Shekaru 6: Don amfanin matasa mun inganta ilimi da noma — Gwamna Buni
Published: 30th, May 2025 GMT
A bikin cikarsa shekaru 6 cur yana mulkin Jihar Yobe, Gwamnan jihar Mai Mala Buni da aka gudanar a ranar Alhamis ɗin da ta gabata ya bayyana irin gagarumin ci gaban da aka samu akan harkokin ilimi da noma, inda ya ce akasarin waɗanda suka amfana a waɗannan fannoni guda biyu matasa ne.
Da yake jawabi a yayin wannan taro na bikin cikarsa shekaru 6 akan mulki da aka gudanar a babban ɗakin taro na Banquet da ke gidan gwamnatin Jihar a garin Damaturu tare da ma su ruwa da tsaki na Jihar.
Gwamnan ya bayyana ƙudirinsa na ci gaba da inganta harkokin da suka shafi matasa da kuma sauran fannonin da tuni gwamnatinsa ta yi nisa cikinsu kamar fannonin noma, kiwon lafiya, kasuwanci, tsaro da makamantansu.
Taron wanda ofishin mai baiwa Gwamna shawara na musamman kan harkokin talabijin, Rediyo da kafafen yaɗa labarai na zamani, Dakta Ibrahim Yabani, ya shirya yadda gwamnan ya amsa tambayoyin da wasu al’ummomin Jihar haɗe da ‘yan jaridu da ƙungiyoyin farar hula daga ƙananan hukumomin Jihar 17 suka yi wanda nan take Gwamnan ke amsa musu tambayoyin da suka masa kai tsaye.
A nasa jawabin, Gwamna Buni ya jaddada cewa taimakawa matasa na da matuƙar muhimmanci wanda kamar yadda ya ambata hakan ne ya ba shi ƙarfin gwiwar ƙara inganta harkokin ilimi wanda matuƙar matasa sun samu Ilimi to kuwa batun zaman banza zai kau kasancewar da sun samu Ilimi mai amfani gwamnatin nada ƙarfin gwiwar samar musu da aikin yi ta kowace irin fuska.
Gwamnan ya ce, aƙalla gwamnatin Jihar a duk wata takan kashe zunzurutun kuɗi sama da Naira miliyan 600 wajen ciyar da ɗaliban makarantun kwana waɗanda dukkansu matasa ne kuma gwamnatinsa ta tura matasa sama da 100 zuwa ƙasar Indiya don samun horo akan karantun likita wanda a yanzu haka matasan sun kammala sun dawo Jihar har an samar musu aikin yi a asibitocin Jihar.
Kan ɓangaren noma ma haka lamarin yake domin gwamnatinsa ta samarwa matasan kayayyakin gudanar da noman zamani, wadda kuma kwalliya tuni ta biya kuɗin sabulu.
Haka nan ta ɓangare tsaro nan ma haka lamarin yake domin gwamnatin ta a kullum takan yi abin da ya dace dangane da harkokin na tsaro musamman ta wajen samarwa jami’an tsaron Jihar haɗe da na Sibilyan JTF kayan aikin da suka haɗa da motocin sintiri da sauransu don ganin an daƙile barazanar da masu tada ƙayar baya ke yi ga al’ummar Jihar.
Ta fuskar gina titunan karkara ma gwamnatinsa ba ta yi ƙasa a gwiwa ba kasancewar yana da matuƙar muhimmanci wajen harkokin inganta kasuwanci, aikin noma haɗa kan al’umma musamman a ƙananan hukumomin Potiskum da Damaturu da Nguru da Gashua da Geidam da aka gina musu hanyoyin mota don ƙara alatu a garuruwan da kuma gina hanyoyin karkara a ƙananan hukumomin Jihar.
Da yake amsa tambayoyi daga mahalarta taron, Buni ya bayyana cewa, yawan gina hanyoyin mota ba wai rage tsadar sufuri ba ne, har ma yana ƙara haɓaka tattalin arzikin yankunan gaba ɗaya ta hanyar sauƙaƙawa manoman kawo amfanin gonakinsu zuwa kasuwannin Jihar.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Gwamna Buni Gwamnan Jihar Yobe harkokin ilimi da noma
এছাড়াও পড়ুন:
ALGON Ta Jihar Jigawa Za Ta Hada Gwiwa Da NUJ Don Inganta Kwarewar Aiki
Ƙungiyar Shugabannin Ƙananan Hukumomi ta Jihar Jigawa (ALGON) ta yi alkawarin kafa kyakkyawar haɗin gwiwa da ƙungiyar ‘yan jarida ta Najeriya (NUJ) reshen jihar, domin inganta ƙwarewar jami’an hulɗa da jama’a a fadin jihar.
Shugaban ALGON, Farfesa Abdurrahman Salim ne ya bayyana hakan yayin da ya karɓi shugabannin NUJ a wata ziyarar girmamawa da suka kai masa a sakatariyar ALGON da ke Dutse, babban birnin jihar.
Farfesa Salim ya jaddada muhimmancin yada bayanai a harkokin mulki da kuma isar da ayyuka ga jama’a, yana mai cewa samun ingantacciyar sadarwa na da matuƙar muhimmanci.
A cewarsa, bai wa jami’an hulɗa da jama’a horo da ƙwarewa zai taimaka wajen sauƙaƙe isar da sahihan bayanai ga al’umma.
Farfesa Salim ya tabbatar wa NUJ da cikakken goyon baya da haɗin gwiwar ALGON wajen ƙarfafa ƙwarewar jami’an bayanai, domin su daidaita da sauye-sauyen da ke faruwa a duniyar kafafen yaɗa labarai.
Tun da farko, Shugaban NUJ na jihar Jigawa, Kwamared Isma’il Ibrahim Dutse, ya ce shugabannin ƙungiyar sun kai ziyarar ne domin neman haɗin kai da goyon baya daga ALGON.
Ya ce NUJ ta yi amanna cewa sadar da bayanai na da matukar muhimmanci wajen tafiyar da mulki da kuma isar da ayyuka ga jama’a.
Usman Mohammed Zaria