyoyi farar da jam’iyyun adawar siyasa a kasar Togo, sun sake yin kira da a gudanar da Zanga-zanga a ranar 16 da 17 ga watan nan na Yuli da ake ciki. Masu Zanga-zangar dai suna son nuna kin amincewa ne da siyasar hukumar kasar da suke bayyanawa da ta kama-karya, haka nan kuma kashe wasu mutane da aka yi a Zanga-zangar da ta gabata. Bugu da kari, kiran a yi zanga-zangar dai ya zo ne bayan kama wasu ‘yan hamayyar siyasa da aka yi da kuam kara kudin wutar lantarki, da amince da sabon tsarin mulki da ya kara bai wa shugaban kasar Faure Gnassingbe karfin iko. Wasu fitattun masu fafutuka a kasar, sun watsa sanarwa a shafukan sada zumunta...
Raundunar sojan jamhuriyar Nijar sun sanar da cewa, an kashe sojoji 10 da kuma jikkata wasu 15 a wasu hare-hare biyu da masu dauke da makamai su ka kai a yankin Telaberi da kudu masu yammacin kasar. Yankin Telaberi dai yana cikin yankunan da masu dauke da makamai su ka fara kai hare-hare saboda kusancinta da iyakokin kasashen Mali da Burkina Faso. Bayanin na sojojin kasar ta Jamhuriyar Nijar wanda kafafen watsa labarun kasar su ka watsa ya kunshi cewa; Daruruwan masu dauke da bindiga sun kai hare-hare a kan sansanonin soja biyu da suke a yankin Telaberi da hakan ya yi sanadiyyar kashe sojoji 10 da kuma jikkatar wasu 15.” Sai dai kuma sanarwar ta ce, sojojin sun yi...
Babban magatakardar kungiyar Hizbullah Sheikh Na’ima Kassim ya bayyana cewa; Dakarun Hizbullah mazajen fagen daga ne da ba su karbar kankanci. Sheikh Na’im Kassim wanda ya gabatar da jawabi a wurin babban taron Ashura a ungiyar Dhahiya dake birnin Beirut, ya bayyana cew; Yaki na tsaron kasa zai ci gaba saboda mun yi Imani da ‘yanto da kasa, kuma wajibi ne akansu, ko da kuwa an dauki lokaci mai tsawo sannan kuma sadaukar da kai ya yawaita.” Sheikh Na’im Kassim ya kuma ce; Isra’ila abokiyar gaba tana ci gaba da mamaye yankuna 5 na Lebanon, don haka babu yadda za a yi mu mika kai.” Haka nan kuma ya yi tambayar cewa; Ta yaya za a tsammaci za mu ki...
Sanatan ya bayyana cewa gwamnonin yankin na farko sun ba da gagarumar gudunmuwa wajen jagorantar hadin kai wajen cimma muradun yankin daga kan ikon sarrafa albarkatun kasa zuwa matsalolin muhalli da sauransu. A kan wannan ya yi kira ga gwamnoni.masu ci a yanzu da su ci gaba da wannan al’adar, kuma su kara kokari kan ciyar da yankin a gaba. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Ɗaya daga cikin hadiman gwamnan jihar Yobe, Hon. Babagana Yakubu Mohammed, ya ajiye muƙaminsa na mai taimakawa gwamna na musamman ya kuma fice daga jam’iyyar APC zuwa jam’iyyar ADC. Babagana, ya sanar da ajiye aikin nasa ne cikin wata wasiƙa da ya aikewa Sakataren Gwamnatin Jihar, Baba Malam Wali. Ba Ni Da Niyyar Barin APC Zuwa Wata Jam’iyyar — Gwamna Zulum Ranar Talata Mai Zuwa Zan Koma Zauren Majalisar Dattawa – Sanata Natasha A kwafin wasiƙar da LEADERSHIP ta samu, Babagana ya bayyana matuƙar damuwarsa kan yadda aka yi watsi da wanda suke hidimtawa gwamnati da taimaka mata. “Don haka ina sanar da ajiye aiki na a hukumance daga matsayin mai taimakawa gwamna na musamman” cewarsa. A ƙarshe, ya godewa...
Masanin Kenya kan huldar kasa da kasa mai suna Cavince Adhere, ya bayyana a yayin zantawarsa da dan jarida na kamfanin dillancin labarai na Xinhua a kwanan nan cewa, a matsayinta na daya daga cikin kasashe masu tasowa, hadin gwiwar Sin da kasashe masu tasowa ya jaddada daidaito da samun albarkatu, inda hakan ya samu aminci daga kasashe masu tasowa. Kuma har ila yau, hadin gwiwar dake tsakanin Sin da kasashe masu tasowa ya riga ya samu gagarumin ci gaba, don haka makomar kasashe masu tasowa na bukatar ci gaba da kasancewar Sin a cikinsu. Bugu da kari, Cavince Adhere ya jaddada cewa, Sin ta bayyana bukatun kasashe masu tasowa na duniya yadda ya kamata, kana tana inganta ra’ayoyin da...
Zalum ya kuma shawarci gidajen jaridu da su dinga tantance labarai kafin su yaɗa shi domin kaucewa labaran ƙanzon kuregen da wasu suke yaɗawa. A ƙarshe gwamnan ya ce ya duƙufa wajen hidimtawa al’ummar jihar Borno a ƙarƙashin jam’iyar mai albarka ta APC . Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Labarin da dan jarida ya samu daga ma’aikatar tsaron jama’a ta kasar Sin a yau Lahadi ya nuna cewa, a kwanan baya kasashen Sin da Myanmar da Thailand sun gudanar da taron ministoci karo na biyu don yaki da laifukan zambar da ake aikatawa ta hanyar sadarwar waya. A gun taron, sassan da abin ya shafa na kasashen uku sun cimma matsaya kan zurfafa hadin gwiwar tabbatar da doka da oda, kuma za su ci gaba da yin hadin gwiwa wajen dakile laifukan zamba ta hanyar sadarwar waya a Myawaddy da sauran wurare, da kawar da harkokin zamba ta hanyar sadarwar waya gaba daya, da kame dukkan ma’aikatan da ke da alaka da laifin zamba, kana za su yi tsayin...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Aƙalla mutum 21 ne suka rasu a wani mummunan hatsarin mota da ya auku a kan babban titin Zariya zuwa Kano. Hukumar Kiyaye Haɗura ta Ƙasa (FRSC), reshen jihar ce ta tabbatar aukuwar hatsarin. Hatsarin ya auku ne da misalin ƙarfe 8:23 na safe a unguwar Kasuwar Dogo da ke yankin Dakatsalle. Zulum ya musanta shirin ficewa daga APC Gwamna ya gargaɗi sarakuna kan mamaye filayen kiwo a Gombe Hatsarin ya rutsa da wata babbar mota ƙirar DAF mai lambar GWL 422 ZE da kuma motar ɗaukar fasinjoji ƙirar Toyota Hummer mai lambar KMC 171 YM. FRSC, ta ce bincike ya nuna cewa direban motar fasinjojin ne ya karya doka ta hanyar bin hanyar da ba ta dace ba, wanda...
