Falasdinawa 30 sun yi shahada a Wani harin Isra’ila kan wata makaranta
Published: 26th, May 2025 GMT
Bayanai daga Falasdinu na cewa wani hari da jiragen yakin Isra’ila suka kai cikin dare a wata makarantar Gaza dake zaman matsugunni ga masu neman mafaka ya yi sanadin shahadar Falasdinawa 30, ciki har da yara da dama, a cewar jami’an kiwon lafiya da na fararen hula.
Da sanyin safiyar yau litinin ne sojojin gwamnatin Isra’ila suka kai hari a makarantar Fahmi al-Jarjawi da ke yankin Daraj na zirin Gaza, inda daruruwan iyalai da suka rasa matsugunansu daga garin Beit Lahia da ke arewacin kasar da Isra’ila ke fama da hare-haren bama-bamai suka samu mafaka.
Hukumar tsaron farar hula ta Gaza ta ce masu aikin ceto sun tsamo gawarwakinmutum 20 daga makarantar, ciki har da yara da dama.
A cewar majiyoyin yankin, wadanda harin ya rutsa da su sun hada da Mohammad al-Kasih, shugaban bincike na ‘yan sandan Hamas a arewacin Gaza, da kuma matarsa da ‘ya’yansa.
Ma’aikatar lafiya ta Falasdinu ta kuma bayar da rahoton cewa, wani hari ta sama da Isra’ila ta kai kan wani gini da ke titin Thawra a birnin Gaza jim kadan kafin harin makarantar.
A cewar ma’aikatar lafiya ta Falasdinu, kusan Palasdinawa 54,000 ne aka kashe tun fara fara farmakin Isra’ila a ranar 7 ga watan Oktoba, yawancinsu mata da yara.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Hukumar Kare Hakkin Bil’adam Ta MDD Ta Bukaci A Kawo Karshen Kissan Kiyashi A Gaza
Shugaban hukumar kare hakkin bil’adama na MDD ta bukaci kasashen duniya su takurawa HKI ta kawo karshen kissan kiyashin da take yi a gaza bayan hare-haren da ta kai a kan wata makaranta a unguwar Fahmi Aljarjawi a cikin birnin Gaza wanda ya kashe falasdinawa akalla 36.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Francesca Albanese tana fadar haka a shafinta na X a jiya Litinin. Ta kuma kara da cewa an kashe mutane da yawa, kuma an kashe yara da yawa. An kona su da ransu, a cikin makarantar inda suke mafaka a ciki.
Albanese ta hada da hotunan bidio wanda suke nuna irin yadda wuta take kona Falasdinawa a cikin makarantar, ta turasu a shafin nata. Ta kara da cewa dole ne mu tsaida wuta a gaza kuma falasdinawa su gafarta mana kan cewa mun kasa yin haka har abin ya kai wannan matsayin.