Majalisar Dokokin Jihar Kaduna ta amince da mutum biyu da Gwamna Uba Sani ya aike da sunayen su a tantance su a matsayin Kwamishinoni.

A cikin wata wasika da Gwamna Uba Sani ya aikawa Majalisar Dokokin, ya bukaci a amince da Farfesa Abubakar Sani Sambo a matsayin Kwamishinan Ilimin sai kuma Barrister Gloria Ibrahim a matsayin Kwamishinar Matasa da cigaban jihar.

Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Kaduna, RT. Hon. Yusuf Dahiru Liman ya bukaci sabbin kwamishinonin da aka amince da su, su yi amfani da kwarewar su domin farfado da bangaren Ilimi da bunkasa ci gaban matasa.

Da yake ganawa da manema labarai jim kadan bayan tantancewa da amincewa da shi a matsayin Kwamishinan Ilimi, Farfesa Abubakar Sani Sambo ya lashi takobin gudanar da sauye-sauye a bangaren Ilimi ta hanyar fadada damarmaki, da yin garambawul a gine-gine da kuma inganta sha’anin koyarwa a makarantun dake fadin Jihar Kaduna.

Haka nan ita ma Barr. Gloria Ibrahim ta bayyana kudirinta na aiwatar da hangen nesa na Gwamna Uba Sani, na shigar da matasa cikin harkokin Mulki da ci gaba, sannan ta sha alwashin yin aiki tukuru wajen samar da damarmaki ga matasan dake fadin Jihar Kaduna.

 

Shamsuddeen Mannir Atiku

উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa

কীওয়ার্ড: Kwamishinoni Majalisar Dokokin Jihar Kaduna

এছাড়াও পড়ুন:

Gwamnatin Zamfara Ta Kira Babban Taron Tsaro Tare Da Bayyana Sabbin Dabaru Na Yakar ‘Yan Bindiga.

A wani gagarumin mataki na karfafa yaki da rashin tsaro, gwamnatin jihar Zamfara ta gudanar da wani babban taron masu ruwa da tsaki a harkar tsaro a Gusau, da nufin karfafa hadin gwiwa tsakanin hukumomi da kuma kaddamar da sabbin dabarun yaki da ayyukan ta’addanci da masu aikata laifuka.

 

Taron wanda aka gudanar a Sakatariyar JB Yakubu wanda ofishin sakataren gwamnatin jihar (SSG) ya shirya, ya hada manyan hafsoshin tsaro, manyan jami’an gwamnati, da wakilan hukumomin tarayya domin duba halin tsaro da jihar ke ciki.

 

A cewar wata sanarwa da babban mataimaki na musamman kan harkokin yada labarai ga SSG, Suleman Ahmad Tudu, ya yi, an kira taron ne domin zurfafa hadin kai a tsakanin masu ruwa da tsaki domin kara inganta ayyukan da ake gudanarwa a fadin jihar.

 

Sakataren gwamnatin jihar, Malam Abubakar Nakwada, wanda ya jagoranci taron, daga bisani mataimakin gwamnan jihar, Mani Malam Mummuni, ya jadadda kudirin gwamnatin jihar na siyasa na maido da zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar.

 

A cewar sanarwar, yayin taron, mahalarta taron sun tsunduma cikin wani muhimmin nazari kan kalubalen tsaro da ake fama da su tare da daukar sabbin shawarwari guda goma da gwamnatin jihar ta bullo da su.

 

Ta ce an tsara matakan ne don karfafa nasarorin da aka samu a baya-bayan nan da kuma kara kaimi wajen yaki da ‘yan fashi.

 

Da yake jawabi, Malam Nakwada ya yabawa jajircewa da sadaukarwar jami’an tsaro da ke aiki a fadin jihar Zamfara.

 

“Gwamnatin Jiha ta yaba da irin sadaukarwar da ku da manyan jami’an ku suka yi wajen kare lafiyar al’ummarmu, a madadin Mai Girma Gwamna Dauda Lawal, ina mika godiyarmu ga sadaukarwar da kuke yi ba tare da gajiyawa ba.” Inji shi.

 

SSG ya jaddada bukatar daidaitawa da dabarun hadin gwiwa wajen tinkarar barazanar da ke tasowa, inda ya bayyana cewa, hazaka, kirkire-kirkire, da hadin kai na ci gaba da zama muhimmi wajen samun zaman lafiya mai dorewa.

 

Ya kara da cewa, “domin tunkarar kalubalen tsaro masu sarkakiya yadda ya kamata, dole ne mu ci gaba da daidaitawa, yin sabbin abubuwa, da kuma yin aiki tare ba tare da wata matsala ba fiye da kowane lokaci.

 

Malam Nakwada ya kuma bayyana bakin cikinsa kan yawaitar hare-hare a sassan jihar, inda ya mika sakon ta’aziyyar gwamnati ga iyalai da al’ummomin da abin ya shafa.

 

“A madadin gwamnatin jihar Zamfara, ina jajantawa duk wadanda hare-haren baya-bayan nan ya rutsa da su, ina kuma tabbatar wa ‘yan kasa cewa ba za mu yi kasa a gwiwa ba har sai an samar da cikakken zaman lafiya a tsakanin kowace al’umma,” inji shi.

 

Ya kuma kara nanata kudirin Gwamna Dauda Lawal na samar wa jami’an tsaro kayan aiki, da tallafin da ake bukata domin fatattakar masu aikata miyagun laifuka da ke barazana ga zaman lafiya da tsaro a jihar Zamfara.

 

A nasa jawabin rufe taron mataimakin gwamna Mani Malam Mummuni ya yaba da gudunmawar da masu ruwa da tsaki suka bayar tare da yin kira da a kara himma da hadin kai.

 

“Muna matukar godiya da kokarin da aka yi ya zuwa yanzu, amma dole ne mu kara himma. Bari mu tabbatar da kowane inci na jihar mu da muke so mu maido da fata ga jama’armu,” in ji shi.

 

Taron dai wani mataki ne mai jajircewa da gwamnatin Dauda Lawal ta dauka na magance matsalolin tsaro a gaba, yayin da gwamnatin ke kokarin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar Zamfara.

 

REL/AMINU DALHATU

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Gwamna Namadi Ya Amince Da Nadin Sabbin Sakatarori Guda Takwas
  • UNICEF Ya Bukaci Jihar Kano Ta Bai Wa Yara Muhimmanci A Kasafin Kudi
  • Gwamna Namadi Ya Sanya Hannu Kan Dokar Kafa Hukumar Hisba Ta Jihar Jigawa
  • Zhao Leji Da Wang Huning Sun Gana Da Shugaban Majalisar Dattijan Kasar Madagascar
  • Majalisar Dokokin Jihar Jigawa Ta Kai Ziyarar Gani Da Ido Kirikasamma
  • HOTUNA: An ƙaddamar da aikin sabunta ginin Majalisar Dokokin Bauchi
  • Yanzu-Yanzu: Majalisa Ta Amince Wa Tinubu Ciwo Bashin Dala Biliyan 21
  • PSC Ta Amince Da Ɗaga Darajar Jami’an ‘Yan Sanda 12 Daga Matakin CP Zuwa AIG, Da Sauransu
  • Gwamnatin Zamfara Ta Kira Babban Taron Tsaro Tare Da Bayyana Sabbin Dabaru Na Yakar ‘Yan Bindiga.
  • Mataimakiyar Shugaban Majalisar Dinkin Duniya Ta Jinjinawa Gwamnan Kano Bisa Ayyukan Cigaban Jihar