Aƙalla mutum 21 ne suka rasu a wani mummunan hatsarin mota da ya auku a kan babban titin Zariya zuwa Kano, kamar yadda Hukumar Kiyaye Haɗura ta Ƙasa (FRSC), ta tabbatar. Hatsarin ya auku ne da misalin ƙarfe 8:23 na safe a unguwar Kasuwar Dogo da ke yankin Dakatsalle. Zulum ya musanta shirin ficewa daga APC Gwamna ya gargaɗi sarakuna kan mamaye filayen kiwo a Gombe Hatsarin ya rutsa da wata babbar mota ƙirar DAF mai lambar GWL 422 ZE da kuma motar ɗaukar fasinjoji ƙirar Toyota Hummer mai lambar KMC 171 YM. FRSC, ta ce bincike ya nuna cewa direban motar fasinjojin ne ya karya doka ta hanyar bin hanyar da ba ta dace ba, wanda hakan ya sa...
Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya ƙaryata jita-jitar da ke yawo a kafafen sada zumunta cewa zai bar jam’iyyar APC zuwa ADC tare da wasu gwamnoni biyar. A wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Dauda Iliya, ya fitar, Zulum ya ce wannan labari ƙarya ne, kuma wasu ne kawai ke ƙirƙirarsa domin cimma wata manufa ta ƙashin kansu. Gwamna ya gargaɗi sarakuna kan mamaye filayen kiwo a Gombe Majalisar Dattawa ta gindaya sharaɗin dawo da Sanata Natasha Ya ce yana nan daram a jam’iyyar APC kuma yana biyayya ga jam’iyyar a matakin jiha da ƙasa baki ɗaya. Sanarwar ta ce, “Mun ji wani labari da ake yaɗawa cewa zan koma jam’iyyar ADC tare da wasu gwamnoni biyar. “Wannan...
Gwamnan Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya gargaɗi sarakunan gargajiya a faɗin ƙananan hukumomi 11 na jihar kan zargin hannu a mamaye hanyoyin kiwo da filayen kiwo, abin da ke haddasa rikici tsakanin makiyaya da manoma. Gwamnan ya nuna damuwa kan rahotannin da ke cewa wasu sarakuna na karɓar cin hanci suna kuma ba da damar shiga filayen kiwo ba bisa ƙa’ida ba, lamarin da ke ƙara tayar da zaune tsaye a tsakanin al’umma. Majalisar Dattawa ta gindaya sharaɗin dawo da Sanata Natasha Ambaliyar ruwa ta yi ajalin mutum 50 a Amurka “Duk wanda aka kama yana da hannu a wannan aika-aikar, za mu hukunta shi bisa doka,” in ji Gwamna. Ya kuma roƙi makiyaya da su guji shiga gonaki domin...

Taron Ashura Ya Zama Lamari Mafi Girma Da Cinkoson Jama’a, Inda Masu Ziyara Daga Sassan Duniya Suka Isa Karbala
Gangamin Ashura ya zama lamarin mafi girma da cunkoson jama’a inda tattakiin Tuwairij yake gudana tare da faɗaɗa da ba a taɓa ganin irinsa ba Tattakin Tuwairij na bana zuwa birnin Karbala na fuskantar hallara da cunkoson jama’a da ba a taba ganin irinsa ba, inda dimbin masu ziyara daga sassan duniya ke tururuwa zuwa hubbaren Imam Husaini da kuma titunan da ke kewaye. Mai ba da shawara ga babban sakataren cibiyar Hubbaren Imam Husain {a.s} Fadel Oz a cikin wata sanarwa da ya aikewa kafafen watsa labarai ya bayyana cewa: “A shirye-shiryen wannan juyayi, babban Sakatariyar Haramin Imam Husain (a.s) da haramin Abbas sun samar da dukkan sharuddan da suka dace don kula da masu ziyara da kuma tabbatar...
An sake gudanar da wani sabuwar zanga-zanga a manyan biranen duniya domin neman kawo karshen kisan kiyashin da ake yi a Gaza A jiya asabar ne aka sake gudanar da wata sabuwar zanga-zanga a kasashe da dama na duniya domin nuna adawa da hare-haren da gwamnatin ‘yan sahayoniyya ke ci gaba da kai wa kan zirin Gaza, wanda ya yi sanadin mutuwar Falasdinawa sama da 192,000 tare da jikkata yawancinsu mata da kananan yara. A cewar cibiyar yada labaran Falasdinu, mutane da dama ne suka gudanar da zanga-zanga a gaban ma’aikatar harkokin wajen kasar a Quito babban birnin kasar, domin nuna goyon bayansu ga Falasdinawa a zirin Gaza. Masu zanga-zangar sun yi kira da a kawo karshen yaki da kisan...
Ministan harkokin wajen kasar Iran ya tafi kasar Brazil don halartar taron BRICS karo na 17 Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Ismail Baqa’i ya sanar da isar ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi a birnin Rio de Janeiro domin halartar taron kasashe mambobi a kungiyar BRICS karo na 17. Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Ismail Baqa’i ya bayyana a cikin wata sanarwa cewa: Tawagar kasar Iran karkashin jagorancin ministan harkokin wajen kasar Abbas Araqchi za ta halarci taron kasashen BRICS. Baqa’i ya rubuta a shafinsa na sada zumunta cewa: “Sun isa birnin Rio de Janeiro na Brazil, domin halartar taron kasashen BRICS karo na 17.”
Babban Mufti na masarautar Oman ya yi kakkausar suka kan kasashen da ke neman kulla alaka da haramtacciyar kasar Isra’ila Babban Mufti na masarautar Oman, Sheikh Ahmed bin Hamad Al-Khalili, ya bayyana mamakinsa kan yadda wasu kasashe ke son kulla alaka da makiya yahudawan sahayoniyya, wata kasa ‘yar mamaya maras tushe. A cikin wani bayani da ya wallafa a shafinsa na X, Ahmed bin Hamad Al-Khalili ya ce: “Abin mamaki ne yadda wasu kasashe ke son kyautata alaka da makiya yahudawan sahayoniyya, alhali su kansu suna kallon wannan mahalukiya a matsayin wata kasa mai gushewa ko ba dade ko ba jima, al’ummarta dai suna son ci gaba da yakin ne kawai don ci gaba da wanzuwarta, in ba haka ba,...
