Sojojin HKI Suna Ci Gaba Da Kai Wa Yankunan Gaza Hare-hare
Published: 27th, May 2025 GMT
Da safiyar yau Talata ne dai sojojin HKI su ka kai wa gabashin zirin Gaza da kuma Khan-Yunus hare-hare, bayan sa’oi daga kisan kiyashin da su ka yi wanda ya ci rayukan mutane 80.
Saandiyyar sabon harin na safiyar yau, wani karamin yaro ya yi shahada, a yankin al-karama dake Arewacin Gaza.
A daren jiya ma dai sojojin na HKI sun kai wasu hare-haren a unguwar ” Zaytun” dake gabashin Gaza.
Tashar talbijin din ‘al-Aqsa” ta bayar da labarin dake cewa; Unguwar Shuja’iyya’ da wasu unguwannin a gabashin birnin Gaza sun fsukanci hare-haren ‘yan sahayoniya daga manyan bindigogi.
Wasu hare-haren na ‘yan sahayoniya sun shafi Arewacin zirin Gaza da su ka yi sanadin rushewar gidaje, haka nan kuma asibitocin da su ka saura su ma sun fuskanci irin wadannan hare-haren.
Wasu kafofin Falasdinawa sun ce an kai gawar wani shahidi a yankin Deir-Balah.
Wasu Falasdinawan sun watsa bidiyo din gobarar da ta tashi saboda harin na ‘yan sahayoniya a jiya, wacce kuma har zuwa yau ba ta mutu ba.
Tashar talabijin “al-Aqsa” ta kuma bayar da labarin dake cewa; kananan jiragen ruwan HKI sun hude wuta a yankin “Mawasi” wanda yake cike da ‘yan hijira a yammacin Khan-Yunus.
Sa’oi kadan da su ka gabaci wannan harin, ‘yan sahayoniyar sun kira yi mutanen yankin da su fice daga gidajensu domin rushe su.
Likitocin da suke yankin sun sanar da tashar talabijin din ‘Al-jariza’ cewa mutane 80 ne su ka yi shahada, fiye da 30 daga cikinsu daga makarantar ‘Fahmi al-jarjawi’ da unguwar “Darj” cikin Birnin Gaza.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Sin: Katsalandan Cikin Harkokin Kamfani Da Netherlands Ta Yi Ya Kawo Tsaiko Ga Tsarin Masana’antu Da Samar Da Kayayyaki Na Duniya
Ya ce Sin tana maraba da kamfanonin dake fuskantar kalubale su tuntubi ma’aikatar ko hukumomi masu ruwa da tsaki, yana cewa, ma’aikatar za ta nazarci ainihin abubuwan dake faruwa da kuma bayar da damar fitar da kayayyaki ga wadanda suka cancanta. (Mai fassara: FMM)
ShareTweetSendShare MASU ALAKA