Aminiya:
2025-05-29@15:16:23 GMT

Bashin da ake bin Najeriya zai koma tiriliyan 162

Published: 28th, May 2025 GMT

Idan har Majalisar Dokoki ta Kasa ta amince da bukatar Shugaban Kasa Bola Tinubu ta neman sake ciyo sabon bashi, jimillar bashin da ake bin Najeriya a yanzu zai koma Naira tiriliyan 162.

A ranar Talata ce shugaban ya aike wa Majalisar Wakilai takardar neman ta sahale masa ya ciyo bashin, wacce shugaban majalisar, Abbas Tajuddeen ya karanta a zauren majalisar.

Abbas ya ce rancen na 2025–2026, ya kunshi Dala biliyan 21.5 (kimanin Naira tiriliyan 34) da Yuro biliyan 2.2 (kimanin Naira tiriliyan 3.96) da Yen na Japan biliyan 15 (kimanin Naira biliyan 164.7) da kuma Yuro miliyan 65 (kimanin Naira biliyan 116.79) a matsayin tallafi.

Tinubu zai ciyo bashin Naira tiriliyan 39 daga kasashen waje Kotu ta ci su El-Rufa’i tarar miliyan 900

Yana kuma neman cin bashin cikin gida ta hanyar bayar da takardun lamuni na Dala biliyan biyu, kimanin Naira tiriliyan 34.285, don biyan basussukan fanshon adashi gata da suka taru.

Tinubu ya nemi amincewa da bayar da takardun lamuni na Naira biliyan N757.98 a cikin gida domin biyan basussukan fansho da suka taru har zuwa ranar 31 ga Disamba, 2023.

Shugaban kasan ya bayyana cewa an tsara neman bashin ne don tallafa wa muhimman ayyukan a fannonin ababen more rayuwa, noma, lafiya, ilimi, da tsaro a dukkan jihohi 36 da Babban Birnin Tarayya.

Ya bayyana cewa bayar da takardun lamuni na Dala biliyan biyu ya yi daidai da Dokar Zartarwa ta Shugaban Kasa da nufin samar kuɗin domin farfado da darajar Naira da gudanar da muhimman ayyukan samar da ababen more rayuwa da samar da ayyukan yi.

Tinubu ya jaddada gaggawar buqatar wadannan kudade, yana mai nuni da tasirin cire tallafin mai da raguwar kudaden shiga na cikin gida.

Ya lura cewa hakan zai magance rashin bin tanade-tanaden Dokar Gyara Fansho a baya saboda matsalolin samun kuɗi, da nufin dawo da ƙwarin gwiwa a tsarin fansho da inganta jin daɗin tsofaffin ma’aikatan gwamnati.

Dukkan buƙatun guda uku an miƙa su ga Kwamitin Kula da Kuɗi na Majalisar don ɗaukar matakan majalisa na gaba.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Najeriya Naira tiriliyan kimanin Naira

এছাড়াও পড়ুন:

Ambaliyar ruwa ta kashe sama da mutum 50 a Neja

Mutanen da ya zuwa yanzu ba a kai ga tantance adadinsu ba sun rasa rayukansu sakamakon wata ambaliyar ruwa da ta afka wa garin Mokwa na jihar Neja.

Mazauna yankin sun kuma ce babbar hanyar da ta hada arewaci da kudancin Najeriya da ta bi ta yankin ita ma ambaliyar ta yanke ta.

Kodayake dai har yanzu babu cikakkun bayanai a kan ambaliyar, amma mazauna yankin sun kiyasta cewa mutanen da suka rasa ransu za su kai 50.

NEJERIYA A YAU: Sai Yaushe ’Yan Najeriya Za Su Ci Gajiyar Manufofin Shugaba Tinubu? ’Yar Najeriya ta tsinci miliyan 8.2 a Saudiyya ta mayar wa da mai su

Gidaje da sauran kadarori na miliyoyin nairori ne dai suka salwanta, yayin da wasu mazauna yankin kuma ke cewa adadin wadanda suka rasun ma zai iya wuce 50, sakamakon har yanzu akwai mata da kananan yara da dama da ba a san inda suke ba.

Aminiya ta gano cewa ambaliya ta biyo bayan wani mamakon ruwan sama da aka tafka na tsawon sa’o’i a daren Laraba, inda ya cinye gidaje yayin da mutane suke tsaka da barci.

Wani mazaunin yankin mai suna Mohammed Usman, a ce tuni har an tsamo gawarwaki da dama a cikin ruwa, amma har yanzu akwai wadanda ba a kai ga gano su ba, musamman a wuraren da gidajen suka nitse baki daya.

Daraktan Yada Labarai na Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Jihar Neja (NSEMA), Dr Ibrahim Audu Hussaini, ya tabbatar da faruwar ambaliyar ga Aminiya.

Ya ce har yanzu hukumar na kan aikin tattara bayanai da alkaluma kafin ta kai ga sanar da abin da ta gano.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Ambaliyar ruwa ta kashe sama da mutum 50 a Neja
  • Gwamnatin Gombe ta rattaba hannu kan kwangilar biliyan 48 na aikin zaizayar Kasa
  • Gwamnatin Tarayya Ta Kaddamar Ayukka 16 A Sakkwato
  • NEJERIYA A YAU: Sai Yaushe ’Yan Najeriya Za Su Ci Gajiyar Manufofin Shugaba Tinubu?
  • Kotu ta yanke wa Murja Kunya hukuncin dauri a gidan yari
  • Gwamna Uba Sani Ya Kammala Titin Unguwar Su El-Rufai
  • Tinubu na neman ciyo bashin Naira tiriliyan 39 daga kasashen waje
  • Tinubu Ya Nemi Amincewar Majalisa Kan Amso Bashin $21.5bn Da ₦757.9bn
  • NAJERIYA A YAU: Matsalolin Da Suke Tarnaki Ga Kananan Yara A Najeriya Da Hanyoyin Magance Su