Aƙalla mutane takwas ne suka mutu a wani mummunan hatsarin mota da ya faru a Atura Bus Stop, hanyar Lagos-Badagry, lokacin da wata motar haya ƙirar Mazda mai ɗaukar fasinjoji 16 ta yi taho-mu-gama da wata babbar mota ƙirar DAF. Hukumar LASTMA ta bayyana cewa hatsarin ya faru ne sakamakon gudun wuce sa’a da rashin iya sarrafa mota daga direban motar hayar. A cikin wata sanarwa, Daraktan Hulɗa da Jama’a na LASTMA, Adebayo Taofiq, ya ce hatsarin ya kasance mai muni matuƙa, inda ya kashe direban motar, yaran moto da sauran fasinjoji shida. Ya ce hatsarin ya jefa al’ummar yankin cikin alhini da ɗimuwa. Jami’an LASTMA, da FRSC, da rundunar ƴansanda da Sojoji daga Ibereko sun gudanar da aikin ceto...
A ranar Asabar, ƙungiyar PSG ta doke Bayer Munich da ci 2-0 a wasan zagayen kusa da na ƙarshe na gasar Kofin Duniya na Kungiyoyi, wanda aka buga a filin wasa na Mercedes Benz, Atlanta, Amurka. Duk da samun katin kora guda biyu, PSG ta nuna kwarewa da jajircewa wajen zura ƙwallaye masu kyau a raga. A wani wasa da aka buga a daren ranar Asabar a filin wasa na MetLife Stadium, New Jersey, Real Madrid ta doke Borussia Dortmund da ci 3-2. Madrid ta fara da ƙwallaye biyu daga Gonzalo Garcia da Fran Garcia, kafin Dortmund ta yi ƙoƙarin dawo da wasan. Kylian Mbappé ya ƙara wa Madrid ƙwallo ta uku da kyakkyawan bugun watsiya, sai dai Dortmund ta...
Hukumomi a Jihar Texas ta Amurka sun ce gomman mutane sun riga mu gidan gaskiya ciki har da kananan yara sakamakon wata mummunar ambaliyar ruwa a ranar Asabar. Sai dai ya zuwa yau Lahadi, adadin wadanda suka mutu sun kai 50 ciki har da kananan yara 15 yayin da ake ci gaba da aikin ceto wadanda lamarin ya rutsa da su kamar yadda wani babban jami’in dan sanda na yankin, Larry Leitha ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na AFP. An kama ɗan Najeriya yana taimaka wa Rasha a yaƙinta da Ukraine Sojoji sun kashe ’yan ta’adda 41 a Nijar Tuni dai Shugaba Donald Trump ya sanar da cewa gwamnati na yin duk mai yiwuwa wajen kai dauki yankin na...
Lamarin da ya haddasa daya daga cikin bala’i da mutane suka taba fadawa, inda sama da mutum miliyan 12 suka tsere daga gidajensu. Darfur ta kasance yankin da nan da nan rikici kan tashi, inda RSF ke iko da yawancin yankin, in banda birnin el-Fasher wanda ya ci gaba da kasancewa a hannun rundunar sojin kasar da kawayenta. Birnin el-Fasher ya sha ruwan bama-bamai a yayin da RSF ke kokarin kama shi. A watan Afirilu RSF din ta sanar da shirin kafa gwamnati domin zama kishiya ga gwamnatin soji, abin da ya haddasa fargaba cewa hakan zai kai ga rarraba kasar. Alawia ta ce yayin da fadan ya tsananta ake ta ruwan bama-bamai a watan da ya gabata, dole ita...
Sojojin Ukraine sun kama wani ɗan Nijeriya da ke taimaka wa Rasha a yaƙin da suke gwabzawa sama da shekaru biyu biyo bayan mamayar ƙasarsu. Wani bangaren sojin da ke ƙunshe da mayaƙan Rasha da ke goyon bayan Ukraine a wannan yakin, wanda ake kira ‘Freedom Of Russia Legion ne ya kama Kehinde Oluwagbemileke mai shekaru 29 a yankin Zaporizhzhia bayan shafe watanni biyar yana yaƙi a cikin mayaƙan Rasha. Sojoji sun kashe ’yan ta’adda 41 a Nijar Kwankwaso ba zai yi mana takara a 2027 ba — NNPP Oluwagbemileke ya shafe shekaru huɗu yana zaune a ƙasar Rasha kafin a kama shi akan laifin da ke da nasaba da miyagun ƙwayoyi. An ruwaito cewa matashin ya amince ya shiga...
Rashford dai ya fi son komawa kungiyar kwallon kafa ta Barcelona domin yana ganin zai iya buga abin a zo a gani a kakar wasa mai zuwa sai dai ita kuma Barcelona ta fi son dan wasa Nico Williams na kungiyar Athletico Bilbao ta kasar Spaniya, wanda shima yake son komawa Bardelona da buga wasa idan har Barcelonan za ta iya biyan kudin da aka yi masa farashi. Kungiya ta kwana-kwanan nan da ta nemi Rashford ita ce kungiyar Bayern Munchen ta Jamus, bayan da Liberpool ta ce ba za ta sayar mata da Luiz Diaz ba, ana ganin yanzu kungiyar za ta karkata akalarta zuwa neman Rashford. Kungiyoyi irinsu Newcastle United da Tottenham da kungiyoyi daga Saudiyya duka sun...
Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci Imam Sayyid Aliyul Khaminae ya halarci zaman makokin da aka gudanar a hussainiyar Imam Khomaini (q) da cikin gidansa a nan birnin Tehran a daren Ashoorah a jiya Asabar da yamma. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Hujjatul Islam Masaoud Ali wanda ya karanta makokin yana fadar cewa, kasar Iran zata dauki darasi daga Imam Hussain (a) na rashin mika kai da azzalumai. Ya kuma bayyana yunkurin da Iraniyawa suke yi a halin yansu yana daga cikin gwagwarmayan duniya don fuskantar azzaluman duniya karkashin jagorancin HKI da Amurka. Ya kuma kara da cewa musulunci ne yake gaba da gaba da kafircin duniya a cikin yakin kwanaki 12 wanda HKI da Amurka...

