Tsaro Ya Inganta A Zamfara, In Ji Gwamna Lawal Yayin Tattakin Zaman Lafiya Na Tarihi A Jihar
Published: 30th, May 2025 GMT
Da yake jawabi ga ɗimbin mutanen da suka halarci wannan tattaki, Gwamna Lawal ya jaddada ƙudirin gwamnatinsa na kawar da duk wani nau’in miyagun laifuka a jihar, tare da mai da hankali sosai kan ‘yan bindiga.
Ya ce, “A yau mun fito dubunnan mu domin mu yi tattakin samun zaman lafiya, domin mu sanar da duniya cewa Zamfara ta samu ci gaba sosai ta fuskar tsaro.
“Gwamnatina ta ba da himma da kayan aiki masu yawa don ƙarfafa sojoji, tattara bayanan sirri, da haɗa kai don dawo da zaman lafiya a jihar.
“Mun sami gagarumar nasara a yaƙin da ake yi da ‘yan bindiga, yawancin wuraren da ake fama da rikici a baya, a halin yanzu sun kasance cikin kwanciyar hankali. Hanyoyin da a da ba a iya wucewa, a yanzu matafiya na wucewa lami lafiya cikin ‘yanci.
“Kuna iya ganin yadda mutane ke tafiya cikin walwala tare da gudanar da ayyukansu na yau da kullum da kuma yadda suke taruwa cikin farin ciki don yin tattakin samar da zaman lafiya. Wannan ya nuna a fili cewa mutanenmu sun samu zaman lafiya kuma suna son zaman lafiya. Hakan kuma ya nuna cewa jama’a sun fahimta kuma sun yaba da abin da gwamnatin jihar ke yi don inganta zaman lafiya.”
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: zaman lafiya
এছাড়াও পড়ুন:
Ranar Foliyo Ta Duniya: Muna Fatan Ganin Karshen Cutar Foliyo A Jihar Katsina -Zulaihat Dikko Radda
A cewar ta a cikin shekarar 2024 jihar Katsina kawai ta samu masu wannan cuta mutum 17 tare da guda biyu a karamar hukumar Danmusa a cikin wannan shekara
Haka kuma Hajiya Zulaihat Radda ya bada tabbacin cewa kowane yaro an tabbatar da ya amshi allurar Riga-kafin shan Inna
Ana jawabin wakilin asusun tallafawa yara na UNICEF na ofishin Kano, Rahama Mohammed Farah ta yabawa kokarin jihar Katsina na dawo da sabon yunkurin kawar cutar shan Inna a Nijeriya baki daya
Ya kuma bayyana cewa asusun kula da kananan yara na UNICEF Yana hadin gwiwa da gwamnatoci da hukumomi da masu ruwa da tsaki a kananan hukumomi domin ganin wajen fadakar da al’umma akan allurar Riga-kafin shan Inna a jihar Katsina.
Shima da yake jawabi shugaban hukumar lafiya a matakin farko ta Jihar Katsina Dakta Shansudeen Yahaya ya yi alkawarin cigaba da wayar da kan al’umma akan wannan cuta ta shan Inna da sauran cututtuka masu kashe yara a kananan hukumomi 34 na jihar Katsina
Wadanda suka shaida wannan bikin ranar ‘Polio’ ta duniya sun hada da hukumar lafiya ta WHO da kuma masu lalurar cutar shan Inna da wakilan asusun UNICEF da matan shugabannin kananan hukumomi 34 na jihar Katsina
ShareTweetSendShare MASU ALAKA