An yanke wa wanda ya yi wa agolarsa fyaɗe ɗaurin rai-da-rai
Published: 27th, May 2025 GMT
Kotu ta yanke wa wani magidanci mai shekara 56 hukuncin ɗaurin rai-da-rai kan laifin yin fyaɗe ga agolarsa ’yar shekara 14.
Babbar Kotun Jihar Ekiti ta yanke wa mutumin hukuncin ne byan an gurfanar da shi kan zargin aikata laifin a watan Oktoban shekarar 2024, watanni bakwai da suka gabata.
A yayin zaman kotun da ke zamanta a garin Ado-Ekiti, mai gabatar da ƙara, Julius Ajibare ya gabatar da shaidu shida da ke tabbatar da laifin da ake tuhumar mijin mahaifiyar yarinyar da yi mata fyaɗe.
Kazalika ya gabatar da wasu hujjoji da kuma sakamakon gwajin asibiti da suka tabbatar da laifin da ake zargin magidancin da aikatawa.
Jama’ar gari sun kashe DPO, sun ƙona ofishin ’yan sanda a Kano NAJERIYA A YAU: Matsalolin Da Suke Tarnaki Ga Kananan Yara A Najeriya Da Hanyoyin Magance SuBisa haka ne kotun ta yanke wa mutumin hukuncin ɗaurin rai-da-rai, bayan ta saurari jawabansa ta bakin lauyansa, Olajide Adedeji, wanda ya gabatar da shaida guda ɗaya.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: agolarsa Ɗaurin rai da rai fyaɗe
এছাড়াও পড়ুন:
Kamfanonin Jiragen Ruwa Sun Yanke Hulda Da Isra’ila Saboda Matsalar Hare-Haren Kasar Yemen
Kamfanonin inshora za su kauracewa jiragen ruwa da ke da alaka da haramtacciyar kasar Isra’ila saboda tsoron fuskantar hare-haren Yemen
Jiragen ruwan da ke da alaka da haramtacciyar kasar Isra’ila za su fuskanci kaurace daga kamfanonin inshora, sakamakon munanan hare-haren baya-bayan nan da sojojin Yemen suka kai kan jiragen Magic Seas da Eternity Sea, wadanda suka kai ga nutsewa, a teku a ranar Alhamis.
A cewar wani rahoto da kamfanin dillancin labarai na Reuters ya wallafa ya bayyana cewa: Majiyoyin masana’antar inshora sun ce “kamfanonin inshora za su yi kokarin kauce wa rufe duk wani jirgin ruwa da ke da alaka da haramtacciyar kasar Isra’ila, ko da kuwa alakar a kaikaice ne.”
Kamfanin dillancin na Reuters ya nakalto daga Munro Anderson babban jami’in gudanarwa a Vessel Protect, wani kamfanin inshorar haɗarin ruwa na teku cewa: “Abin da suka gani a wannan makon yana kama da komawa ga ka’idojin kai hari a tsakiyar shekara ta 2024, wanda a zahiri ya haɗa da duk wani jirgin ruwa ko da kuwa yana da alaƙa mai nisa da haramtacciyar kasar Isra’ila.