Sojojin Mamayar Isra’ila Suna Ci Gaba Da Kai Hare-Haren Wuce Gona Da Iri Kan Birnin Tul-Karam Na Falasdinu
Published: 25th, May 2025 GMT
Sojojin mamayar Isra’ila na ci gaba da kai hare-haren wuce gona da iri kan birnin Tulkaram da sansanoninsa da ke gabar yammacin kogin Jordan
Sojojin mamayar Isra’ila na ci gaba da kai hare-hare kan birnin Tulkaram da sansanoninsa a rana ta 119 a jere, da kuma sansanin Nour Shams a rana ta 106, a daidai lokacin da sojojin suke ci gaba da tsananta kai hare-hare kan yankuna Falasdinawa da kuma kma su tare da yinawungaba da su zuwa wuraren da baa san ko’ina ba ne.
Da sanyin safiyar Lahadi ne sojojin mamayar Isra’ila suka kai farmaki gidan Essam Odeh, sakataren kungiyar hadin kan iyalan shahidai da ke yankin kudancin Falasdinu, inda suka kama shi da diyarsa Sarah mai shekaru 20 bayan an yi musu tambayoyi. An saki Issam Odeh, yayin da sojojin mamayar suka tafi da diyarsa Sarah, da nufin matsawa dansa Amir ya mika kansa. Idan dai ba a manta ba, an sha tsare Issam Odeh, sannan kuma an tsare ‘ya’yansa biyu Muhammad da Isma’il a gidan yari na tsawon watanni ba tare da gurfanar da su a gaban kotu ba.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: mamayar Isra ila kai hare hare
এছাড়াও পড়ুন:
Jonh Kerry Ya Ce HKI Ba Zata Iya Wargaza Cibiyoyin Nukliyar Kasar Iran ba
Tsohon sakataren harkokin wajen kasar Amurka JohnKerry ya bayyana cewa HKI bata isa ta wargaza cibiyoyin makamacin nukliya na kasar Iran ba.
Kamfanin dilancin labaran IP na klasar Iran ya nakalto Kerry na fadar haka a jiya, ya kuma kara da cewa babban al-amari a cikin duk wani kokari na kauda cibiyoyin Nukliyar kasar Iran ita ce yakin da zai biyo bayan wannan kokarin,
Kerry yana magana ne don maida martani ga maganar cewa HKI tana shirin kai hare-hare ko yiyuwan ta kai harehare kan cibiyoyin nukliya kasar Iran idan ta ki amincea ta dakatar da tashe makamashiun uranium a cikin gida a tattaunawan da take da Amurka kan shirin nata.
Labarin ya kara da cewa wannan yana tabbatar da karfin sojen da kasar Iran take da ci abin lura ne hatta ga mahuntan kasar Amurka.