Tarayyar Turai Ta Yi Barazanar Karin Matsin Lamba Akan “Isra’ila”
Published: 30th, May 2025 GMT
Wasu jami’an diplomasiyyar turai sun yi wa gwamnatin Benjamin Netanyahu da cewa za ta fuskanci Karin matsin lamba idan har ba ta sauya halayyarta akan Gaza ba.
Jaridar “Washington Post” ta Amurka ta ambato jami’an diplomasiyyar turai suna cewa; sabon tsarin da ake yin aiki da shi na raba kayan agaji a Gaza, ya juya ya zama harigitsi kuma ana bude wuta akan mutane da hakan ya yi sanadiyyar jikkatar Falasdinawa da dama.
Har ila yau jami’an diplomasiyyar na turai sun ce, ko kadan ba su da aniyar bayar da kayan agajinsu ga masu tafiyar da tsarin da su ne Isra’ila da Amurka.”
Bugu da kari, majiyar diplomasiyyar ta tarayyar turai ta ci gaba da cewa; Hotunan masu ban tsoro da suke fitowa daga Gaza, sun kai musu iya wuya, ba za su iya ci gaba da jurewa ganinsu ba.”
A cikin kwanakin bayan nan dai kasashen turai sun fara yin matsin lamba akan HKI da ta bari a shigar da kayan agaji cikin yankin na Gaza da kuma yadda take ci gaba da kashe fararen hula da kuma rusau din da take yi mai yawa.
A karon farko, tun kirkirar HKI, kasar Jamus ta soki siyasar Tel Avi akan Gaza, da hakan yake nuni da yadda kasashen turai din suke kara matsin lamba.
Shugaban gwamnatin jamus Friedrich Merz ya ce; Harin da Isra’ila ta kai wa wata makaranta a Gaza, ya tashi daga karkashin fada da ta’addanci, ya zama wani abu daban.”
A can kasar ta jamus din dai jam’iyyar hamayya ta ” Green Party” ta ce; bai kamata a rika amfani da makaman kasar Jamus a yakin Gaza ba.”
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Dalibin Jami’ar Jos Ya Kashe Abokinsa Ya Binne Gawar A Rami
A wani bidiyo daban da PUNCH Metro ta gani a Facebook, wanda Mc Pee ya wallafa, wani mutum da ake zargin dalibi ne na jami’ar ya bayyana abin da ya faru.
A cewarsa, marigayin ya roki a bar shi ya rayu kafin daga bisani wanda ake zargin ya kashe shi.
Ya ce: “Nanpon ya riga ya yanke Peter a kumatunsa yayin da yake rokon a bar shi. Lokacin da muka shiga tsakani muka ce ya daina, sai ya yi barazanar yanka duk wanda ya kusanto shi.
“Da Peter ya ga ba ya sauraron rokonsa, sai ya rungume shi yana rokonsa da kuka.
“Mun fita neman taimako amma babu wanda ya amsa mana. Da Peter ya yi kokarin tserewa sai ya fadi, Nanpon ya kamo shi ya ci gaba da saransa da adda.”
Wani kwararren masanin tsaro da yaki da ta’addanci ya wallafa a dandalin D a ranar Lahadi cewa jami’an rundunar ‘yan sandan Jihar Filato sun kama wanda ake zargin.
Ya kuma ambaci majiyoyi da suka tabbatar da faruwar lamarin ta hanyar rahoton da aka samu daga Babban Jami’in Tsaro na jami’ar.
Ya rubuta cewa, “Rundunar ‘Yansanda ta Filato ta kama wani dalibi mai shekaru 23 na Jami’ar Jos bisa zargin kashe abokinsa sannan ya binne shi a rami mara zurfi a cikin dakinsa da ke kauyen Rusau a Karamar Hukumar Jos ta Arewa.
“Majiyoyi sun tabbatar da faruwar lamarin a ranar Lahadi a Jos, inda suka danganta da rahoton da aka samu daga Babban Jami’in Tsaron jami’ar.
“A cewar majiyoyin, wanda ake zargin mai suna Dabid Nanpon Timmap, dalibi a matakin shekara ta uku a jami’ar, ya kai wa Peter Mata Mafurai, mai shekaru 22, hari da adda, ya kashe shi a gidansa.”
Zagazola ya kara da cewa, bayan samun kiran gaggawa da misalin karfe 9:30 na safiya, DPO na sashin Laranto ya jagoranci tawagar ‘yansanda zuwa wurin, inda aka kama wanda ake zargin.
“Majiyoyin sun ce bincike ya nuna cewa wanda ake zargin ya binne mamacin a cikin rami mara zurfi da ya haka a cikin dakinsa. An tono gawar kuma an kai ta dakin ajiye gawarwaki na Asibitin koyarwa na Jami’ar Bingham domin yin binciken gawar (autopsy),” in ji shi.
Ya kara da cewa, an tsare wanda ake zargin yayin da ake ci gaba da bincike domin gano hakikanin dalilin kashe abokin nasa.
ShareTweetSendShare MASU ALAKA