Gwamnatin Jigawa Za Ta Kulla Yarjejeniyar Hadin Gwiwa Kasar Indiya Don Habbaka Kiwon Dabbobi
Published: 29th, May 2025 GMT
A cikin wani mataki na ci gaba da sauya fasalin bangarorin noma da kiwo, Gwamnatin Jihar Jigawa na shirin kulla yarjejeniyar hadin gwiwa da daya daga cikin manyan kamfanonin kiwon kaji na kasar Indiya, wato Srinivasa Farms.
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan jihar Jigawa, Hamisu Mohammed Gumel, ya fitar.
Ya ce a wani bangare na ziyarar zuba jari a fannin noma da gwamnatin jihar ke gudanarwa zuwa kasar Indiya, tawagar jihar karkashin jagorancin Gwamna Malam Umar Namadi ta kai ziyara ofishin babban kamfanin Srinivasa Farms dake birnin Hyderabad domin tattauna damar hadin gwiwa da nufin farfado da harkar kiwon kaji a Jigawa.
Hamisu Mohammed Gumel ya kara da cewa ana sa ran za a rattaba hannu kan wata takardar yarjejeniyar fahimtar juna (MoU) a makonni masu zuwa domin kulla wannan hadin gwiwa, wanda zai bude kofa ga musayar ilimi, zuba jari daga masu zaman kansu, da ci gaba mai dorewa a bangaren kiwon kaji na jihar Jigawa.
Yayin da yake jawabi a lokacin ziyarar, Gwamna Namadi ya bayyana kwarin gwiwarsa kan tasirin wannan shiri.
Ya ce hadin gwiwar wani babban ci gaba ne wajen cika alkawurransa na sauya fasalin harkar noma, inda ya kara da cewa da fasaha ta zamani, horo, da hadin gwiwa irin wannan, Jigawa za ta zama cibiyar kiwon kaji ta kwarai a Najeriya.
Ziyarar tawagar zuwa kasar Indiya na daga cikin wani yunkuri na kasa da kasa wajen samar da hadin gwiwa, gogewa da kirkire-kirkire da suka yi daidai da Manufar Makomar Ci Gaban Tattalin Arziki da Samun Isasshen Abinci ta Matakai 12 da Jihar Jigawa ta tsara.
Usman Mohammed Zaria
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Indiya Jigawa jihar Jigawa hadin gwiwa
এছাড়াও পড়ুন:
Birgediya Janar Sabahi Fard Ya Jaddada Cewa: Duk Wani Sabon Hari Kan Iran Zai Fuskanci Martani Mai Gauni
Kwamandan rundunar hadin gwiwar hedikwatar tsaron saman Iran ya jaddada cewa: Duk wani sabon kuskure da ‘yan sahayoniyya suka aikata zai haifar da mummunan sakamako
Kwamandan rundunar hadin gwiwar hedikwatar tsaron saman Iran kuma kwamandan bataliyar Khatam al-Anbiya (s.a.w) Birgediya Janar Alireza Sabahi Fard, ya jaddada cewa: Duk wani sabon kuskure da yahudawan sahayoniyya za su sake yi, zai haifar da mummunan sakamako.
Birgediya Janar Seyyed Majid Mousavi, kwamandan rundunar sararin samaniyar Iran na dakarun kare juyin juya halin Musulunci ta Iran ya ziyarci hedikwatar hadakar tsaron sojojin saman na Khatam al-Anbiya, inda ya tattauna da Birgediya Janar Sabahi Fard, kan sakamakon arangamar da sojoji suka yi a baya-bayan nan da kuma hanyoyin inganta hadin kan tsaro.
A zaman taron, Sabahi Fard ya ce, “Tsarin tsaron saman kasar Iran ya shiga cikin yakin kwanaki 12 na baya-bayan nan da jajircewa da himma, tare da yin nasara ta hanyar hadin gwiwa da daukar matakin jihadi wajen dakile manufofin makiya yahudawan sahayoniyya tare da tilasta musu ja da baya. Ya bayyana karara cewa ci gaba da ta’addancin yana kara ta’azzara halin da ake ciki a cikin yankunan da aka mamaye, musamman a Tel Aviv da Haifa.”
Ya kara da cewa, “Suna dogara da karfin kasa wajen bunkasa na’urar tsaronsu, kuma jinin shahidansu ko daga sojoji ne ko farar hula, ba zai zuba a banza ba. Zai haifar da mummunan tasiri kan ‘yan mamayar yahudawan sahayoniyya. Kisan gillar da aka yi wa masana kimiyyar nukiliya da shugabannin tsaron Iran ba zai hana kasar cimma nasarorin fasaha, soja, da tsaro ba. Maimakon haka, za su yi aiki a matsayin wani gagarumin shiri na yaki da makiya.”