Sheikh Na’im Kassim: Gwagwarmaya Tana Da Wata Hanyar Ta Korar ‘Yan Mamaya
Published: 26th, May 2025 GMT
Babban magatakardar kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon Sheikn Na’im Kassim ya bayyana cewa; Idan har gwamnatin kasar ta gajiya wajen yin abinda ya rataya a wuyanta na aiki da tsagaita wutar yaki, to gwgawarmaya tana da wata hanyar da za ta yi aiki da ita akan ‘yan mamaya.
Sheikh Na’im Kassim wanda ya gabatar da jawabi a jiya danage da zagayowar cikar shekaru 25 daga korar ‘yan sahayoniya daga kasar Lebanon da gwgawarmaya ta yi, ya jaddada cewa; “Gwagwarmaya ba za ta yi shiru ba, ba kuma za ta mika wuya ba, tana yin hakuri ne saboda ta bayar da Karin lokacin,don haka ya zama wajibi a yunkura.
Sheikh Na’im Kassim ya kuma ce; Gwamnati ce mai hakkin ganin an yi aiki da tsagaita wutar yaki a Lebanon, amma idan gwamnatin ta kasa, to da akwai mafita a hannun gwgawarmaya.”
Babban magatakardar kungiyar ta Hizbullah ya kuma ce; Aikin gwgawarmaya shi ne kare kai, da kuma kin mika kai ga ‘yan mamaya, wani lokaci tana yaki, wani lokacin kuma tana takawa ‘yan mamaya birki, ko ta yi hakuri tana jira amma tana cikin shiri.”
Sheikh Na’im Kassim ya kuma ce, makami ana yin amfani da shi ne bisa dacewar maslaha.”
Wani sashen na jawabin sheikh Na’im Kassim ya kunshi cewa; A wurin gwagwarmaya har yanzu yaki bai kare ba, kuma abinda Isra’ila take yi, yana karawa gwgawarmaya karfi ne da tsayin daka.”
Haka nan kuma ya ce; Kamar yadda babu wanda ya isa ya kawar da Lebanon, babu wanda kuma zai iya kawar da gwagwarmaya daga Lebanon.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: Na im Kassim ya
এছাড়াও পড়ুন:
UNICEF Ya Ba Da Tallafin Kayayyakin Aiki Ga Cibiyoyin Lafiya A Kirikasamma
A wani yunkuri na inganta kula da mata masu juna biyu da sauran ayyukan kiwon lafiya a jihar Jigawa, Asusun Kula da Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF tare da hadin gwiwar Karamar Hukumar Kirikasamma sun mika kayayyakin aiki da wasu muhimman kayayyaki ga cibiyar kiwon lafiya ta farko a Kirikasamma.
Mai kula da cibiyar kiwon lafiya ta farko, Kabiru Musa, ya bayyana cewa kayayyakin sun haɗa da gadajen haihuwa, zannuwan gado, kayan aikin jinya, matashin kai da sauransu, kuma za a rarraba su zuwa wuraren kiwon lafiya a fadin karamar hukumar.
A cewarsa, kayan da UNICEF da karamar hukumar suka samar za su inganta yadda ake gudanar da ayyukan kiwon lafiya a yankin.
Yayin mika kayayyakin ga mai kula da cibiyar kiwon lafiya, shugaban karamar hukumar Kirikasamma, Alhaji Muhammad Maji Wakili Marma, ya bukaci ma’aikatan lafiya da su tabbatar da gaskiya da adalci a lokacin rabon kayan.
Haka kuma, ya yaba da kokarin Gwamna Umar Namadi da sauran abokan hulda wajen gyara cibiyoyin kiwon lafiya da gina gidajen Ungozoma a Kirikasamma da kuma fadin jihar domin inganta ayyukan kiwon lafiya.
Usman Muhammad Zaria