MDD: Yankin Gaza Ne Ya Fi Ko’ina Fama Da Yunwa A Doron Kasa
Published: 30th, May 2025 GMT
MDD ta yi gargadi akan yunuwar da mutanen Gaza suke fama da ita, sannan ta kara da cewa: Isra’ila ta hana shigar da kayan agaji, kuma rabin cibiyoyin kiwon lafiya na yankin sun daina aiki saboda rashin isar da kayan agaji daga waje.”
Ofishin MDD wanda yake kula da ayyukan agaji ne ya yi wannan gargadin, sannan ya kara da cewa: Yankin Gaza shi ne wurin da aka fi fama da yunwa a duniya baki daya.
Mai Magana da yawun ofishin na MDD ya ce: da akwai manyan motoci 600 da suke dauke da kayan agaji da su ka isa kan iyakar Gaza, amma asalinsu 900 ne da bisa wasu dalilai an hana su isa bakin iyaka.”
Haka nan kuma ya kara da cewa; Ya zuwa yanzu abinda su ka iya shigar da shi cikin yankin na Gaza, shi ne gari kadai, kuma shi ba a dafe yake ba, dole ne sai an dafa shi, alhali dukkanin kaso 100% na mutane Gaza suna fuskantar hatsarin yunwa.”
Da akwai mutane miliyan 2.4 da suke fama da yunwa a zirin Gaza saboda rufe kan iyakokin shigar da kayan abinci da HKI ta yi.
Sai dar har yanzu duk da rashin amincewa da hakan da kasashen duniya da kungiyoyin kasa da kasa suke yi, har yanzu HKI ta ki bude iyakokin shigar da su.
Amurka da HKI, sun fito da wani tsari na raba kayan abinci wanda kungiyoyin gwgawarmaya su ka bayayan da cewa; tarko na ci gaba da kashe Falasdinawa.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Kwamitin Tsaron Majalisar Dinkin Duniya Ya Fara Tattaunawa kan Masifar Zirin Gaza Na Falasdinu
Kwamitin tsaron Majalisar Dinkin Duniya ya fara tattauna masifar da ta faru a Gaza tare da jaddada kawo karshen kisan kiyashi yanki
Kwamitin tsaron Majalisar Dinkin Duniya ya gudanar da wani sabon zama domin tattauna batutuwan da suke faruwa a Gaza da kuma tabarbarewar al’amuran jin kai a yankin, inda ake ci gaba da yin kiraye-kirayen gaggauwa da kuma kira ga kasashen duniya da su dauki kwararan matakai na kawo karshen bala’in da ya biyo bayan yakin kisan kare dangi a yankin.
Majalisar Dinkin Duniya ta yi kira da a hanzarta dakatar da tilastawa al’ummar Gaza gudun hijira kamar yadda ta bukaci gwamnatin mamayar Isra’ila da ta ba da damar kai agajin jin kai ga al’ummar Zirin Gaza.
Mataimakin babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya mai kula da yankin Gabas, Mohamed Khaled Khari, ya tabbatar da cewa an kashe Falasdinawa kusan 300 a kusa da wuraren raba kayan agaji tun bayan jawabinsa na karshe a watan jiya.
“Mummunan halin da ake ciki a Gaza yana kara tabarbarewa tare da karuwar hasarar rayuka. Dole ne a daina yakin Gaza kuma a sako mutanen da aka yi garkuwa da su. Ayyukan da gwamnatin mamayar Isra’ila ke yi a Deir al-Balah ya haifar da karuwar ‘yan gudun hijira.”