Iran ta Bukaci Gudanar da Bincike Kan Sacewar jami’ar Diblomasiyyar kasar A Lebanon Shekaru 43 Da Suka gabata
Ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ta yi tir da ci gaba da riki jami’an diblomasiyyar kasar 4 wanda HKI take yi tun shekaru 43 da suka gabata. Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto ma’aikatar harkokin wajen kasar tana fadar haka a wata sanarwa da ta fitar shekaru 43 cur da sacewar wadanda Jami’an diblomasiyyar kasar a birnin Beirut babban birnin kasar Lebanon a ranar 4 ga watan Yuli n shekara 1982. Jami’an diblomasiyyar suna ne Seyed Mohsen Mousavi, Ahmad Motevaselian, Kazem Akhavan, and Taghi Rastegar Moghadam, wadanda wata kungiyar yar ta’adda wacce HKI take goyon bayanta ta kamasu ta kuma mikawa HKI a lokacinda take mamayae da kasar Lebanon. Rahoton ya yabawa gwamnatin kasar Lebanon kan hadin...
Majiyar kafafen yada labarai na Amurka sun bayyana cewa akalla mutane 52 suka rasa rayukansu sanadiyyar ambaliyar ruwan sama a jihar Texas. Jaridar US Today ta bayyana cewa an kubutar da daruruwan mutane daga halaka, amma kuma har yanzun ba san makamon daruruwan mutane ba. Sannan kungiyoyin bada agaji suna ci gaba da neman masu sauran shanruwa. Ruwan sama kamar da bakin kwarya ne ya sauka a jiya Asabar ya kuma ciika kogin Guadalupe wanda yayi ambaliya ya kuma rufe garuruwa da dama da suke bakin kogin. Gwamnatin Jihar Tezas Dan Patrick ya bayyana cewa an kubutar da mutane kimani 850 amma yawan matattu kuma yana karuwa a lokacinda jami’an agaji suke ci gaba da neman gawaki da kuma masu...
Kamfanin jiragen sama na UAE airlines ko emirate ya sake farfado da zirga zirga zuwa kasar Iran bayan da aka rufe sararin samaniyar kasar Iran a ranar 13 ga watan Yunin da ya gabata. Jaridar National ta kasar Amurka ta bayyana cewa kasashe da dama a duniya sun dakatar da zirga zirga zuwa JMI saboda yakin da HKI da Amurka suka kai mata daga 13 ga watan zuyi har zuwa kwanaki 12. Labarin ya kara da cewa kasashen Iraki da Jordan sun dakatar da zuwa kasar Iran saboda yaki kuma saboda gwamnatin Iran ta hana jiragen sama tashi ko kuma zuwa kasar. A ranar Alhamis ne JMI ta gabata ne hukumomin Iran suka bude sararin samaniyar kasar wanda ya nuna...
Dakarun sojin Nijar sun samu nasarar kashe ’yan ta’adda 41 a yayin wasu tagwayen hare-hare da aka kai musu ranar Juma’a a yammacin ƙasar. A cikin wata sanarwa, Ministan Tsaron Nijar, Janar Salifou Modi ya ce hare-haren ta’addancin da ɗaruruwan ’yan ta’adda suka kai a lokaci guda, sun auku ne a yankunan Bouloundjounga da Samira a Ƙaramar Hukumar Gotheye. Sanarwar da aka karanto a tashar talabijin ta ƙasar ta ƙara da cewa an yi asarar dakarun ƙasar 10, kana wasu 15 suka ji rauni a sakamakon wannan hari. Yankin Gotheye yana kusa da iyakar Nijar da Mali da Burkina Faso kuma yanki ne da ya daɗe yana fuskantar hare-hare daga ƙungiyoyi masu iƙirarin jihadi. Ƙauyen Samira na da kamfanin hakar...
Rukunin farko: Morocco da Zambiya da Senegal da kuma Jamhuriyar Congo Rukuni na biyu: Nijeriya da Tunisia da Algeria da kuma Botswana. Rukuni na uku: Afirka ta Kudu da Ghana da Mali da kuma Tanzania. Bayan karawar bude labulen gasar, akalla za a rika buga wasanni bibiyu kowacce rana a fafatawar cikin rukuni har zuwa ranar Litinin 14 ga watan Yuli. Sannan a lokacin wasannin cikin rukuni za ake buga su daga 13:00 da 16:00 da kuma19:00 daidai da agogon GMT. Za a fara karawar zagaye na biyu daga ranar Juma’a 18 ga watan Yuli. Shekara ukun da ta gabata, Morocco ta gudanar da gasar cin kofin Afirka ta mata, kuma filaye ukun da ta yi amfani da su,...
Ibrahim ya bayyana cewa, sun rarraba mukamai na rikon jam’iyyar a tsakaninsu, kafin babban taro na kasa a nan gaba. Gwamnan Jihar Kaduna, Nasiru El-Rufai ya tabbatar cewa; hadakar ta ADC, ta zabi Aregbesola a matsayin sakatarenta na kasa na riko, har ma ya wallafa a jawabin karbar mukamin da ya yi a shafukan sada zumunta. Matakin ‘yan adawar na shiga ADC, na zuwa ne bayan kasa cimma bukatarsu ta yi wa sabuwar kungiyar mai suna ‘All Democratic Alliance’ (ADA), rajista a matsayin jam’iyyar siyasa, sakamakon jan kafa da suka rika samu daga babbar hukmar zabe ta kasa (INEC). Haka zalika, Atiku Abubakar da wasu manyan jam’iyar PDP, sun nemi ‘yan jam’iyyar da su hada hannu da su wajen shiga...

Wakilin Sin Ya Yi Jawabi Game Da Raya Hidimomi Ga Nakasassu Ta Hanyar Fasahar AI A Madadin Wakilan Kasashe Fiye Da 70
Zaunannen wakilin Sin dake ofishin MDD da sauran kungiyoyin kasa da kasa a birnin Geneva Che Xu, ya yi jawabi a gun taron tattaunawa na shekara-shekara, kan gudummawar fasahohi karo na 59, na majalisar kare hakkin dan Adam ta MDD a jiya Juma’a, a madadin walikan kasashe fiye da 70, game da raya hidimomi ga nakasassu ta hanyar fasahar AI, inda ya yi kira ga raya fasahar AI don inganta fasahohi, da karfin hidimomin da ake samarwa nakasassu, da kuma sa kaimi ga sassan kasa da kasa, ta yadda za su iya more fasahohin bunkasa fasahar AI. A cikin jawabin nasa, ya gabatar da shawarwari uku. Na farko ya ce kamata ya yi a mai da hankali ga bukatun dan...
