Fizishkiyan: Wajibi Ne A Kawo Karshen Ta’addanci A Kan Iyakokin Iran Da Pakistan
Published: 27th, May 2025 GMT
Shugaban kasar Iran wanda ya karbi bakuncin Fira ministan Pakistan da marecen jiya Litinin, ya bayyana cewa; Kasar Pakistan, makwabciyar jamhuriyar musulunci da muhimmanci, ta dubban shekaru.
Shugaban kasar ta Iran Mas’ud Fizishkiyan wanda yake Magana a lokacin taron manena labaru na hadin gwiwa da Fira ministan na Pakistan, ya kuma ce; Da akwai haduwar mahanga a tsakanin kasashen biyu akan batutuwa masu yawa da su ka shafi wannan yankin da kuma duniyar musulunci da kuma a fagen siyasar kasa da kasa.
Shugaba Mas’ud Fizishkiyan ya kuma ce: “A yayin ganawar da mu ka yi da dan’uwana Fira minisan Pakistan da tawagar da taek tre da shi, mun jaddada yadda za a bunkasa alaka ta siyasa, tattalin arziki da al’adu.”
Da yake yin ishara akan aiwatar da yarjeniyoyin da aka kulla a baya a tsakanin kasashen biyu, shugaban kasar ta Iran ya bayyana cewa: Bangarorin biyu za su aiwatar da yarjeniyoyin da su ka kulla a baya, kuma yana cikin abubuwan da mu ka tattauna akai.”
A nashi gefen, Fira ministan na kasar Pakistan Shahbaz Sharif ya yi godiya ga shugaban kasar ta Iran wanda a makwannin da su ka gabata ya kira shi, domin nuna damuwarsa akan halin da ake ciki a yankin-na rikicin kasar da Indiya.”
Haka nan kuma ya bayyana yadda kasar Pakistan ta sami nasara a yakin da ta yi da Indiya, ya kuma ambaci yadda al’ummar kasar ta Pakistan su ka nuna goyon bayansu ga sojojin kasar tasu.
Haka nan kuma bangarorin biyu sun nuna takaicinsu abinda yake faruwa a Gaza, tare da yin kira a kawo karashen yakin da shigar da kayan agaji, haka nan kuma hukunta ‘yan sahayoniyar da su ka tafka laifukan yaki.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Bida Poly ta kawo sojoji su kula da jarrabawar ɗalibai
Rikicin kwamitin gudanarwa da malaman Kwalejin Fasaha ta Tarayya da ke Bida (Bida Poly), ya ƙara ƙamari bayan da makarantar ta dakatar da ayyukan Kungiyar Malamai (ASUP) sannan ta kawo sojoji domin kula da jarrabawa da dalibai ke gudanarwa.
Ƙungiyar ASUP reshen kwalejin ta shiga yajin aiki mara wa’adi, domin neman a biya su alawus ɗin ƙarin aiki na watanni 18 da suka wuce.
Ƙungiyar ta umarci mambobinsu da kada su gudanar da jarrabawar zangon da ta fara ranar Litinin, 15 ga Satumba, 2025.
Wani ma’aikacin makarantar ya shaida wa wakilinmu cewa sojojin an gayyace su ne domin kare ɗalibai da wasu malamai daga shirin da ASUP ke yi na hana gudanar da jarrabawa.
’Yan bindiga sun kai wa sojoji hari a ranar da ake zaman sulhu An kama su kan satar zinarin Naira miliyan 110 a Kebbi“Ba wai don su gudanar da jarrabawar aka kawo sojojin ba, sai don su kare ɗalibai da malamai daga duk wani cikas. Amma abin mamaki shi ne, me ya sa aka kawo sojoji maimakon ’yan sanda ko Sibil Difens?” in ji shi.
Shugaban ASUP na kwalejin, Kwamared Kolo Joshua, ya tabbatar da komawar su yajin aiki, yana mai cewa gwamnati ta yi biris da haƙƙoƙin malaman.
“Shekaru biyu ke nan muna jurewa, amma yau malaman suna bin bashin watanni 18 na kuɗin ƙarin aiki.
“Duk da tattaunawa da saƙonni da muka aika, ba a ɗauki mataki ba. Sai ma aka dakatar da ƙungiya sannan aka fara tsoratar da shugabanninmu da tambayoyi. Wannan ya jefa malaman cikin rashin kuɗi da raguwar ƙwarin guiwa,” in ji shi.
Ya ce sai dai idan gwamnati ta biya hakkokin malamai da kuma ta koma kan tattaunawa ta gaskiya ne za a samu zaman lafiya a makarantar.
Wata sanarwa da Babban Sakataren Makarantar, Hussaini Mutammad Enagi, ya fitar, ta ce an dakatar da ayyukan ƙungiyar ne bisa dalilin “fargba da kuma rahoton tsaro mai tayar da hankali.”
Sai dai jami’in hulɗa da jama’a na makarantar, Malam Abubakar Dzukogi, ya musanta cewa sojoji aka kawo.
“Na zagaya duk cibiyoyin jarrabawa, ban ga sojoji ba. ASUP ne kawai suka shiga yajin aiki, sai makaranta ta ci gaba da gudanar da jarrabawar. Wannan lamari na farar hula ne, ba na soja ba,” in ji shi.