Sin Na Maraba Da Kamfanonin Kasa Da Kasa Har Da Na Amurka
Published: 29th, May 2025 GMT
Yau Laraba, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning, ta bayyana a gun taron manema labarai na yau da kullum cewa, ma’anar dangantakar tattalin arziki da cinikayya tsakanin Sin da Amurka, ita ce cimma moriyar juna da kuma samun nasara tare. Kuma ra’ayin ba da kariya ga cinikayya ba zai samar da mafita ba.
Dangane da umarnin da gwamnatin Trump ta bayar ga ofishin jakadancin Amurka, da karamin ofishin jakadancin kasar na dakatar da sabuwar damar bayar da Biza ga daliban waje dake koyon ilmi a kasar kuwa, Mao Ning ta bayyana cewa, kasar Sin na fatan Amurka za ta kare hakki da muradun daliban sassan kasa da kasa, ciki har da daliban kasar Sin.
Bugu da kari, Mao Ning ta ce, domin kara saukaka mu’amalar al’ummun Sin da kasashen ketare, bangaren Sin na kira ga dukkan kasashe mambobin kungiyar GCC da su shigo Sin ba tare da Biza ba. (Safiyah Ma)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Xi: A Shirye Sin Take Ta Hada Hannu Da Canada Wajen Mayar Da Dangantakarsu Bisa Turbar Da Ta Dace
Yayin ganawarsa da firaministan Thailand, Shugaba Xi Jinping ya ce a shirye kasarsa take ta karfafa hadin gwiwa da Thailand kan dabarun samun ci gaba, tare kuma da gabatar da gogewarta na samun ci gaba a sabon zamani, kuma ya yi kira da a gaggauta gina layin dogo tsakanin Sin da Thailand da bunkasa hadin gwiwa a bangaren cinikin amfanin gona da tattalin arziki mai kiyaye muhalli da kuma kirkire kirkiren fasaha. (Mai fassara: FMM)
ShareTweetSendShare MASU ALAKA