Aminiya:
2025-07-12@01:04:34 GMT

An ga watan Babbar Sallah a Saudiyya

Published: 27th, May 2025 GMT

Hukumomin Kasar Saudiyya sun sanar da ganin jinjirin watan Zulhajji a ranar Talata, wanda ke nuna cewa ranar Laraba 28 ga Mayu, 2025, ita ce 1 ga watan Zulhajji, 1446 Bayan Hijira.

Hakan yana nufin Alhzai za su yi Tsayuwar Arfa ranar Alhamis, a yi Babbar Sallah ranar Juma’a na mako mai zuwaa yi

.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Babbar Sallah Layya Saudiyya

এছাড়াও পড়ুন:

Kwastam ta kama mazaƙutar jakai da aka yi yunƙurin safararsu

Hukumar hana fasa ƙwauri ta Najeriya (Kwastam), ta ce ta kama wata mota da ke ɗauke da wata kontena maƙare da mazaƙutar jakai a kan hanyar Kaduna zuwa Abuja.

Hukumar ta Kwastam ta sanar da kama motar ne a ranar Alhamis.

Sojoji sun tarwatsa matsugunin ’yan ta’adda da kashe wasu a Borno An gurfanar da wasu kan zargin kashe matafiya bikin aure a Jos

An gano waɗanda suka yi safarar ne da ake zargin suna shirin fitar da shi zuwa ƙasashen waje ba bisa ƙa’ida ba.

An samu nasarar ne a ranar Juma’a 5 ga watan Yuni, 2025, da misalin ƙarfe 9 na dare, bayan wani haɗin gwiwa da jami’an ofishin kula da namun daji na musamman da na hukumar Kwastam suka gudanar.

Kwaturola Janar na Hukumar kwastam, Mista Adewale Adeniyi ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai a Abuja ranar Alhamis.

Maimagana da yawun hukumar ta Kwastam, Abdullahi Aliyu Maiwada wanda ya wakilci Kwanturola Janar na Kwastam ya bayyana cewa, nasarar kama masu aikata hakan na cikin ƙoƙarin da ake yi na daƙile kasuwancin dabbobin dawa ta ɓarauniyar hanya.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • An tsare mutum 20 da ake zargi da kisan ’yan ɗaurin aure a Filato
  • Kotu ta aike mutum 20 da ake zargi da kisan ’yan ɗaurin aure a Filato
  • Kwastam ta kama mazaƙutar jakai da aka yi yunƙurin safararsu