OPEC+ Ta Fara Shirin Ayyana Yawan Man Fetur Da Zata Haka Zuwa Sekara Ta 2027
Published: 29th, May 2025 GMT
Kungiyar kasashe masu arzikin man fetur da kuma kawayenta a wajen kungiyar sun gudanar da taro a birnin Riyad na kasar Saudia inda suka tattauna kan yawan man fetur da zasu haka daga shekara da ta 2027.
Shafin yada labarai na tanar gizo na kasar Saudia Arab News ya bayyana cewa wannan yana daga cikin abinda kasashe suka amince a bayan kuma a halin yanzu kungiyar ta rika ta tsara yawan man da ko wace kasa zata haka daga shekara ta 2022 har zuwa shekara ta 2026.
Labarin ya kara da cewa kungiyar tana da tsare tsaren haka man fetur har guda uku biyu suna tafiya kamar yadda suka tsara a yayinda daya kuma sun warewa kasashe 8 daga cikinsu su aiwatar da shi. Wannan tsarin yana daga cikin tsare tsaren kungiyar na dogon zango.
A halin yanzu dai farshin man yana kan $60 a cikin watan Afrilun da ya gabata, Sannan shi ne farashi mafi karanci tun shekaru 4 da suka gabata, kuma sana diyyar kara kudaden fiton da Trump yayi farashin ya tashi zuwa $65 kan ko wace ganga.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Kwara ETF Ya Dauki Nauyin Karatun Fitattun Dalibai A Matakin Sakandare
Fitattun dalibai akalla 12 ne daga makarantun gwamnati suka samu guraben tallafin karatun sakandare a ƙarƙashin Asusun Tallafin Karatu na Jihar Kwara (Kwara-ETF).
A wajen taron gabatarwa ga waɗanda suka fara cin moriyar shirin, Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq ya bayyana cewa ci gaban harkar ilimi a Najeriya abu ne mai tsada kuma ya zama wajibi kowa ya bayar da gudummawarsa.
Ya roƙi masu masu hannu da shuni da kungiyoyi masu zaman kansu da su tallafa wajen gina makarantu ko kuma su ɗauki nauyin daliban da suka nuna bajinta da jajircewa a harkar karatu.
A cewarsa, an zabo daliban 12 ne sakamakon bajintar da suka nuna a matakai daban-daban na tantancewa da Kwara ETF ta gudanar.
Gwamnan ya bayyana cewa tallafin ya kunshi dukkan kuɗin da ake buƙata a karatun sakandaren daliban.
“Muna kira da jama’a su ba da gudummawa da kuma ɗaukar nauyin ɗalibai. Kada a bar wannan aiki ga gwamnati da iyaye kadai. Ilimantar da ‘ya’yanmu hakki ne da ya rataya a kanmu gaba ɗaya,” in ji Gwamna.
Ya yaba da tsarin zaɓen kuma ya taya waɗanda suka yi nasara murna.
A nata jawabin, Babbar Shugabar Kwara ETF, Oluwadamilola Amolegbe, ta ce daliban 12 sun fito ne daga cikin jerin ɗalibai 640 da aka fara tantancewa bisa cancanta.
Ta bayyana cewa tsarin zaɓen ya fara ne da rubuta jarabawa ga dukkan daliban firamare na aji shida da suka amfana da shirin KwaraLEARN na koyon fasahar zamani, har zuwa lokacin da aka kammala tantancewa.
Ali Muhammad Rabi’u