Tinubu ya ɗaga darajar Kwalejin Kimiyya ta Kabo Zuwa Jami’ar Fasaha ta Tarayya
Published: 28th, May 2025 GMT
Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da ɗaga darajar Kwalejin Kimiyya da Kere-kere ta Tarayya da ke Kabo a jihar Kano, zuwa Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Tarayya, Kabo.
Wannan cibiyar ilimi, wacce aka kafa a shekarar 2022, yanzu ta zama jami’a ta uku ta gwamnatin tarayya a jihar, bayan Jami’ar Bayero Kano da kuma Jami’ar Ilimi ta Tarayya da aka assasa a kwanan nan, wacce aka sanya wa sunan marigayi Yusuf Maitama Sule.
Kano na kuma da jami’o’o’i biyu mallakin gwamnatin jiha.
Wannan ci gaban ya zo ne a daidai lokacin da ake fama da damuwa game da samar da kuɗaɗe ga manyan cibiyoyin da makarantu na gwamnati da kuma yawaitar sabbin da ake kafawa.
Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau I. Jibrin, wanda ya gabatar da ƙudirin dokar, ya yaba wa Shugaba Tinubu bisa amincewa da ƙudirin.
A yayin zaman Majalisar Dattawa na ranar Talata, an karanta wasiƙun shugaban kasa game da kafa sabbin jami’o’i a jihohin Kano, Akwa Ibom, da Oyo.
Sanata Barau, a cikin wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin yada labarai, Ismail Mudashir, ya bayar, ya ce sauya fasalin ya yi daidai da kyawawan halaye na duniya a fannin ilimi kuma yana da nufin inganta samun damar yin manyan makarantu.
Ya ce: “Kafa Jami’ar Kimiyya da Kere-kere ta Tarayya ta Kabo, yana nuna jajircewar Shugaban ƙasa wajen bai wa matasan Najeriya muhimman dabarun samun ƙwarewa a fannoni irin su kere-kere da basirar na’ura da fasahar sarrafa na’ura mai kwakwalwa, da kuma an fasahar tsaron intanet.”
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Barau
এছাড়াও পড়ুন:
An kama mabaraci da kuɗaɗen ƙasar waje a Ilorin
Hukumar jin daɗin jama’a ta Jihar Kwara tare da haɗin gwiwar Hukumar Gyaran Hali ta Najeriya sun kama wasu mabarata a titunan Ilorin, ciki har da wasu da aka samu da kuɗaɗen ƙasashen waje.
Daga cikin waɗanda aka kama akwai wani mabaraci mai suna Musa Mahmud daga Jihar Kano, wanda aka samu da takardar daloli.
Musa Mahmud ya shaida wa manema labarai cewa wani ne ya ba shi takardar Dala a Abuja.
Jami’ai sun bayyana damuwa kan yadda masu bara ke riƙe da kuɗaɗen da ba su dace da yanayin rayuwarsu ba.
Mutuwar majinyata: Asibitin Aminu Kano na roƙon KEDCO ya dawo da wutar lantarki Cire tallafin man fetur shi ne abin da ya dace —Sarki Sanusi II“Za mu bincika asalin waɗannan kuɗaɗen da kuma dalilin da ya sa suke da su,” in ji Adebayo Okunola, shugaban cibiyar gyaran hali a Jihar Kwara.
Jami’an gwamnati sun kwashe kusan mutane 40 daga wuraren da suka haɗa da Tipper Garage, Offa Garage, Tank da Geri Alimi Roundabout.
Jami’an sun ce bakwai daga cikin waɗanda aka kama an taɓa kama su a baya, amma sun koma tituna bayan an sako su.
Kwamishinar jin daɗin jama’a ta jihar, Dakta Mariam Imam, ta ce adadin masu bara da aka kama ya ragu sosai idan aka kwatanta da na baya, inda ta ce suna sauya dabaru don su guje wa kama.
Ta roƙi jama’a da su daina ba wa masu bara kuɗi kai tsaye, su maida gudummawarsu ta hanyar wuraren ibada da gidajen marayu.
Jami’an gyaran hali sun ce za a tilasta wa waɗanda aka kama su yi aikin tsaftace tituna a matsayin horo da kuma darasi.
Wasu daga cikin masu barar sun roƙi gwamnati da ta tausaya musu, ba su da wata hanyar rayuwa sai bara.