FCTA ta rufe hedikwatar PDP saboda rashin biyan haraji
Published: 26th, May 2025 GMT
Hukumar Kula da Birnin Tarayya (FCTA), ta rufe hedikwatar jam’iyyar PDP da ke unguwar Wuse a Abuja.
Lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 2:05 na ranar Litinin.
Wike ya rufe ofishin FIRS da Bankin Access kan rashin biyan haraji Ana zargin wani mutum da kashe ɗan maƙwabtansa a SakkwatoJami’an FCTA sun isa ginin tare da jami’an tsaro, inda suka rufe ofishin.
Wasu ma’aikata sun nuna rashin jin daɗinsu, bayan tafka sa-in-sa na tsawo mintuna 15, jami’an FCTA sun bar ma’aikata su fitar da motoci da kayayyakinsu kafin kulle ginin.
A makon da ya gabata, FCTA ta sanar da cewa za ta ƙwace sama da kadarori 4,700 a Abuja saboda rashin biyan haraji na tsawon shekaru 10 zuwa 43.
Waɗannan kadarorin suna yankunan Central Area, Garki, Wuse, Asokoro, Maitama da Guzape.
FCTA, ta ce mallakar waɗannan filaye ya koma hannun gwamnati.
Tun daga Litinin, gwamnati ta fara ƙwace su ba tare da la’akari da wanda ya mallaki kadarar ba.
Daraktan Sashen Kula da Ci Gaban Birnin Tarayya, ya ce za a rufe waɗannan gine-gine kuma ba za a bari kowa ya shiga ba.
Ya ƙara da cewa gwamnati za ta yanke hukunci kan yadda za a yi da su a nan gaba.
Daraktan Sashen Filaye, ya bayyana cewa babu wani hukuncin kotu da ya hana FCTA ɗaukar matakin da ta ke ɗauka a yanzu, don haka za su ci gaba da yin aikinsu.
Ya kuma ce suna tantance kadarorin da suka daɗe ba su biya haraji ba daga shekara ɗaya zuwa 10, kuma za su ɗauki mataki bayan sun kammala tantancewar.
Tun a watan Maris, 2025 FCTA, ta sanar da soke takardun mallakar filaye guda 4,794 saboda rashin biyan haraji, inda ta gargaɗi cewa za ta fara karɓe ikon mallakar filayen daga ranar Litinin.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Babban Birnin Tarayya Haraji Kadarori rashin biyan haraji
এছাড়াও পড়ুন:
Kaso 90 na ’yan bindigar da suka addabi Katsina ’yan asalin jihar ne – Radda
Gwamnan jihar Katsina, Dikko Radda, ya ce kimanin kaso 90 cikin 100 na ’yan bindigar da suka hana jiharsa sakat ba baki ba ne, ’yan cikinta ne.
Ya bayyana haka ne lokacin da ya bayyana a cikin shirin Sunrise Daily na gidan talabijin na Channels a ranar Talata.
Ya ce tuni gwamnatinsa ta kafa rundunar tsaro mallakin jihar mai suna Katsina Community Watch Corps, inda aka debi matasa daga yankunan da ke fama da matsalolin tsaron domin a dakile ta tun daga tushe.
DAGA LARABA: Shin Ko Zafin Nema Na Kawo Samu? Malaman firamare sun janye yajin aiki a AbujaKatsina dai na daya daga cikin jihohin Arewa maso Yamma da ke fama da matsalar ’yan bindiga, inda mutane dauke da makamai kan kai farmaki kan kauyuka su kashe mutanen gari sannan su dauki wasu domin karbar kudin fansa. Sai dai a ’yan kwanakin nan jihar ta dan samu saukin hare-haren.
A cewar Gwamnan, akasarin maharan ba baki ba ne, a yankunan danginsu suke, inda ya ce amfani da mutanen yankin na taka muhimmiyar rawa wajen shawo kan matasalar tun daga tushe.
Ya ce a sakamakon haka, an sami nasarar kama mutane da dama da ke samar wa da ’yan bindigar kayayyaki da kuma bayanan sirri.
Radda ya ce, “Ba wai cewa muke an ga bayan matsalar tsaro gaba dayanta ba, saboda har yanzu a kan samu hare-hare jifa-jifa, amma dai yanzu an samu sauki.
“A baya akwai wadanda suke tunanin gaba daya jihar ma ta koma hannun ’yan ta’addan saboda kashe-kashen da ake yi a ko ina. Amma wannan tunanin ya saba da abin da yake a zahiri.
“Dalilinmu na kirkirar sabuwar rundunar tsaro ta jiha shi ne mu taimaka wa sauran jami’an tsaro a ayyukansu. Mun dauki mutane daga dukkan yankunan da ke da matsalolin tsaro saboda su suka fi sanin yankunansu da ma mutanen cikinsa fiye da kowa.
“Mazauna wadannan yankunan sun san iyayen ’yan bindigar nan da kakanninsu, saboda ba baki ba ne. wannan ne sirrin samun nasararmu, har muke iya zuwa mu farmake su a har a maboyarsu. Dole sai da dan gari a kan ci gari,” in ji Gwamnan na Katsina.