HausaTv:
2025-05-27@19:32:12 GMT

Iran Ta Kira Yi Jakadan Faransa Akan Furucin Ministan Harkokin Wajen Kasarsa

Published: 26th, May 2025 GMT

Ma’aikatar harkokin wajen jamhuriyar musulunci ta Iran ta gayyaci jakadan kasar Faransa dake nan Iran domin nuna masa kin amincewa da furucin ministan harkokin wajen kasarsa da ya shafi batunci ga Iran.

Muhammad Tanhaye wanda shi ne mai kula da bangaren kasashen turai a ma’aikatar harkokin wajen jamhuriyar musulunci ta Iran,  ya bukaci Karin bayani a hukumance dangane da abinda ministan harkokin wajen Faransa Jean Nuel Barrot ya fada akan Iran a yayin bikin ” Cannes” na fina-finai a da wani daga cikin fina-finan Iran ya sami kyauta.

Har ila yau, Tanhaye ya yi suka akan yadda gwamnatin ta Faransa ta yi amfani da bikin fina-finan domin yada manufofinta na siyasa.

Haka nan kuma ya ce; Faransa wacce kasa ce mai goyon bayan ‘yan sahayoniya ba ta da  bakin fada akan batun da ya shafi kyawawan halaye da za ta yi Magana akan hakkin bil’adama balle ta soki wasu kasashe.

Jakadan na Faransa ya yi alkawalin mika sakon na Iran ga gwamnatinsa.

উৎস: HausaTv

কীওয়ার্ড: harkokin wajen

এছাড়াও পড়ুন:

Xi Jinping Ya Taya Murnar Bude Bikin Baje Kolin Kayayyaki Na Yammacin Sin

Adadin “nau’i uku na manyan kamfanoni 500” da suka halarci bikin baje kolin a bana ya kai 114, wanda ya kai kashi 55.6 bisa dari. Daga cikin su, akwai kamfanoni 61 dake cikin manyan kamfanoni 500 na duniya, adadin da ya karu da kashi 74.3 bisa dari kan na baje kolin da ya gabata. (Bello Wang, Safiyah Ma)

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Jamhuriyar Musulunci Ta Iran Ta Jaddada Cewa: Ba Zata Taba Amincewa Da Batun Dakatar Da Sarrafa Uranium Ba
  •  Fizishkiyan: Wajibi Ne A Kawo Karshen Ta’addanci A Kan Iyakokin Iran Da Pakistan
  • Iran ta yi kira da a karfafa hadin gwiwar tattalin arziki da kasashen Afirka
  • Shugaban Kasar Kenya: FOCAC Ya Samar Da Damammaki Ga Sin Da Afirka Wajen Inganta Hadin Kansu Da Samun Moriya Tare
  • Ministan Harkokin Wajen Iran Yace Faransa Bata Da Yencin ZarginWata Kasa Dange Da Kare Hakkin Bil’adama
  • Xi Jinping Ya Taya Murnar Bude Bikin Baje Kolin Kayayyaki Na Yammacin Sin
  • Ministan Gine-Ginen Hanyoyi Na Kasar Iran Tana Kasar Iraki Don Kula Da Aikin Layin Dogo
  • Rasha Ta Tarwatsa Makaman Ukiraniya A Tashar Jiragen Ruwa Ta Odessa
  • Afirka Ta Kudu Ta Zargi Shugaban Kasar Amurka Da  Rashin Dalili Akan Zargin Yi Wa Fararen Fatar Kasar Kisan Kiyashi