Kwamatin kananan hukumomi na majalisar dokokin jihar Jigawa ya tunasar da karamar hukumar Roni game da bukatar gina wani rukuni mai dauke da ajujuwa guda biyu ga makarantun ‘ya’yan Fulani makiyaya domin inganta rayuwar su. Shugaban kwamatin, Alhaji Aminu Zakari, ya yi wannan kiran a karshen ziyarar kwanaki biyu da kwamatin ya yi a karamar hukumar Roni. Alhaji Aminu Zakari wanda shi ne wakilin mazabar Gwiwa a majalisar dokokin jihar Jigawa, ya ce tanadin gina ajujuwan ga makarantun ‘ya’yan Fulani makiyaya na kunshe cikin kasafin kudin kananan hukumomi. Ya kuma bayyana gamsuwa da bin kyakkyawan tsarin sadarwa tsakanin bangaren zartaswa da na kamsiloli ta yadda bangaren kamsiloli ya nemi bayani kan jerin ayyukan raya kasa da karamar hukumar ta...
Jita-jita ta fara ƙarfi cewar Sanata Ibrahim Lamiɗo da ke wakiltar Sakkwato ta Gabas a Majalisar Dattawa, na shirin ficewa jam’iyyar APC zuwa ADC. Wannan jita-jita ta fara ƙarfi ne bayan da wasu ‘yan siyasa suka haɗu don kafa sabuwar jam’iyya mai suna ADC da nufin kayar da APC a zaɓen 2027. Gonakin Koko: Mata sun yi barazanar zanga-zanga tsirara a Kuros Riba Kwankwaso ba zai yi mana takara a 2027 ba — NNPP A cewar wasu, Sanata Lamiɗo ba ya mu’amala da gwamnatin APC a jihar inda alaƙarsa ta fi ƙarfi da ‘yan adawa. Wannan ne ya sa ake ganin ba zai tsaya takara a APC ba a 2027. Wani ɗan siyasa da ya nemi a sakaya sunansa ya...

Kuri’ar Jin Ra’ayin Jama’a Ta CGTN Ta Nuna Goyon Baya Ga Fadadar Kungiyar BRICS A Matsayin Hanyar Bunkasa Hadin Gwiwa
Taron farko na tsarin hadin gwiwar kungiyar BRICS, tun bayan shigar Indonesia da sauran abokan huldar kungiyar 10, ya ja hankulan sassan kasa da kasa. Har ma wata kuri’ar jin ra’ayin jama’a da kafar CGTN ta kasar Sin ta gudanar, ta nuna cewa kaso 91.2 bisa dari na masu bayyana ra’ayoyi na ganin hadin gwiwa karkashin tsarin hadakar BRICS, ya zamo wani muhimman karfi na ingiza nasarar samar da duniya mai mabanbantan tasiri, wadda za ta wanzu bisa daidaito da adalci, da kuma tsari mai game dukkanin sassa, da tattalin arziki da dukkanin duniya za ta ci gajiyarsa. Kasashe mambobin BRICS, sun yi aiki tukuru wajen ingiza tsarin cinikayya da kudaden juna, da gina tsarin hada-hadar kudade mai zaman kansa,...
“Ni na san fina-finan da aka haska a gidajen Gala da aka samu fiye da Naira miliyan daya a rana daya, wasu kuma har miliyan biyu, yanzu idan ka duba tun daga Kano har Nijar za ka dinga ganin gidajen Gala, haka zalika daga nan Kano har zuwa birnin Legas ma akwai su, saboda haka; me zai hana mu rika amfani da wannan dama wajen fadada adadin kudaden shiga da wannan masana’anta mai albarka take samu? Daga karshe, ya bukaci hadin kai daga dukkanin wasu masu ruwa da tsaki, wajen ganin wannan haka ya cimma ruwa. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga...
Rahotanni daga kudanci Lebanon sun ce, sau uku jiragen yakin HKI su ka kai hare-hare a kan gidajen mutane da hakan ya yi sanadiyyar shahadar mutum daya da kuma jikkatar wasu da dama. A garin Shaqra’dake yankin Bint-jubail, jiragen sama marasa matuki sun kai hare-hare da ya yi sanadiyyar jikkatar mutane biyu da raunuka, kamar yadda ma’aikatar kiwon lafiya ta Lebanon ta sanar. Har ila yau wani jirgin maras matuki na abokan gaba ya kai wani harin akan wata mota a yankin “Safful-Hawa” da hakan ya yi sanadiyyar shahadar mutum daya. A garin Shab’a kuwa ‘yan sahayoniyar sun kai hari akan wani gida, wanda ya yi sanadiyyar jikkatar mutanen dake cikinsa. Majiyar asibiti a garin Marja’iyyun ta ce an kai...
Dakarun kare juyin musulunci na Iran sun fitar da bayani a lokacin tunawa da sace jami;an diplomasiyyar Iran 4 a birnin Beirut, wanda ya kunshi cewa: Ya zama wajibi ‘yan sahayoniya su kwana da sanin cewa; Duk laifukan da su ka aikata a baya za a yi musu sakamako a kansa,kuma duk wani sabon wuce gona da iri, zai gaggauta zuwa karshensu ne.” Sanarwar ta kuma ce: Muna tunawa ne da zagayowar cikar shekaru 42 daga wancan aikin ta’addanci, da a yanzu kwanaki kadan ne su ka wuce na kawo karshen yakin da HKI da Amurka su ka kallafa mana na tsawon kwanaki 12. Yaki ne wanda martani mai karfi da jamhuriyar musulunci ta Iran ta mayar yake kara fito...
Wasu ƙungiyoyin mata a ƙauyukan Bendeghe-Ekiem da Abiya da ke Ƙaramar Hukumar Etung, a Jihar Kuros Riba, sun yi barazanar gudanar da zanga-zangar tsirara idan gwamnati ba ta janye ƙudirin sayar da gonakin koko ba. Matan sun ce wannan shawara da gwamnati ta ɗauka ba su aminta da ita ba, domin gonakin koko su ne tushen rayuwarsu, wanda da su suke cin abinci, suke biya wa ’ya’yansu kuɗin makaranta. Kwankwaso ba zai yi mana takara a 2027 ba — NNPP Mutanen unguwa sun kama masu ƙwacen waya a Kano Aminiya ta samu rahoton cewa gwamnati na shirin sayar da hannun jarinta a wasu manyan gonakin koko da ke wannan yanki, wanda hakan ya fusata matan da sauran al’ummar ƙauyukan da...
