‘Yansanda Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Kisan Wata Matar Aure, ‘Yar shekara 22 A Kano
Published: 27th, May 2025 GMT
Mijinta mai suna Ibrahim Mohammed ne ya gano ta, inda aka garzaya da ita asibiti, daga bisani aka tabbatar da mutuwarta.
“Wanda ake zargin ya amsa laifin da ake zarginsa da aikatawa, inda ya amince da haurawa cikin gidan matar, inda ya shake ta, sannan ya daba mata wuka a wuya, wanda ya yi sanadiyar mutuwarta.
Sanarwar ta kara da cewa “Za a gurfanar da wanda ake zargin a gaban kotu bayan kammala bincike.”
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
’Yan sanda sun ƙaddamar da samamen “Operation Kukan Kura”, sun kama mutum 98 a Kano
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano, ta kama mutum 98 da ake zargi da aikata laifuka daban-daban, ciki har da fashi da makami, safarar miyagun ƙwayoyi, sata, zamba da kuma tayar da hankalin jama’a.
An kama waɗannan mutane ne ƙarƙashin sabon samamen da rundunar ta ƙaddamar mai suna “Operation Kukan Kura” wanda ya fara aiki a ranar 1 ga watan Yuli, 2025.
Kotun ƙoli ta tabbatar da Okpebholo a matsayin gwamnan Edo Jami’ar Tarayya ta Gashuwa za ta ba matar Tinubu digirin girmamawaKwamishinan ’Yan Sandan Kano, Ibrahim Adamu Bakori, ne ya bayyana hakan yayin taron manema labarai da aka gudanar a hedikwatar rundunar da ke Bompai a ranar Alhamis.
Ya ce wannan aiki wani ɓangare ne na ƙoƙarin daƙile aikata laifuka da tabbatar da zaman lafiya a faɗin Jihar Kano.
Ya ce samamen ya samu goyon bayan Sufetan Janar na ’Yan Sanda, Kayode Adeolu Egbetokun, domin ƙarfafa haɗin kai da al’umma wajen yaƙi da laifuka.
Kwamishinan, ya bayyana cewa wannan aiki yana bin tsarin aikin rundunar, wanda ke nufin haɗa kai da al’umma wajen hana aikata laifuka.
Rundunar ta nazarci halin tsaro a jihar tare da duba yankunan da laifuka suka fi yawa kafin ta ƙaddamar da samamen.
Ya ce babban burin wannan aiki shi ne zama tamkar wata hanyar gargaɗi domin gano da kuma daƙile barazanar laifuka tun kafin su faru.
Daga cikin waɗanda aka kama akwai mutum 21 da ake zargi da fashi da makami, huɗu ana zargin su da garkuwa da mutane, biyar kan safarar miyagun ƙwayoyi.
Sauran sun haɗa da mutum 12 da ake zargi da satar motoci, huɗu ana zargin su da zamba, sai wasu biyar da ake zargi da sata, da kuma mutum 47 da ake zargi da tayar da hankalin jama’a.
Kayayyakin da aka ƙwato sun haɗa da motoci guda shida, adaidaita sahu guda takwas, babura guda tara, tabar wiwi, kwalabe 86 na kayan maye, takubba 16 da wuƙaƙe.
Kwamishinan, ya ce waɗannan nasarori za a ci gaba da amfani da su wajen inganta dabarun aiki da rundunar ke aiwatarwa.
Ya ƙara da cewa rundunar za ta ci gaba da ɗaukar matakan kare rayuka da dukiyoyin al’ummar Jihar Kano.