Mai Martaba Sarkin Kazaure Ya Bukaci Alhazai Su Yi Addu’o’i Na Musamman Ga Kasarsu
Published: 27th, May 2025 GMT
An bukaci Maniyyatan Jihar Jigawa su yi addu’o’i ga jihar da kasa Najeriya domin samun zaman lafiya a yayin zaman su a kasa Mai tsarki.
Amirul Hajj na Jihar, Mai Martaba Sarkin Kazaure Dr Najib Hussaini Adamu yayi wannan kiran a lokacin da yake jawabi ga Maniyyatan Jihar a Kasar Saudi Arabia.
Amirul hajjin ya hori Maniyyatan da suyi addu’a tare da karkatar da zukatansu ga dabi’u nagari, inda ya bayyana cewar canza dabi’u tare da komawa ga Allah ne kadai hanyar da za’a bi don magance matsalolin da suka addabi kasa Najeriya.
Dr Najib Hussaini Adamu, yace Allah ya albarkaci Jihar Jigawa da ni’imomi da dama, a don haka ya bukace su da su kara karfafa addu’o’i.
Kazalika, Sarkin ya kuma yabawa tallafin da gwamnati jihar ta bayar domin tabbatuwar aiwatar da hajjin bana.
A don haka, yayi kira ga Maniyyatan da su yi wa gwamnatin Jihar jigawan addu’a.
Ya kuma bukace su da su zama masu bin dokokin kasar saudiyya, yana mai horan su da su zamo masu tsafta kuma jakadu nagari a ko ina musamman a zaman Muna.
Mai Martaba ya kuma kara jan hankulansu da su zama abin misali a wajen kula da tsaftar muhalli yana mai fatan Allah yasa ayi ibada lafiya a koma gida lafiya.
Usman Mohammad Zaria
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
এছাড়াও পড়ুন:
Xi Jinping Ya Halarci Kwarya-Kwaryan Taron Shugabannin APEC Na 32 Tare Da Gabatar Da Jawabi
Shugaba Xi ya kuma bayyana cewa, cikakken zama na 4 na kwamiti na 20 na JKS ya amince da shirin raya kasa na shekaru biyar-biyar karo na 15. Sin za ta yi amfani da wannan damar don ci gaba da gyare-gyaren tattalin arzikinta, da kuma fadada bude kasuwancinta mai zurfi ga ketare, ta haka za ta ci gaba da ba da sabbin damammaki ga yankin Asiya da Pasifik da sauran kasashen duniya ta hanyar zamanantar da al’ummarta. (Amina Xu)
ShareTweetSendShare MASU ALAKA