Babban magatakardar kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon Sheikh Na’im Kassim ya mayar da martani ga wadanda suke son, kungiyar ta mika makamanta, yana mai cewa; Ku fara da neman makiya su fice daga cikin Lebanon, domin babu hankali ace ba ku cewa komai akan ‘yan mamaya,ya zamana kuna neman wanda yake gwgawarmaya ya ajiye makamansa.” Sheikh Na’im Kassim ya kuma ce: Duk wanda ya amince da mika wuya, ya yi, amma mu ba za mu laminta da hakan ba. Mu almajiran makarantar Imam Hussain ( a.s) ne da yake cewa: Ba Za Mu Taba Lamunta Da Kaskanci Ba.” Sheikh Na’im Kassam ya ce: Wadanda suke jingina da kasashen waje, suna kuskuren lissafi, domin masu gwgawarmaya ba su ganin wani kwarjinin...

Wang Yi Da Takwaransa Na Ghana Sun Aikewa Juna Sakon Murnar Cika Shekaru 65 Da Kulla Dangantakar Diplomasiyya A Tsakanin Kasashensu
A yau Asabar ne ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi da takwaran aikinsa na kasar Ghana Samuel Okudzeto Ablakwa, suka aikewa juna sakon murnar cika shekaru 65, da kulla dangantakar diplomasiyya a tsakanin kasashen biyu. A cikin sakonsa Wang Yi ya bayyana cewa, cikin shekaru 65, an raya dangantaka tsakanin Sin da Ghana yadda ya kamata, kana an karfafa imani da juna kan harkokin siyasa, tare da samun manyan nasarori a hadin gwiwarsu ta fannoni daban daban. Kazalika, sassan biyu sun goyi bayan juna a fannin kulawa da harkokin kasa da kasa. Wang Yi ya ce, ana fatan yin kokari tare da minista Ablakwa, wajen kara fadada mu’ammala a tsakanin ma’aikatun harkokin wajen kasashen biyu, da goyon bayan juna,...
Sunana Hassana Yahaya Iyayi (Maman Noor) daga Jihar Kano: Gani suke ai in su nuna suna samu kamar matan nasu za su dora musu hidima da yawa, sun gwamma ce su bar matansu da wahala. Wani ma dan rashin imani kokari yake ita matar ta ciyar da shi alhalin yana da damar sa, shi ya sa ko yaran wani lokaci in suka taso komai na mahaifiyarsu sai daga baya ya zo ana da-na-sani mara amfani a lokaci da ba shi da amfani. Rashi tausayi ne kawai kuma kusan yanzu ma kaso casain na maza haka suke, ka so daya ne suke kyautatawa iyalansu. Kalubale babba ma kuwa shi ya sa sam! yanzu auren ma ba ya karko, karshe a jefa...
Jam’iyyar NNPP, ta bayyana cewa Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, wanda ya yi mata takarar shugaban ƙasa a 2023, ba zai tsaya takara a 2027 ba. Shugaban jam’iyyar na ƙasa, Dokta Agbo Major, ne ya bayyana haka a wata sanarwa, inda ya mayar da martani kan wata magana da Buba Galadima ya yi. Tinubu ko ɗansa zai naɗa shugaban INEC, APC sai ta faɗi zaɓen 2027 — Dalung Tsadar rayuwa ta sa ’yan Nijeriya na siyan abincin da ya lalace Galadima, ya ce har yanzu Kwankwaso yana cikin NNPP kuma zai tsaya takara a 2027. Galadima ya shaida wa manema labarai cewa: “Babu wani tabbaci da ke nuna cewa Kwankwaso yana shirin komawa APC. Za mu ci gaba da zama a...
Yadda za’a hada: Asamu biredi mai yanka-yanka a shafe shi da bota a ajiye a gefe. Sai a zuba mai a cikin karamin kaskon miya sai a zuba yankakkiyar albasa a dan soya na minti biyu, sai a zuba jajjagagen su attaruhu din nan a ci gaba da soyawa. A zuba kayan kamshi da kayan dandano, sai a zuba yankakken kabeji. Idan aka tabbatar duk sun soyu sai a dauki kifin gwangwani a tsiyaye man cikinsa sai a faffasa shi a zuba a kai a ci gaba da juyawa har komai ya hade jikinsa. Akunna injin gasa buredi, sai a dauko wannan buredi mai yanka-yanka wanda aka shafa bota a jiki sai a zuba wannan hadin su kifin nan a...
Idan ko tana wannan kazar-kazar din to dukkanin jikinta budewa yake yi. Don haka idan budurwa ta yi aure kuma ta kasance mai irin wannan dabi’a shi ne sai ki ga an sami matsala da miji yana zarginta da ko tana yawon banza tun da bai same ta a matsayin wacce ba ta taba aure ba. Nan kuwa ba haka bane, yawan tsalle-tsalle ne ya jawo a yayin al’ada. Idan kuma matar aure ce to sai ka ga jikinta ya sake budewa, idan ta gama al’ada ta koma turaka sai ki samu maigida bai damu da ya rika waiwayarta ba saboda a madadin jikinta ya matse a a sai ma ya kara budewa da yayi. Don haka idan har kina...
Kungiyar Kananan Hukumomin Nijeriya (ALGON) reshen Jihar Kaduna, ta mika sakon taya murna ga Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, bisa lambar karramawa ta CON da shugaban kasa ya yi masa ado da ita, wacce ke matsayin wata alamar girmamawa a Jamhuriyyar Nijeriya ta Hudu. Wannan karramawar, wata alama ce a sarari ga sadaukarwar mai girma gwamna, da gagarumin nasarorin da ya samu a hukumance, da kuma jagoranci mai tsari da yake kai domin ci gaba da tsara tafiyar dimokuradiyyar kasa. Dalilin Kwararru Na Bukatar Kafa Cibiyoyin Bincike Kan Nau’ikan Dabbobi A Nijeriya Abin Da Ya Sa Ilimi Yake Da Muhimmanci Ga Rayuwar Al’umma (8) Wannan na kunshe ne a cikin wata takarda dauke da sa hannun sakataren yada labarai...
Salim Sani Shehu Jam’iyyar NNPP ta bayyana a hukumance cewa tsohon ɗan takararta na shugaban ƙasa a zaɓen 2023, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ba zai sake yin takarar shugaban ƙasa karkashin jam’iyyar a zaɓen 2027 ba. Shugaban jam’iyyar na ƙasa, Agbo Major, ne ya bayyana hakan a ranar Asabar yayin da yake mayar da martani ga kalaman Buba Galadima, wanda ya ce Kwankwaso zai ci gaba da zama cikin jam’iyyar kuma zai tsaya takarar shugaban ƙasa a 2027. Major ya ce jam’iyyar ta riga ta kori Kwankwaso da Galadima bisa zargin aikata laifukan cin amanar jam’iyya, don haka ba su da ikon magana da sunan NNPP, balle su wakilci jam’iyyar a a duk wani sha’anin siyasa. “Tun da dadewa NNPP...
