Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp.

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Wani abu ya fashe kusa da barikin soji a Abuja

Rundunar ‘yan sandan Birnin Tarayya ta buƙaci al’ummar da ke kewayen hanyar Mararaba zuwa Nyanya su kwantar da hankalinsu bayan jin ƙarar wani abu da ya fashe a yammacin ranar Litinin.

Lamarin ya faru ne a wata tashar bas da ke kusa da barikin sojoji na Mogadishu a kan hanyar Mararaba zuwa Nyanya.

A wata sanarwa da rundunar ta fitar mai ɗauke da sa hannun kakakinta, Josephine Adeh, ta ce tuni ta tura jami’anta wajen domin bincike da kuma tabbatar da zaman lafiya a yankin.

Kwastam ta kama Tiramol ta N150m, ta miƙa wa NAFDAC a Kano FCTA ta rufe hedikwatar PDP saboda rashin biyan haraji

“A ranar 26 ga watan Mayu da misalin ƙarfe 2:15 na rana aka yi mana kiran gaggawa kan wani abu ya fashe a shatale-shatalen hanyar Mararaba-Nyanya.

“Muna samun rahoton jami’anmu da ke sashen da abun ya shafa suka dira a wajen in da suka kange wurin.

“Mun samu nasarar ceto mutum guda da ya samu rauni, kuma yana asibiti yana karɓar magani.

“Muna nan muna bincike domin gano abin da ya fashe, da kuma musabbabin hakan.

Daga nan ne rundunar ta bukaci al’ummar yankin su ci gaba da harkokinsu ba tare da wata fargaba ba, su kuma miƙa wa rundunar duk wani motsi da ba su amince da shi ba.

Rahotanni sun bayyana cewa wanda ya tayar da bam ɗin ya mutu.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • ’Yar Najeriya ta tsinci miliyan 8.2 a Saudiyya ta mayar wa da mai su
  • Yadda Rashin Ɗaukar Wani Maniyyaci Ya Hana Jirgi Tafiya Har Sai Da Ya Dawo Ya Ɗauke Shi
  • Mutum 1 Ya Rasu, 2 Sun Jikkata A Wani Mummunan Hatsarin Mota A Abuja
  • Gwamna Uba Sani Ya Kammala Titin Unguwar Su El-Rufai
  • Kotu ta ci su El-Rufa’i tarar miliyan 900
  • Sojoji Sun Kashe ‘Yan Ta’adda Da Dama A Wani Sabon Hari Da Suka Kai Sansanin Sojoji A Borno
  • Raya Al’adu Wani Sirri Ne Na Ci Gaban Kasar Sin
  • Wani abu ya fashe kusa da barikin soji a Abuja
  • FCTA Ta Rufe Hedikwatar PDP Ta Ƙasa Saboda Ƙin Biyan Harajin Ƙasa