Jami’ar Jos Ta Samu Lambobin Zinare 14 A Gasar NUSSA, Yayin Da FUT Daura Ta Lashe Kofin Kwallon Kafa
Published: 31st, May 2025 GMT
Jami’ar Jos ce ta zama gwarzon gasar wasannin ma’aikatan jami’o’in Nijeriya karo na 14 (NUSSA), wadda Jami’ar Bayero da ke Kano ta karɓi bakuncinta. Jami’ar ta Jos ta lashe lambobin yabo guda 13, ciki har da Zinare 7, Azurfa 3 da Tagulla 3, wanda ya ba ta damar darewa saman teburin nasarori.
A matsayi na biyu kuma, Jami’ar Ahmadu Bello, Zaria, ta samu nasarar lashe lambobin yabo 12 – zinare 6, azurfa 3 da tagulla 3.
Babban abin da ya dauki hankali a gasar karshe da aka gudanar a ranar Juma’a, 30 ga Mayu, 2025, shi ne wasan karshe na kwallon kafa tsakanin Jami’ar Tarayya ta Harkokin Sufuri, Daura da Jami’ar Tarayya, Dutsinma. Bayan wasan ya kare 1-1, FUT Daura ta doke Dutsinma da ci 3-1 a bugun fenareti, inda ta lashe zinaren kwallon kafa.
Wannan gagarumar nasara da Jami’ar Jos ta samu na kara tabbatar da jajircewar jami’ar wajen bunkasa wasanni a tsakanin ma’aikata, da kuma karfafa dankon zumunci da kwarewa a tsakanin jami’o’in kasar nan.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: Wasanni
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamna Radda Da Makarrabansa Na Samun Kulawa A Asibiti Bayan Hatsarin Mota A Hanyar Daura
Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umar Radda, tare da wasu mutane goma sha biyu na samun kulawa a asibiti bayan tsira daga wani hadarin mota da ya faru a kan hanyar Katsina zuwa Daura, a Jihar Katsina.
Hatsarin ya faru ne sakamakon taho-mu-gama da wata motar haya kirar Volkswagen a kusa da Tashar Motoci ta KTSTA da ke Daura.
Duk da cewa hukumar kiyaye hadurra ta kasa (FRSC) ba ta fitar da sanarwar hukumance dangane da lamarin ba, shaidu da hotunan da aka dauka daga wurin sun tabbatar da cewa motocin biyu sun lalace matuka.
Shaidun gani da ido sun shaida wa Radio Nigeria cewa motar gwamnan ba ta cikin sahun motocin rakiyar gwamnati a lokacin da hadarin ya faru.
Daya daga cikin wadanda suka taimaka wajen daukar wadanda suka jikkata zuwa Asibitin Tarayya na Daura, ya shaida wa Radiyon Najeriya cewa dukkan fasinjoji tara da ke cikin motar hayar sun samu raunuka.
“Mun kai su Asibitin Gwamnati na Daura inda ake kula da su yanzu,” in ji shi.
A halin yanzu, Kwamishinan Yada Labarai na Jihar Katsina, Alhaji Bala Salisu Zango, ya ziyarci fasinjojin motar hayar da suka jikkata a Asibitin Gwamnati na Daura, inda ya bayyana cewa gwamnatin jihar za ta dauki nauyin dukkan kudin maganinsu.
Bakwai daga cikinsu sun samu raunuka kadan ne kawai, yayin da biyu kuma suka sami karaya.
“Gwamnatin Jihar Katsina za ta biya dukkan kudin maganinsu kuma za ta ci gaba da kula da lafiyarsu har sai sun warke.” in ji Zango.
Ya kara da cewa gwamnan ma yana cikin koshin lafiya, kuma tuni aka sallame shi daga Asibitin Tarayya na Daura.
“Na yi magana da shi ta waya ba da dadewa ba, yana cikin koshin lafiya. An kwantar da shi tare da sauran wadanda suka jikkata a Asibitin Tarayya na Daura, kuma an sallame shi bayan an tabbatar da cewa lafiyarsa ta daidaita.”
Haka kuma, wata sanarwa da Sakataren Watsa Labarai na Gwamna Radda, Malam Kaula Mohammed ya sanya wa hannu ta tabbatar da cewa gwamnan yana cikin koshin lafiya.
A wani faifan bidiyo da aka wallafa a kafafen sada zumunta, gwamnan ya bayyana cewa shi da sauran wadanda hatsarin ya rutsa da su suna cigaba da samun kulawa.
Daga Isma’il Adamu.