Wike ya rufe ofishin FIRS da Bankin Access kan rashin biyan haraji
Published: 26th, May 2025 GMT
Hukumar Kula da Babban Birnin (FCTA) Tarayya ta rufe ofishin Hukumar Tara Haraji ta Kasa (FIRS) da kuma ginin Bankin Access kan rashin biyan haraji na sama da shekaru 25.
Daraktan Kula da Filaye na Hukumar FCTA, Chijioke Nwankwoeze, ya bayyana cewa hukumar bin ginin da bankin Access yake bashin harajin shekara 35, ofishin FIRS da ke unguwar Wuse Zone 5 kuma bashin harajin shekara 25.
Babban Ofishin na FIRS na daga cikin fitattun gine-gine da Hukumar Tara Kuɗaɗen Haraji na Babban Birnin ta rufe a safiyar Litinin, kan zargin rashin biyan haraji.
Sauran sun shafa da ginin Bankin Access da da ofishin kamfanin mai Total Energy da fitaccen otel din Ibro Hotel a unguwar Wuse, da sauran wurare 4,700 a Abuja.
Rikici ya barke a taron Atiku da kungiyoyin Arewa NAJERIYA A YAU: Tasirin Dangantakar Bangaren Zartarwa Da Na Majalisa A Kan TalakaChijioke Nwankwoeze, ya bayyana cewa ginin bankin Access da matakin ya shafa, mallakin wani wani kamfani ne, inda bankin ta kama haya.
Kazalika hukumar ta kwace izinin mallakar wasu filaye a wasu fitattun unguwanni saboda matsalar rashin biyar harajin.
Daraktan Kula da Bunƙasa Birnin Abuja, Mukhtar Galadima, ya jagoranci aikin ne bayan hukumar ta fitar da sanarwar rashin biyan harajin da ya kamata.
Ya bayyana cewa ana bin kamfanin Total harajin Shekara 10, wanda ya cika a watan Maris na 2025.
Fili mai lamba 2456 da ke titin Cadastral Zone A02, a unguwar Maitama, mallakin Kamfanin Rana Taher Furniture saboda rashin biyan harajin kas ana shekara 34.
Galadima ya bayyana cewa aikin zai ci gaba a sauran unguwannin Abuja, yana mai gargaɗin waɗanda abin ya shafa su gaggauta yin abin da aya kamata, ko su kuka da kansu.
Hukumar FCDA ta tsaurara matakan karbar haraji, musamman kam dokokin da suka shafi gine-gine da mallakar kasa a ƙarƙashin Minista mai ci, Barista Nyesom Wike.
Ya bayyana cewa wajibi ne masu filayen da hukumar ta kwace su tashi nan take, su bi hanyar da ta dace domin warware duk wata matsala.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Haraji rashin biyan haraji ya bayyana cewa
এছাড়াও পড়ুন:
PDP ta dakatar da Anyanwu da wasu ’yan tsagin Wike
Rikici a babbar jam’iyyar adawa ta PDP, na ƙara ƙamari, bayan da jam’iyyar ta dakatar da sakatarenta na ƙasa, Sanata Samuel Anyanwu, da wasu da ake ganin ’yan tsagin Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT), Nyesom Wike ne.
Mai magana da yawun jam’iyyar na ƙasa, Debo Ologunagba ne, ya sanar da dakatarwar bayan wani taro da Kwamitin Ayyuka na Ƙasa (NWC), ya gudanar a hedikwatar jam’iyyar da ke Abuja.
Zargin Kisan Kiristoci: Maganar Trump a kan Najeriya tsagwaron ƙarya ce — Shehu Sani Zaɓen Tanzania: Shugaba Samia ta yi tazarce da kashi 97 an ƙuri’uSauran da aka dakatar sun haɗa da Mai Bai wa jam’iyyar Shawara kan Harkokin Shari’a, Kamaldeen Ajibade (SAN); Sakataren Tsara Harkokin Jam’iyya, Umar Bature; da Mataimakin Mai Bai wa jam’iyyar Shawara kan Harkokin Shari’a.
Rahotanni sun bayyana cewa waɗanda aka dakatar ba sa halartar tarukan jam’iyyar.
An dakatar da su na tsawon wata ɗaya, sannan aka miƙa lamarinsu ga Kwamitin Ladabtarwa na jam’iyyar PDP domin gudanar da bincike.
Waɗanda aka dakatar ’yan tsagin Wike ne, kuma sun raba ƙafa a rikicin da jam’iyyar ke fuskanta tun bayan zaɓen 2023.
Idan ba a manta ba, a ranar Juma’a ne, wata Babbar Kotu a Babban Birnin Tarayya, ta dakatar da PDP daga shirin gudanar da babban taronta da aka tsara yi a Ibadan, Jihar Oyo, a ranar 15 da 16 ga watan Nuwamba, 2025.
Sai dai jam’iyyar ta ce za ta ɗaukaka ƙara kan hukuncin, kuma hakan ba zai hana ta ci gaba da shirye-shiryen gudanar da taron ba.
Wasu daga cikin ’ya’yan jam’iyyar sun ce rashin jituwa a PDO shi ne babban dalilin da ya sa aka kai ƙarar taron’ kotu.