“A kowane mako, muna karbar yara fiye da 100 da ke fama da cutar maleriya. Sannan kuma, mafi yawancin lokaci; ba a kawo su asibiti, sai cutar ta tsananta”, in ji likitan. – Ciwon ciki da amai da gudawa (kwalera): Lokacin damina na kawo yawan samun gurbataccen ruwa, wanda ke haddasa cututtuka kamar ciwon ciki, amai da gudawa da kuma zazzabin taifod. Wannan na yawan shafar yara, musamman ‘yan kasa da shekara biyar. Dakta Ahmad ya kara da cewa, “Yara na da rauni a garkuwar jikinsu, sannan kuma idan suka kamu da gudawa, jikin nasu na rasa ruwa cikin sauri, har ta kai ga samun mace-mace.” -Kaikayi da kurajen fata: Likitan ya ce, lokacin damina na matukar kawo danshi,...
Tsadar rayuwa ta sa ’yan Nijeriya amfanin da kayayyakin da wa’adin amfani da su ya ƙare, lamarin da ya jefa mutane da dama cikin mawuyacin hali. Wani da ya samu kansa a cikin irin wannan hali shi ne Bitrus da ke Maidugurin Jihar Barno, wanda bayan kammala aikinsa na yau da kullum gab da almuru, ya koma gida a gajiye, ga kuma yunwa, inda ya ji cikinsa ya fara ƙugi. Kawai sai ya garzaya wani ɗan shago a bakin hanya ya sayo ƙaramar robar madarar yogot da kuma biskit domin rage yunwar da ta taso, kafin ya ci abincin dare. Sayen su ke da wuya, ya buɗe robar ya fara kwankwaɗar madarar, yana haɗawa da biskit ɗin a hanya, kafin...
Wacce irin gudunmwa kafofin samun ilimi suke badawa ta yadda za a samu hanyar kara ilimi A kokarin da ake yi na yadda za a samar da dama wadda kowa zai iya samun ilimi mai kuma inganci,ta kuma kafofin sadarwa na zamani. Hanyoyin koyo da kafofin sadarwa na zamani,kamar digirin da ake yi saboda yin karatun digiri ta kafar sadarwa ta zamani,da kuma a kasnce kamar ana cikin aji ne,saboda a ba dalibai wata dama wadanda kuma suka kasance daga wuraren da suka bambanta, manufa anan itace yadda suka zo daga wurare daban daban.Rin wannan ci gaban wanda ya kan kasance ga mutane ko al’umma daban daban,wadanda zasu iya fuskantar bambanci saboda daga wurin da suka fito, lamarin kudi,ko kuma...

Al’ummar Iran Ba Zasu Amince Da Ci Gaba Da Zaman Tattaunawa Da Amurka Ba Saboda Fushin Da Suke Ciki Na Kai Musu Hari
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran ya bayyana cewa: Babu wanda ko da a kuskure ya yi magana a kan tattaunawa da Amurka saboda tsananin fushin da al’ummar Iran ta yi Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran Ismail Baqa’i ya ce dangane da tattaunawar da aka yi da Amurka, “A halin yanzu al’ummar Iran suna cikin fushi matuka, ta yadda babu wanda ya isa ya yi magana kan batun gudanar da zaman tattaunawa da Amurka ko harkar diflomasiyya.” A cikin wata hira da gidan talabijin na Sky News, yayin da yake mayar da martani kan wata tambaya kan shirin nukiliyar Iran biyo bayan harin wuce gona da iri da Amurkawa da ‘yan sahayoniyya suka kai kan cibiyoyin makamashin nukiliyar Iran, Baqa’i ya...
Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran ta jaddada cewa Ta’addancin yahudawan sahayoniyya kan Iran laifi ne na yaki da ya zama wajibi duniya ta yi mata hukunci a kai Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Ismail Baqa’i ya yi kira da a dorawa mahukuntan yahudawan sahayoniyya alhakin munanan laifukan da suka aikata a kan al’ummar Iran, musamman a lokacin da ake ci gaba da kai hare-hare a birnin Tehran fadar mulkin kasar da sauran garuruwan kasar ta Iran. A wani sakon da ya wallafa a dandalin X a yau Asabar, Baqa’i ya ce, “Harin da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta kai a asibitoci da kurkukun Evin a ranar 24 ga Yunin wannan shekara ta 2025, wanda ya yi sanadin shahadar fararen hula...

Kungiyar Hamas Ta Sanar Da Matsayinta Kan Shirin Dakatar Da Bude Tsakaninta Da Gwamnatin Mamayar Isra’ila
Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas ta sanar da cewa: Ta gabatar da martani mai kyau ga shawarar dakatar da bude wuta tsakaninta da gwamnatin mamayar Isra’ila Kungiyar Hamas ta sanar da kammala tuntubarta tare da gabatar da kyakkyawar amsa ga sabuwar shawarar neman dakatar da bude wuta, inda ta bayyana shirinta na nan take na yin shawarwari kan tsarin aiwatarwa. Kungiyar gwagwarmayar Musulunci a Falastinu ta Hamas ta sanar a yammacin jiya Juma’a cewa ta kammala shawarwarin cikin gida da kuma tuntubar wasu bangarori da dakarun Falasdinawa dangane da sabuwar shawara da masu shiga tsakani suka gabatar na dakatar da hare-haren wuce gona da iri kan al’ummar Falasdinu a zirin Gaza. Kungiyar ta yi nuni da cewa ta mika martanin...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Al’ummar yankin Bachirawa a Jihar Kano sun yi ta maza sun cafke wasu matasa biyu da ake zargi da ƙwace waya a unguwar a yayin da ɓata-garin suke tsaka da ƙwacen. Matasan dai sun tare wata mata ce a unguwar suka ƙwace mata waya, wanda hakan ya sa mutanen yankin suka yi kansu tare da kama su. An samu nasarar karɓe wayar da suka amsa tare da ƙwace makaman da aka samu a hannunsu. Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ne ya sanar da haka bayan al’ummar sun miƙa waɗannan matasa ofishin ’yan sanda a ranar Juma’a.
“Wannan aiki ne, wanda za a iya cewa; tamkar a yanzu ne muka fara dora damba a kansa”, a cewar shugaban. Haka zalika, shugaban ya kuma sanar da wadanda suka halaccin taron kaddamar da shirin tabbacin cewa; wadannan ayyuka na noman zamani, za su kara taimakawa wajen kara samar da ayyuka a fannin aikin noma sama da 2,000. Ya ci gaba da cewa, kayan za su kuma taimaka wajen kara ayyukan masana’antun kasar da samar da damar gudanar da yin bita da kuma kwararrun kayan aikin noma 9,000. Shugaban ya jaddada muhimmancin yin amfani da kayan aikin noma na zamani, wanda hakan zai taimaka wa manoman wannan kasa. Har ila yau, ya kuma yi nuni da cewa; kaddamar da wannan...
