Falasdinwan Akalla 16 Sojojin HKI Suka Kashe A Gaza Ya Zuwa Yanzu A Yau Laraba
Published: 28th, May 2025 GMT
Majiyar kungiyoyin bada taimakon gaggawa a Gaza sun bayyana cewa ya zuwa lokacin bada wannan labarin a yau Laraba, sojojin yahudawan Sahyoniyya sun kashe akalla mutane 16.
Shafin labarai na Arab News ta kasar Saudia ya nakalto Mahmud Bassal kakakin wata kungiyar bada agaji na Gaza yana cewa da misalign karfe biyun dare jiragen yakin HKI sun kai hare-hare kan gidan Osama Al-arbeed dan jarida mai daukar hotuna a gidansa da ke arewacin Gaza, inda harin ya raunata Osman Arbeed sannan ya kashe wasu daga cikin yan gidansa.
Har’ila yau wasu mutane 6 sun kai ga shahada a yayinda wasu 15 suka ji rauni daga ciki har da yara kanana, a garin Khan Yunus a safiyar yau Laraba. A lokacin da kamfanin dillancin labaran AFP na kasar Faransa ya tuntubi sojojin HKI dangane da wadannan hare-haren basu bada amsa ba.
A cikin watan da ya gabata ne gwamnatin Natanyahu ta kara yawan hare-hare a gaza, na nufin samun abinda ya kira cikekken Nasara a kan Hamas a gaza. Don haka ne sojojin HJI suke kashe falasdinawa gwargwadon iyawarsu a Gaza a ko wace rana.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Sojojin Sudan Sun Fatattaki Dakarun Kai Daukin Gaggawa Daga Sansaninsu Da Ke Birnin Omdurman
Sojojin Sudan sun yi nasarar fatattakan ‘yan tawayen kasar na kungiyar Rapid Support Force daga sansanoninsu da ke kudancin Omdurman
Hukumomin sojin Sudan a birnin Omdurman na jihar Khartoum, sun sanar da cewa: Dakarun kai daukin gaggawa na Rapid Support Forces sun tsare sun bar makamai da alburusai da dama da suka hada da haramtattun makamai da aka hana amfani da su a dokokin kasa da kasa, bayan da suka sha kashi a yankin Al-Saliha da ke kudancin birnin. Majiyoyin sun kuma tabbatar da cewa: Dakarun kai daukin gaggawan suka kwace gidajen zaman jama’a da karfi da yaji domin amfani da su a matsayin ma’ajiyar makamai.
Yakin baya- bayan nan da sojojin Sudan suka yi da dakarun kai daukin gaggawa na Rapid Support Forces a yankin Al-Saliha da ke kudancin Omdurman ba abu ne mai sauki ba. An kwashe sama da wata guda ana gwabza fada. Babban dalilin shi ne mallakar manyan makamai da Dakarun kai daukin gaggawa suka yi, wanda ya janyo bullar tambayoyi da dama kan yadda dakarun da ba su da isasshen horo don amfani da irin wadannan makaman za su iya mallakar su, sai dai idan suna samu goyon baya daga waje.
Suleiman Abdo Ali, kwamandan rundunar soja ta Takht Omdurman, ya ce: “Alhamdu lillahi, an fatattaki makiya sun bar kayan aikin soja, da a ce sun kasance sojoji ne na yau da kullun ko kuma sojoji ne masu manufa ko wata akida da su tsaya a fafata da su.