An fara tuhumar tsohon ɗan ƙwallon Arsenal, Thomas Partey da laifuka biyar da suka haɗa da fyaɗe da kuma cin zarafi, an bayar da rahoton cewa ya aikata laifukan ne a tsakanin shekarar 2021-2022, cewar ‘yansandan Birtaniyya. Daga cikin laifukan akwai fyaɗe akan wasu mata uku waɗanda ake tuhumarsa da cin zarafinsu ta hanyar tursasawa kan mace ta farko da ta biyu sai kuma laifin lalata da mace ta uku. ‘Yansanda a ƙasar Birtaniya sun ce ya kamata Thomas ya bayyana a Kotun Majistare ta Westminster a ranar 5 ga watan Agusta, tuhumar ta biyo bayan binciken da jami’an tsaro suka gudanar, wanda ya fara a watan Fabrairun 2022 bayan da ‘yansanda sun samu rahoton fyaɗen. Partey dai ya bar...
Miliyoyin Iraniyawa a ranar 8 ga watan muharram sun fito sanye da bakaken kaya da tunawa a bubuwan da suka faru a ranar kwanakin Asoora inda aka kashe Imam Hussain (a) jikan manzon All… Banda wannan raya kwanakin Ashoora ci gaba ne da nuna turjiya da kuma saukar da kai kan azzaluman shuwagabanni ko da ba tare da samun nasara a zahiri ba kuma nan kusa ba. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa an gudanar da taturrukan Ashoora a duk fadin Iran, kuma a yau Tasoo’a za’a ci gaba da fitowa har zuwa gobe a Ashoora randa Imam Hussain (a) tare da sahabbansa 72 suka yi shahada a hannun sojojin yazeed a Karbala a ranar 10...
Hukumar IAEA mai kula da ayyukan makamashin nukliya a kasar Iran ta bada sanarwan cewa ma’aikatan hukumar sun fice daga kasar a jiya Jumma’a bayan da gwamnatin kasar ta jingine aiki da ita, bayan hare-haren da HKI da kuma Amurka suka kaiwa cibiyoyin nuklliya na kasar da ke Fordo, Natanz da kuma Esfahan a yakin kwanaki 12 da suka dorawa kasar. Hukumar ta bada sanarwan cewa ma’aikatan hukumar a Iran suna cikin kasar a lokacin yakin kwanaki 12 kan Iran, kuma a jiya sun bar Tehran zuwa Vienna bayan da gwamnatin kasar ta jingine aiki da ita, kuma tuni sun isa birnin Vienna inda cibiyar hukumar take. A ranar Alhamis da ta gabata ne ministan harkokin wajen kasar Iran abbas...
Sheikh Na’in Kasem shugaban kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon ya bayyana cewa kungiyar bata bukatar Izini don kare kasar Lebanon daga makiyanta. Yama fadar haka ne ga wanda suka cika kunnen duniya kan cewa dole ne kungiyar ta mika makamanta ga gwamnatin kasar. Kamfanin dillancin labaran Tasnim ya nakalto Sheikh Kasim yana fada a wani jawabin da ya gabatar a ranakun Ashoora na Imam Hussain (a) ta kafar Bidiyo. Ya kuma kara da cewa wadanda suke maganar kungiyar Hizbullah ta mika makamanta ga gwamnatinsa kasar, ya fiye masu sauki su fadawa yan mamaya su fice daga kasar Lebanon su kuma dakatar da hare-haren ta’addancin da suke kawo mata. Ya kara jaddada cewa kungiyarsa zata ci gaba da rike makamanta sannan...
Kungiyar Hamas wacce take iko da zirin Gaza na kasar Falasdinu da aka mamaye, ta bada sanarwan cewa da ita da sauran kungiyoyi da suke gwagwarmaya da HKI kimani shekaru biyu da suka gabata, sun amince da batun tattaunawa da kuma tsagaiuta budewa juna wuta wanda masu shiga tsakani suka gabatar. Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya bayyana cewa, shugaban kasar Amurka Donal Trump ya ce, wai HKI ta amince da shawarar budewa juna wuta da ya gabatar, amma kuma har yanzun ba’a bayyana dalla-dalla menen a cikin yarjeniyar ta kunsa ba. Har’ila yau gwamnatin kasar Masar ta ce tana kokarin ganin an samar da tsagaita budewa juna wuta na kwanaki 60.

Sojojin HKI Kimani 40 Ne Suka Halaka Ko Suka Jikata A Jiya Jumma’a A Yankin Shuja’iyya Na Birnin Gaza
Kungiyar Falasdinawa ta Jihadul Islami a Gaza, ta bada sanarwan halaka ko jikatar sojojin yahudawan Sahyoniyya 40 a gaza a wani tarko mai sarkakiyan da suka dana masu. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto majiyar Saraya Qudus” reshen soje na kungiyar Jihadul Islamim yana fadar haka a jiya Jumma’a. Daya daga cikin kwamnadojin dakarun ya bayyana cewa da farko halakar yahudawan ta faru ne a garin Gaza a kuma unguwar shuja’iyya. Inda da farko suka halaka sojojin yahudawa kimani 10 a cikin wani ginin da suka shiga cikinsa tare da amfani da makamai mai linzami, sannan a wani gidan Sannan waso sojojin kimani 20 sun halaka ko sun ji rauni a lokacin dakarun suka yi am,fani da...
‘Yan kasuwa sun yi hasashen cewa za a yi sabon tsarin farashin daga ranar Lahadi. Tun a ranar Talatar da ta gabata, wakilinmu ya lura cewa sauran masu gidajen man da masu shigo da kaya sun daidaita farashinsu domin nuna sabon tsarin farashin da ya biyo bayan tsagaita wuta tsakanin Isra’ila da Iran. Daga Naira 920, akasarin gidajen sun rage farashin zuwa matsakaicin farashin Naira 845 akan kowace lita. A cewar Petroleumprice.ng, RainOil, Pinnacle, Matrid, Emadeb, Wosbab da First Royal suna sayar da man fetur a kan Naira 845 a Legas ranar Talata. Hakazalika, NIPCO, Aipec sun sayar da mai akan Naira 850 akan kowace lita. A sauran defot da ke wajen Legas, irin su Warri da Fatakwal, ana sayar...